Haruna Aliyu Maifata

Haruna Aliyu Maifata

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Haruna Aliyu Maifata, Health/Beauty, House of assembly estate abuja, Abuja.

Photos from Wasiyya Page Nigeria's post 31/10/2024

SAKON WATA BAIWAR ALLAH MARAS LAFIYA DA TABAYAR A ISARMATA GA MAITAIMAKON AL UNMA KAMAR YANDA TA AMBATA ALHAJI MURTALA ABDULKADIR DAN IYAN JARMAN SOKOTO

Don Allah yan uwa ku idarmin sakonga nau zuwaga wanga bawan Allah ko na kusa gareshi

Yanzu haka Ina kwance asibiti banida lafiya sosai na kwan biyu can akwai allurar da ake yimin Kullum 3,500 kuma wlh yanzu ko kuddin magani bamuda bare na allurar

Shine nikeson Don girman Allah ku idarmin Sakonga nau zuwa gareshi Ina ganin yadda yake taimakawa al'umma musamman idan irin haka ta faru Don Allah ya taimaka mini

Allah yasa Sakona yakai ga Murtala Abdulkadir Dan Iya wlh na yarda dashi kuma inada tabbacin indai kun isarda sakona Garai in Allah yaso zai taimaka mini ngd

01/08/2024

Zamu kawomaku yanda zanga zanga kecigaba da faruwa a Babban birnin Sokoto

19/08/2023

Tunda aka tsareni lalataccen abinci ake bani, yanzu haka busasshen taliya da shinkafa nike ci, inji Bazoum.

A wasu makonnin da s**a gabata, CNN ta nakalto Bazoum a cikin jerin sakonnin Message ga wani abokinsa yana cewa "an hana shi duk wani hulda da mutane", ba tare da bashi abinci mai kyau ko magunguna ba.

A cewar hambararren shugaban, ya jima yana rayuwa ba tare da wutar lantarki ba. Bazoum ya ce duk abincin da aka kawo masa ya lalace, kuma yanzu haka yana cin busasshen taliya da shinkafa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin mulkin sojan ta baiwa Bazoum damar ganin likitansa. Allah ya kyauta.
Wasiyya Company

Photos from Wasiyya Page Nigeria's post 18/08/2023

Wannan shine hoton Adamu wanda ya tashi daga Bauchi ya tafi Kano domin ganin jarumar KannyWood Aisha Humaira, daga karshe an sace mishi komai nashi a jihar Kano.

A jiya da dare jaridar Dokin Karfe TV tayi hira dashi yace sunanshi Adamu yazo daga jihar Bauchi yanzu haka yakai tsawon kwanaki 15 a garin Kano domin ya samu yayi ido hudu da jarumar KannyWood Aisha Humaira, saboda wakokinta suna burgeshi.

Ance lokacin da yazo Kano da jakarshi da kayanshi masu kyau yazo, daga karshe aka sace mishi komai nashi harda kudin shi ya dawo kwana duk inda ya samu.

A hirar da aka yi dashi, ya yiwa iyayenshi karyar sunsan da zuwan nashi kuma sun mishi Addu'ar Allah yasa yaga jaruma Aisha Humaira, yace suna zaune da iyayenshi a Bauchi dai-dai layin gidan kaura da ke GRA, kusa da gidan baban Anas.

Dazun nan yaron ya fadi kasa yana fitar da farin ruwa, yanzu haka an dauki yaron an tafi dashi Asibitin Murtala da ke Kano. Mutanan jihar Bauchi ya kamata ku taimaka ku binciko inda yaron nan yake domin iyayenshi susan halin da yake ciki.

✍️Wasiyya Company

15/06/2023

Gini ya danne masu ɗibar 'ganima' a wurin rusau a Kano

Ƙarin bayani - https://bbc.in/3PdV8Ye

05/06/2023

Shin dai-dai ne Abba Gida Gida ya cigaba da ɗaukar shawara irin ta El-rufai ?

Bayyana mana ra'ayin ku.

Photos from Wasiyya Page Nigeria's post 05/06/2023

Kwamitin Kar-ta-kwana Mai Alhakin Rushe Gine-ginen Da Akayi Ba Bisa Ƙa'ida Ba Na Gwamnatin Jihar Kano Ya Ziyarci Filin Masallacin Idi Inda Ya Rushe Wasu Gine-gine

Sai dai a yau akwai wasu gine-gine da ba'a rushe ba, sakamakon ana tunanin akwai kaya a ciki, domin bawa masu kayan damar kwashe kayan su.

05/06/2023

QALUBALEN GA SABON GWAMNA AHMAD ALIYU SOKOTO!!
Daga Jaridar Nasara
Hari Mafi Muni Da Aka Kai A Hawan Ahmad Aliyu!!

Hakika ina so nayi amfani da wannan dama domin tunatarda sabon Gwamna Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto cewa, ya kamata ya tashi tsaye tsayin daka wajen ganin ya kakkabe matsalar tsaro a jihar Sokoto tun da wuri, domin wannan matsala tana daga cikin matsalolin da s**a janyowa tsohon Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal s**a da bakin jini.

Wannan hari da 'yan bindiga su ka kai a garin Raka da ke cikin karamar hukumar Tangaza shine hari mafi muni da aka kai a hawan ka Gwamna, don haka idan har ka yi sakaci wannan matsala ta cigaba da faruwa ga al'ummar jihar Sokoto to ko shakka babu s**a da bakin jinin da Gwamna Tambuwal ya yi zasu dawo ta kanka.

Wannan wane irin rashin imani ne 'yan bindiga su shiga gari su halaka mutun sama da 35 tare da kone dukiya da gidaje?

Tabbas akwai matsala!

Ubangiji Allah ya jikan su da rahama.

5/6/2023

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

House Of Assembly Estate Abuja
Abuja