Muhammad Basiru Lautaye Bunkure
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muhammad Basiru Lautaye Bunkure, Health/Beauty, BUNKURE LAUTAYE, Kano.
Assalam alaikum warahmatullah
Assalam alaikum warahmatullah yan uwa barka da jumaa
02/11/2021
Amincin Allah yatabbata agareku Yan uwa musulmi da fatan kowa yana cikin koshin lafiya
19/10/2021
Ruwa a Abuja kamar da bakin kwarya
Assalam alaikum warahmatullah yan uwa barka da wannan lokaci
*FITILA. 381:*
*LADUBBAN CIN ABINCI.*
_Ku A Matsayin Ku na *Iyaye* Ya kamata ace Kuna kula Sosai Da yadda *'ya'yanku* Suke Gudanar Da duk Al'amuran Su, Domin *Dora* Su akan *Tarbiyyar Musulunci* , Musamman Wajen *Cin Abinci* ._
_Fadin *"bismillah"* A lokacin fara *cin abinci:* Wannan kuma saboda hadisin *Umar Dan* *Abi-salamah (RA)* yace: Na kasance *yaro* karkashin kulawar manzon Allah " *(S.A.W)* kuma hannuna ya kasance yana yawo a cikin Akushin abinci, sai yace:_
*" ﻳَﺎ ﻏُﻼَﻡُ ! ﺳَﻢِّ ﺍﻟﻠَّﻪَ، ﻭَﻛُﻞْ ﺑِﻴَﻤِﻴﻨِﻚَ، ﻭَﻛُﻞْ ﻣِﻤَّﺎ ﻳَﻠِﻴﻚ . ﻓَﻤَﺎ ﺯَﺍﻟَﺖْ ﺗِﻠْﻚَ ﻃِﻌْﻤَﺘِﻲ ﺑَﻌْﺪ "* .
```(Ya kai yaro!``` _Ka Ambaci sunan Allah, ka *ci* da hannun dama, kuma ka *Ci* Abinda ke gabanka. – *Jabir yace* :- Daga wannan lokacin ban gushe ba; wannan ne irin *cin abincina)*_ .
_*Cin abinci* da hannun *dama* Sannan Mutum ya ci gabansa Shima wannan sunna ne saboda hadisin da ya gabata._
*Yaa Allah ka Bamu Ikon kiyaye wa*
إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْـمُؤْمِنِينَ وَالْـمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَـمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ
إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ
Innnalillahi wa innnalaihirraji'unn Allah yayiwa matar AUWALU MASHAURA BUNKURE Rasuwa a jiya jumaa.
Allah yajikanta yayi Mata Rahma.......
Amincin Allah yatabbata agareku Yan uwa musulmi da fatan kowa yawuni cikin koshin lafiya
Assalam alaikum warahmatullah yan uwa barka da dare
NASIHOHI GUDA HAMSIN (50)
1 ka kula da kanka
2 yazamana kana jin tsoron Allah
3 ka san cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne
4 ka zamu mai cika alkawari
5 ka zauna da kowa lafiya
6 ka dinga tunawa da mutuwa
7 ka rage buri
8 ka cire kwadayi
9 banda yin hassada don kaga Allah ya daukaka wani
10 kasan cewa ita fa duniya ba matabbaciya bace
11 ka yawaita istigifari
12 ka yawaita salati ga manzon Rahama
13 banda yin gulma ko munafurci
14 banda cin amana
15 ka zauna da kowa lafiya
16 ka tsarkaka zuciyarka
17 banda nufar mutum da sharri
18 karkayi zalunci
19 karkayi girman kai
20 karkayi wulakanci
21 ka zama mai taimako
22 ka kula da addininka
23 ka zamu mutum mai Alkunya
24 ka zama mutum nagari mai kirki
25 kasan cewa komai mai wucewa ne
26 ka dinga hakuri kar ama shaidar cewa baka da hakuri
27 ka kuma yawaita addu'a
28 kayi biyyah ga iyayenka
29 ka zama mai tausayi
30 ka zama mai imani
31 kana aiki da hankalinka
32 ka guje wa sabon Allah
33 karka ci haram
34 karkayi shaye-shaye
35 ka nisanci zina
36 ka mai da hankalinka guri daya
37 ka ciyar da kanka halal
38 karka zama mutum mai yaudara
39 duk abinda zakayi kayi saboda Allah
40 banda aibatan mutum don kaga yana wani yanayi,yi mishi addu'a
41 ka zama mai taimako da tausayin iyayenka
42 ka yawaita yiwa wadanda s**a rasu addu'a
43 kazama mutumin da kowa zai dinga maka kyakkyawar shaida
44 kabi duniya a hankali
45 karka dinga yin gaggawa
46 sannan ka rike gaskiya duk maganar dazaka fada kake yin gaskiya.
47 ka zamu mai adalci a duk inda kake
48 kar abin duniya ya rudeka har kaje kana aikata sabo
49 ka kula da hakkin makwaftanka
50 kayi fatan gamawa da duniya lafiya...
Allaah Yasa mudace...
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Kano
