Basdiq Crypto

Basdiq Crypto

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Basdiq Crypto, NAVY Estate, Abuja.

📊 Crypto Educator & Analyst
🎥 Digital Content Creator
📉 Smart Money | Market Structure
🌱 Agriculturist
📖 Quran Reciter
✨ Ads & Promotions

📩 DM for Collaboration

Photos from Basdiq Crypto's post 07/06/2026

*🐝 KIMIYYAR ƘUDAN ZUMA A CIKIN ALƘUR'ANI 📖*

Wata Baturiya mai suna *Mac Kay Orton,* wacce ta shafe shekaru masu yawa a sana'ar kiwon zuma, ta yi matuƙar mamaki da ganin yadda Alƙur'ani ya yi fayyataccen bayani game da ƙudan zuma.

Alƙur'ani littafi ne da aka saukar fiye da shekaru 1445 da s**a gabata, amma ya ƙunshi bayanai game da ƙudan zuma waɗanda ilimin kimiyya ya fara gano su ne a zamaninmu.

Ta yaya *Annabi Muhammad (ﷺ)* ya san wannan ilimi alhali bai yi karatun boko ba?

Mac Kay tana da masaniya a fannin *Entomology* (reshen ilimin halittu da ya shafi ƙwari). Ta yi shekaru tana kiwon zuma, sannan ta ci gaba da karatun digiri na biyu (Master's Degree) a fannin kiwon ƙudan zuma a Jami'ar Cornell.

An ga wani bidiyo nata a shafinta na Instagram inda take riƙe da Alƙur'ani mai fassarar Turanci. Ta fara karanta Suratul Nahl, surar da ta yi magana kan ƙudan zuma 🐝

Babban abin da ya ja hankalinta shi ne yadda Suratul Nahl ta zo a lamba ta goma sha shida (16) cikin jerin surorin Alƙur'ani.

Sannan ayar da ta yi magana kai tsaye a kan ƙudan zuma ita ce aya ta 68, wacce ta ƙunshi bayanai masu zurfi game da rayuwar ƙudan zuma.

*"وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحْلِ أَنِ ٱتَّخِذِي مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ"*

Abin mamaki kuwa shi ne, macen ƙudan zuma (worker bees da queen bee) suna da chromosomes guda 32 (pairs 16), yayin da mazan ƙudan zuma (drones) suke da chromosomes guda 16 kacal.

Ta yi matuƙar farin ciki da yadda Musulunci ya ba ƙudan zuma muhimmanci, har ma ya hana kashe su ba tare da dalili ba.

Mac Kay ta fitar da muhimman abubuwa guda uku:

Na farko: Yadda Alƙur'ani ya bayyana cewa zuma tana ɗauke da waraka ga mutane.

Na biyu: Yadda ƙudan zuma suke gudanar da rayuwarsu cikin tsari da haɗin kai, kowacce tana da aikin da take yi a cikin gidan zuma.

Na uku: Yadda Alƙur'ani ya yi amfani da sigar mace yayin magana da ƙudan zuma.

Tun tsawon tarihi, mutane sun san cewa ƙudan zuma suna tattara ruwan furanni, suna samar da zuma kuma suna gina gidajensu. Amma sai a ƙarni na sha tara ne masana kimiyya s**a fara fahimtar cewa ƙudan zuma mata ne suke tattarawa da sarrafa ruwan furanni zuwa zuma. Mazan ƙudan zuma ba sa shiga wannan aiki.

Abin mamaki shi ne Alƙur'ani tun farko ya yi amfani da kalmomin da suke nuni da jinsin mace wajen umartar ƙudan zuma:

_"Ki riƙi gidãje..."_

_"Sa'an nan ki ci..."_

_"Kuma ki bi hanyoyin Ubangijinki..."_

Allah (ﷻ) Ya ce:

*"Kuma Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cewa: 'Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa. Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itatuwa, kuma ki bi hanyoyin Ubangijinki waɗanda aka sauƙaƙa. Ana fitowa daga cikin cikkunansu wani abin sha mai launuka dabam-dabam; a cikinsa akwai waraka ga mutane. Lalle a cikin wannan akwai alama ga mutanen da suke tunani.'"*
(Suratun Nahl: 68-69)

Waɗannan ayoyi suna nuna mana cewa ƙudan zuma mata ne suke gudanar da ayyukan tattarawa da samar da zuma.

Haka kuma, wajen bayanin cikin ƙudan zuma, Alƙur'ani ya yi amfani da kalmar "بُطُونِهَا" wacce ke nufin "cikkunansu". Masana kimiyya sun gano cewa ƙudan zuma suna da sassa daban-daban a tsarin narkar da abinci. Akwai honey stomach (cikin adana nectar) da kuma ainihin cikin narkar da abinci. Wannan ne ya sa nectar ɗin da suke tattarawa ke canzawa zuwa zuma kafin a ajiye ta a cikin gidan zuma.

Wannan ilimi da ake koyarwa a yau a fannin kimiyya, Alƙur'ani ya yi ishara da shi tun fiye da shekaru 1445 da s**a gabata.

Abu na ƙarshe kuma shi ne, mutane da yawa sun fi sanin ƙudan zuma da yin gida a kan bishiyoyi. Amma daga baya masana s**a gano cewa akwai nau'o'in ƙudan zuma da suke yin gidajensu a cikin kogunan duwatsu, ramukan ƙasa da sauran wurare daban-daban.

Alƙur'ani kuwa tun farko ya ambaci waɗannan wurare uku:

*"Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."*

Allah (ﷻ) Ya ce:

*"Za Mu nuna musu ayoyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cewa lalle shi (Alƙur'ani) ne gaskiya."*
(Suratu Fussilat: 53)

Allah Ya ƙara mana shiriya da fahimta.

*✍🏾 ABUBAKAR SADIQ ADAM

06/06/2026
06/06/2026

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.

With profound sadness, I received the news of the passing of Malam Sadiq Pharmacy, a respected Islamic scholar, Qur’anic teacher, and practitioner of Islamic medicine whose knowledge and service touched countless lives beyond Gombe State.

His dedication to the propagation of Islamic teachings, Qur’anic exegesis, and the welfare of the Ummah earned him the admiration and respect of many. His demise is not only a loss to his family and community but to the broader Muslim Ummah.

I extend my heartfelt condolences to his family, students, associates, and the people of Gombe State. May Almighty Allah forgive his shortcomings, expand his grave, and grant him Aljannatul Firdaus. Amin. -AA

02/06/2026

ALHAMDULILLAH

23/05/2026

Idan Peter Obi ya biyawa musulmi 44 kujerar aikin hajji, wannan baya zama dalilin cewa shi shugaba ne adali mai kishin muslunci

Kamar yadda Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce: Bola Ahmad Tinubu ya gina masallatan jumu'a sama da 400 a arewacin Nigeria duk da haka bai kasance adali ga addinin muslunci ba

Saboda haka yiwa addinin muslunci hidima a gabanin zaɓe zai iya kasancewa campaign domin neman ƙuri'un musulmi

Asalin kishin muslunci a zuciya yake, har abada waɗannan mutanen ba zasu so addinin muslunci da musulmi ba

Allah ya riga ya gayamana acikin littafi mai tsarki.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


NAVY Estate
Abuja
900101