Dplus perfumes and cosmetics

Dplus perfumes and cosmetics

Share

1

31/03/2026

Amina ta kasance mace mai nutsuwa, amma rayuwarta cike take da damuwa da tunani. Tana zaune a ƙaramin gida tare da ’ya’yanta biyu, bayan mijinta ya rasu shekaru biyu da s**a gabata. Rayuwa ta sauya mata gaba ɗaya, daga matar gida mai dogaro da mijinta, zuwa uwa da ke fuskantar duniya ita kaɗai.
Kullum tana zaune tana tunani:
“Yaya zan yi na riƙe kaina da ’ya’yana cikin mutunci?”
Wata rana, tana dube-dube a Facebook, ta ga wata mace tana tallar kayan mata, kayan shafawa da atamfofi. Amma abin da ya ja hankalinta ba kayan ba ne… labarin da matar take ba da shi ne.
Matar ta fara da cewa:
"Na taɓa zama kamar ke… babu wanda ya san wahalata. Amma yau, wannan ƙaramin kasuwancin ya bani murya, ya bani daraja."

Amina ta tsaya cak.
Ba tallar kaya kawai ba ce… zuciyarta aka taɓa.
A ranar ne Amina ta yanke shawara. Ta ce:
"Ni ma zan iya."
Ta fara da ƙaramin jari, ta sayo ƙananan kayayyakin mata: turare, gyale, da man shafawa. Amma matsala guda ɗaya ta taso… babu wanda yake siya.
Ta ɗora hoto kawai, ta rubuta:
"Turare mai kyau, ₦5,000."
Kwana uku… babu mai tambaya.
Sai ta tuna da waccan matar. Ta tuna yadda labari ya sa ta tsaya.
A nan ne komai ya canza.

Rana ta gaba, Amina ta ɗauki waya, ta rubuta:
"Shekaru biyu da s**a gabata, na rasa mijina… na ji kamar rayuwa ta tsaya. Amma yau, ina tsaye da ƙafafuna saboda wannan ƙaramar sana’a. Wannan turaren ba kawai ƙamshi ba ne… alamar sabon farawa ne gare ni."
Ta ɗora.
Mintuna kaɗan… wani ya yi comment:
"Yaya zan samu?"
Sai wani:
"Ina son guda biyu."
Amina ta kalli wayarta, hawaye s**a cika mata ido.
Ba wai saboda kuɗin ba… amma saboda ta ji an gan ta. An ji labarinta.
Daga wannan rana, Amina ta fahimci wani sirri mai girma:
Mutane ba kaya suke saya ba… labari suke saya.

Ta ci gaba da amfani da Storytelling.
Idan za ta sayar da gyale, ba za ta ce kawai “gyale mai kyau” ba. Sai ta ce:
"Wannan gyalen na tuna min ranar da na fara fita kasuwa bayan dogon lokaci… ranar da na dawo na ji cewa zan iya sake gina rayuwata."

Idan turare ne, sai ta ce:
"Wata kwastoma ta ce min, bayan ta saka wannan turaren, mijinta ya tambaye ta ko ta sauya wani abu… sai ta yi murmushi kawai."

A hankali… kasuwancinta ya fara girma.
Ba tare da fita kasuwa ba.
Ba tare da hayaniya ba.
Ba tare da wahalar fita rana ba.
Amina ta zauna a gida, amma kuɗi na shigowa.
Wannan ne rufin asirin da Online Business ya bata.
Ba wanda ya san halin da take ciki. A Facebook, ana ganinta a matsayin mace mai ƙarfi, mai kasuwanci, mai daraja.
’Ya’yanta sun fara zuwa makaranta cikin nutsuwa.
Abinci bai ƙara zama matsala ba.
Kuma mafi muhimmanci… Amina ta fara murmushi da gaske.
Wata rana, wata mace ta turo mata saƙo:
"Yar’uwa, ina son yadda k**e rubutu. Kina sa ni jin kamar kina magana da ni kai tsaye. Ta yaya k**e yi?"
Amina ta ɗan yi murmushi, ta amsa:
"Ina faɗin gaskiyata ne kawai."
Domin storytelling ba ƙarya ba ne… gaskiya ce da aka zuba a cikin zuciya.
Yana haɗa kai tsakaninka da kwastomarka.
Kwastoma ba ta jin kamar tana siya ne… tana jin kamar tana cikin labarinka.
Amina ta gane cewa:
Idan mutum ya yarda da kai, zai siya daga gare ka.
Amma idan ya ji ka… zai dawo gare ka.

Shekarar farko ta cika.
Amina ta duba inda ta fito, daga mace mai kuka a cikin ɗaki, zuwa mace mai sayar da kaya ga mutane daban-daban a ƙasar.
Ta ce a ranta:
"Da ban fara ba, da har yanzu ina jiran taimako daga mutane."
Yanzu kuwa… ita ce take taimakon wasu.
Ta fara koyawa wasu mata yadda ake amfani da storytelling a kasuwanci. Ta ce musu:
"Kada ku sayar da kaya kawai… ku sayar da labarinku. Domin a cikin labarinku akwai zuciyar da zata ji ku."
A yau, Amina ba kawai ’yar kasuwa ba ce.
Alama ce ta cewa mace na iya tsayawa da kanta.
Alama ce ta cewa Online Business ba kawai sana’a ba ce… hanya ce ta mutunci, rufin asiri, da ’yanci.
Kuma duk wannan ya fara ne da abu guda ɗaya wato Labari.

Wannan labarin Sadaukarwa ne ga duk Wata Mace da take Online Business, ki sani cewa koda ba a faɗa ba, koda ba a ce Maki komai ba kina ƙoƙari matuƙa.🙏💔🥰

© Zaidu Barmo
-Storytelling Coach.

25/03/2026

Kasuwa akwai dadi

14/03/2026
08/03/2026

Mentorship

As part of our community engagements at , we've hit the ground running with our first phase of Mentorship Program.

To start with we paid JAMB registration of some few selected students.

The next line of action is to put them through a rigorous training on how to go about the exams.

YD CHARITY FOUNDATION is beyond helping the helpless, we go further to mentor the young generation.

08/03/2026

Ciyarwar azumin Ramadan 2026

08/03/2026

A turo Opay jama’a zamuyi alkhairi

16/02/2025

30k bakaraj rouge

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kasuwar Sabon Gari Kano
Kano