Imam Junaidu Abubakar Fan's

Imam Junaidu Abubakar Fan's

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Imam Junaidu Abubakar Fan's, Health/Beauty, Bauchi.

27/11/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN:

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa. Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin sanannun malamai masu zurfin ilimi, hikima da tasiri a fadin Najeriya da ma wasu ƙasashen waje.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi fice wajen yaɗa ilimin addini, gyaran tarbiyya, da jawo hankalin al’umma zuwa zaman lafiya, adalci da tsoron Allah. Kalamansa sun kasance cike da nasihohi masu taushi da faɗakarwa, tare da bin sahihin tafarkin Annabi (SAW) wajen isar da sakon addini.

Marigayin ya rayu da sadaukarwa wajen gina al’umma, ya ilmantar da dubban dalibai waɗanda s**a yada iliminsa a sassa daban-daban na duniya.

Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya sanya kabarinsa cikin fadawar Aljanna.
Allah Ya ba iyalansa, almajiransa, mabiyansa da dukkan al’ummar Musulmi hakurin jure wannan babban rashi. Amin.

22/11/2025

DA DUMI-DUMI:

Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Yi Kira Ga Yin Addu’o’i Kan Barazanar da Amurka Ta Yi wa Najeriya

An samu rahoton cewa Maulana Sheikh Usman Dahiru Bauchi (RTA), ta bakin wani daga cikin wakilansa, ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su tsunduma cikin addu’o’i, bayan jita-jitar barazanar da ake dangantawa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, kan Najeriya.

A cikin sakon, an bukaci Musulmi su yi dogon istighfari da addu’o’i domin neman kariya da sauƙi ga kasa. Daga cikin abin da aka sanar akwai:

Karatun Suratul Fātiha sau ɗaya

Istighfari 1000

Salatul Fātihi 1000

“Ya Latīfu” 1000

Haka kuma, an bukaci manyan Zawiyoyi da Tsangayu a fadin ƙasar su gudanar da addu’o’i masu yawa, ciki har da:

Istighfari 1,000,000

Salatul Fātihi 1,000,000

“Ya Latīfu” 1,000,000

An ce manufar wannan kira ita ce neman tsare kasa, da rokon Allah ya kawar da duk wata fitina ko barazana, tare da sauƙaƙa al’amuran Najeriya da al’ummar ta.

Sakon ya fito ne a matsayin gargadi da jan hankali kan halin da ake ciki, tare da kira ga musulmi su kara dagewa a ibada da yin addu’a domin zaman lafiya.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Bauchi