Sunnah saka
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱصْبِرُوا۟ وَصَابِرُوا۟ وَرَابِطُوا۟ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ لَعَلَّكُم
18/02/2026
Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Muna Sanar da Ƴan'uwa cewa: Insha'Allah Gobe 2 ga watan Ramadan Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto zai fara Gabatar Da Tafsirin Al'qur'ani Mai Girma Na Wannan Shekarar 1447/2026 Kamar yadda aka saba.
Masallacin Aliyu Bin Abi Dhalib Dake Unguwar Koko Road A Cikin Babbar Birnin Sokoto
⏰. Ƙarfe 4:30 na Yamma
Sannan Zaku Iya Bibiyar Tafsirin Live a Facebook da YouTube ta Link dake Ƙasa:
YouTube: https://youtube.com/?si=GSdev4_DtTeEXb7K
Facebook: https://www.facebook.com/malambasharahamadsani?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
Allah Ya Karba Ibadunmu Kuma Ya Karama Malam Lafiya Amin.
21/09/2025
💞Sheikh Bin Uthaimin (Rh) Yace: "A kwaɗaitar da ƴan uwan mu akan yawaita addu'a ga iyayen su, suna raye ko sun mutu, domin hakan koyi ne da tafarkin ƴaƴan magabata waɗanda s**a yi koyi da faɗar Allah (ﷻ): "Ka kuma ƙasƙantar da kai gare su domin tausayawa, kace ya Ubangiji ka jiƙan su, k**ar yadda s**a jiƙaina ina ƙarami".
فتاوى نور على الدرب / ج1 / ص(2
20/09/2025
KUNYA ADON MACE
Gaskiyar magana shi ne duk wadda ya Rasa Kunyar sa toh fa rayuwar sa tana cikin Hatsari dadi anan duniya uquba a ranar Alqimaya, musamman ga ke Mace kene mutumiyar Farko da yak**ata a ce kina da Kunya over ga dukkan dabi'un ki da halayyen ki, shiyasa a yanzu da wai kai ya waye amma Hankali ya bata Mace ce Musulma iyayen ta Musulmai ne amma abun da ta ke aikatawa a social media da zahiri ko Arne ba zai yi hakan ba.
Mace Musulma ce zata fito a idon duniya ta gayawa duniya cewa ai saurayin ta yace ya gaji da zama a Hotel da ita shiyasa ya Siya mata gida na naira kaza ya Bata kuɗi naira kaza, don Allah Ina me Kunya ta ke anan?
Allah ya sa Mu Wanye Lafiya
Amin ya Rabbil Aalamin
______________________________
Islamic Graphics Designers
Abu Safwan Bin Maharazu
24/08/2025
Hukuncin Wanda ya saki matar sa cikin fushi
👇🏾👇🏾👇🏾
Mutane na yawan tambaya akan wanda ya saki matarsa a cikin fushi.
Ba wanda ke sakin matarsa cikin nishadi da wasa. Mafi yawa fada da fushi kesa ayi saki. Idan akace ba saki ga wanda ya saki matarsa a fushi wannan yana nufin ba ko wanne irin saki kenan. Wannan ba haka bane.
Abinda wancen hadisin yake nufi shine إغلاق wato mutum yakai lokacin da bai san mi ya fada ba, bai san me ake ciki ba, Kamar yadda Shaikhul Islam, Ibn Taymiyyah ya ke cewa:
وحقيقة الإغلاق أن يُغلَق على الرجل قلبه ، فلا يقصد الكلام ،
أو لا يعلم به ، كأنه انغلق عليه قصده وإرادته
Kuji tsoron Allah ku rike matanku kuyi hakuri.
Ku daina baiwa kanku fatawa. Mutum ya saki matarsa saki uku ya dawo yace ai na ukun yana cikin fushi ne.
Wallahu A’alam
Dr Jabir Sani Mai Hula
*_Yakai Dan Uwa Musulmi_*
*Annabi* (ﷺ) Yasha Wahala saboda nida kai *Annabi* An kore shi daga garin da ya Zauna😭 *Annabi* Yayi Hijira yabar garinda Aka haife shi😭 ya fita Ya tsaya Bayan gari yana cewa....😭 badan bana Sanki bane na fita Saboda An kore nine na barki😭😭 Amma kece Mafi Soyuwan gari A waje na😢 Amma haka *Manzon Allah* (ﷺ) Yabar Garin Saboda Yayi Hijira da *Musuluncin* da Yau nida kai Muke Tak**a dashi😭😭 Dan Uwa ka Suranta Rayuwar babu Musulunci kaga ya Zata Kasance? Kaje duniyar da S**a fi kowa Wayewa a yau Wadanda S**aqi Musulunci kaga irin Rayuwar *Dabbobi* da Suke In badan shi ba Wllh Ba *mamakin Nida ku yanzu ba Musulmai* bane🥺 Da baka san *Sujuda* da *Ruku'u* ba da ba kasan yadda Ake *Sallah* ba da duk Mun Zama k**ar *Dabbobi*😢 da kowa aka ce ya nuna Mahaifin sa wllh bai isa ya Nuna ba😭
*Amma* duk da haka Wannan *Annabin* ne zaice kayi kuma kaqiyi Yace ka bari kaqi bari Anya kuwa Kana san tsira Arayuwarka ta duniya da lahira?
_Ka bawa kanka Amsa broh and sister_
*_Da'awa Fisabilillah_✍*
*FALALAR KWANAKI GOMAN ZHUL-HIJJA (2)*
Cigaba da bayani game da falalar waɗannan kwanaki masu albarka, munji yadda Allah yayi rantsuwa dasu, sannan kuma ya ƙirasu da kwanaki sanannu, awannan rubutun kuma zamu kawo hadisai da suke nuni bisa ga falalar waɗannan kwanaki masu albarka.
