Hon,Sha'arani Lawan Rogo
Rogo local government bakin kofar gari political
16/06/2023
SIYASAR MU A YAU.!!!
-----------------------------------
Zanyi Anfani Da Wannan Lokacin Domin Yin Kira Gami Da Bada Shawara Ga Shuwagaban Nin Jam'iyyar Mu.,Ta N.N.P.P.
Tun Daga Matakin Local Government, Har Zuwa Ga Matakin Mazaba, Wato Ward level.
Ku Sani Adalci Shine Ginshikin kawacce Irin Nasara, kuma Bayyanawa Wadanda ake wakilta Komai Shine Zai Samarda Natsuwa Da Kuma Gamsuwa gameda Yadda kuke Jagoran tar Al'ummah.
Hakika Akwai Ciwo Da Bacin Rai Ga Wanda aka karkatak Da Hakkinsa, dole Ya koka Kuma bugu Da Kari dole Ya Nuna fishinsa.
To da Wannan Nake Kira Ga Shugaban Nin Jam'iyyar Mu Ta Rogo Sabon Gari Da ku Daure kuyi Abinda Ya Dace Domin Gaskiyar Magana Bai kamata Tun Yanzu ku,Tunzura Mutane Ba.
Kunyi Abinda baidace Kuma kunyi Kuskure, Muddin Ana bukatar aga Daidai tilas ku Rage son zuciya kuba Masu hakki hakkisu.
Domin Mun Samu Korafe Korafe Daga mabanbantan Yan"Jam'iyya Wadanda aka zalunta, ku, Da kanku kukace, A Wannan Tsarin kowanne agent Na akwatu, Da slot dinsa Amma Akwai agent Da Yawa Wadan Da aka Cire sunayen Su,aka saka Wasu.
Kuma Wannan zalunci ne, Wallahi muddun kukace Haka zakuyiwa Mutane a Wannan Lokacin Wallahi kwabarkuce zatayi Ruwa., Domin a Tsarin Kwankwasiyya Musamman a bana, kowa Yasan Yadda Mutane Sukayi Aiki tukuru Domin Samun Nasara, Amma Daga farawa har kun Soma Yiwa Al'ummah babakere.
Nasan Zaku ji haushi Amma Sai Mun fada muku gaskiya Domin Mu Bukatar Mu Shine Duk Wanda Ya wahaltawa Wannan Tsarin Shima Ya Sami Rabonsa.
Muddun bazaku Gyaraba To Su Mutane Ai Ba wawaye bane zasu Nemawa kansu mufuta, Ta Masu iya Magana Idan kunne Yaji To jiki Ya tsira.
Wallahi Duk Abinda kuke Ciki Mutane Suna sane Kuma taraku Suke, Daman Akwai sanayya Da Kara Da mutunci Da ake Ganin ku Dashi Amma, Daga lokacin Da Allo yaje Kala, Zaku gane kuranku.
Hannun Ka Mai sanda, Nasan Wannan posting din bazai muku dadiba To Amma tilas Sai Mun fada Kuma Idan Anyi Daidai Nan ma Mu fada.
Wanda Duk Yaji haushi Yayi Hakuri, Yayi Abinda Ya Dace Domin kaucewa Bacin Rai Na kowanne Irin al'amari.
Allah Yasa Mu Dace, Kuma Allah Yasa sakona yaje Inda ake bukata.!!!
M
Click here to claim your Sponsored Listing.
