Daga Zuciyar Bintu
Ina kawo muku labaran rayuwa kamar yadda suke. Ba Kari, ba ragi. Na ji na gani…Zan fada!
06/09/2025
Abinda ya faru yanzu haka ya karya min zuciya 🥲.
Na fita yin waybill na kayan da abokan cinikina s**a siya, sai na dawo na tarar da fuskar ɗana a haka.
Na bar shi tare da mahaifinsa. Na tambaye shi, “wanene ya yi maka haka?” sai ya ce mini, “daddy ne ya yi.” Na ƙara tambayar ’yata yar shekara huɗu, ta kuma bayyana cewa yana kuka lokacin da na fita, sai daddy ya ɗauki hangar na kaya ya buge shi a fuska 😭😭. Ta bayyana haka a gaban mahaifinsa, kuma bai ƙaryata ba.
Na yi matuƙar fushi yanzu, ban san abin yi ba saboda zuciyata ta cika da kuka, kuma hannuwana sun ɗaure.
Don Allah ku bani shawara saboda zuciyata ta karye 🥲.
Daga NaijaVlog
20/08/2025
With Chefbie – I just got recognised as one of their top fans! 🎉
03/08/2025
A duk ranar da Nayi wannan abincin, Toh fa bama na iya ci don tunani da Kewar mahaifiya ta… MASA ita ce abincin da mamata tafi kwauna. Allah ya jiqan ki mama! Wani abincin mahaifiyar ku ta fi so.
30/07/2025
28/07/2025
With Murjanatu Ringim – I just got recognised as one of their top fans! 🎉
28/07/2025
With Asher Kine – I just got recognised as one of their top fans! 🎉
“Idan za ki/ka iya komawa lokacin da kake/kike shekara 20, wane shawara za ki/ka ba kanki ko wani?”
Ni zan fara a cikin comment ⬇️
Mu tattauna. Watakila akwai wanda zai amfana da shawarar ka/ki a yau.
’ana
08/06/2025
Sallar Layya ta farko ba tare da Mama
ba.
Tunda na yi aure shekaru da dama da s**a wuce, tun wannan lokacin nake aikin naman Sallah tare da mahaifiyata. Ba ni kadai ba dukkan mu. yaran ta mata. Muna haduwa a gida domin gudanar da aikin naman Sallar mu. Ko da kuwa akwai daga cikinmu da ba su yi layya ba a shekarar, mahaifiyarmu kan zo da fara’a ta cire musu cinya daga layyarta, ko wannen mu ma haka, kowa na murna da jin daɗin hadin kai.
Ban taɓa yin Sallar layya ba batare da mahaifiyata ba. Tana sa mu dariya, tana bada umarni, tana sanya komai cikin tsari da annashuwa.
Amma wannan Sallar… ta zo da ƙalubale daban. Domin wannan ce Sallar farko da nayi ba tare da mahaifiyata ba. Ta rasu kafin Sallah bana. Yanzu haka zuciyata cike take da kewarta, da soyayyarta, da dukan abubuwan da take yi da muke ɗauka kamar al’ada kawai.
Yanzu na fahimta- ba wai nama kawai muke yankawa ba, amma muna gina ƙauna, zumunci da tunani mai zurfi. Aikin naman Sallah ya canza ma’ana a gare ni. Yanzu, kowanne yanka, kowacce tafasa, tana tuna min da ita.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya jikanki, Mama. Zaki ci gaba da rayuwa a zuciyata har abada.
Allah dai ya sa mu dace… Amin
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Opening Hours
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |

14/05/2025