1️⃣ *HADISI NA FARKO:-* An karbo daga Sahabi Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda dashi yace manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace "Babu wasu kwanaki wanda aiki acikinsu yafi soyuwa ga Allah fiye da kwanaki goma na farkon zhul hijja" sai sahabbai s**a ce ya manzon Allah har da jihadi don ɗaukaka kalmar Allah? sai yace eh! har da jihadi sai dai mutumin da ya fita dashi da dukiyarsa kuma babu abinda ya dawo daga cikinsu".
أبو داود ٢٤٣٨
2️⃣ *HADISI NA BIYU* An karɓo daga Sahabi jabir Allah ya yarda dashi yace manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "lallai kwanaki goma sune kwanakin goman layya, witiri kuma shine ranar arfa, shafa'i kuma shine ranar sallar layya"
مسند الامام أحمد ٣/١٤٥٥١
3️⃣ *HADISI NA UKU:-* An karbo daga Sahabi Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda dashi yana cewa manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "babu wani aiki wanda yafi tsarkaka a wajen Allah sannan kuma yake da girman lada fiye da aikin da aka yishi acikin kwanakin goman layya" sai akace masa harda jihadi? sai yace eh! harda jihadi sai dai wanda ya fita da dukiyarsa, sannan babu wanda ya dawo acikinsu".
سنن الدارمي ٢/١٧٧٤
Daga waɗannan hadisan zamu fahimci cewa haƙiƙa wannan kwanaki suna da falala mai girman gaske, da kuma miza atsakanin kwanaki na shekara gabaɗaya, wanda mun ambaci yan kaɗanne daga cikin hadisan da suke magana akan falalar waɗannan kwanakin saboda gudun tsawaitawa.
Arubutu na gaba in Sha Allah zamu kawo muhimman abubuwa da waɗannan kwanaki s**a keɓanta dasu.
Mu haɗu akashi na uku.
Julaibeeb
29/11/1446
27/05/2025
Manzon Allah (ﷺ) Ya kasance yana fadin ALLAHU AKHBAR a yayin da yake haura tudu, yana kuma fadin SUBHANALLAH a yayin saukowa. [Sahihul Bukhari]
ayita maimaita Allahu Akhbar ne har a gama hawa haka ma za ayita maimaita Subhanallah har a gama sauka.
Note:
Akwai kuskure a rubutu farko da muka turo (typng error) wannan shi ne dai dai.
25/05/2025
Menene a ka hana wanda yake da niyyan yin layya aikatawa? shin kuma hanin ya shafi sauran iyalanshi?
Daga Ummu Salamah RA, cewa Manzon Allah ﷺ yace:" Idan kuka ga jinjirin watan Zhul hijjah kuma ɗayanku yana da nufin yayi layya, to ya kame daga aske gashinsa da kuma yanke ƙumbarsa. Muslim
A wata riwayar: "Kar da ya cire gashinsa ko wani abu na fatan jikinsa.
Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen ya ce: "Wannan hukuncin ya keɓanci wanda zai yi layyan ne, amma wanda yi mishi layyan za a yi to ba shi da alaƙa da wannan, domin Manzon Allah SAW cewa yayi: "Kuma ɗayanku yayi nufin yin layya.." bai ce: ko za a yi mishi layya ba, kuma saboda Manzon Allah SAW ya kasance yana yin layya wa iyalansa amma ba a naƙalto cewa ya umarcesu daga kamewa daga wannan ba(yanke ƙumba/farce ko fitar da gashi).
27/12/2024
﷽
Akwai sigogi guda bakwai da salati yake dasu, waɗanda s**a tabbata daga Manzon Allah ﷺ. Waɗannan Sigogin gasu k**ar haka;
1. Daga ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah ﷺ, ya ce: Manzon Allah ﷺ ya kasance yana cewa: "Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ahli baitihi, wa ala azwajihi, wa zurriyatihi, k**a sallaita ala Ibrahim, innaka hamidun Majid. Wabarik ala Muhammadin wa ala A~li baitihi wa ala azwajihi, wa zurriyatihi k**a barakta ala a~li Ibrahim, innaka hamidun Majid".
الألباني (ت 1420)، أصل صفة الصلاة 3/913 • إسناده صحيح
2. Daga Abdullahi Bin Mas'ud رضي الله عنه Manzon Allah ﷺ ya ce: "Idan ɗayanku yayi Tahiya a cikin sallah to ya ce:
"Allahumma salli ala Muhammadin wa ala A~li Muhammadin k**a sallaita ala Ibrahim wa ala A~li Ibrahim innaka hamidun majid, Allahumma barik ala Muhammadin wa ala A~li Muhammadin k**a barakta ala Ibrahim wa ala A~li Ibrahim innaka hamidun majid".
صحيح الجامع
3. Daga Ɗalhata Bin Abdallah رضي الله عنه Manzon Allah ﷺ ya ce: "Kuce:
Allahumma salli ala Muhammadin wa ala A~li Muhammadin, k**a sallaita ala Ibrahim, wa ala A~li Ibrahim, innaka hamidun majid, wa barik ala Muhammadin wa ala A~li Muhammadin k**a barakta ala Ibrahim, wa ala A~li Ibrahim innaka hamidun majid".
صحيح الجامع
4. Daga Uƙubatu Bin Amrin رضي الله عنه ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Idan kunyi salla kuce:
Allahumma salli ala Muhammadin, Annabiyil ummi, wa ala A~li Muhammadin k**a sallaita ala A~li Ibrahim, wa barik ala Muhammadin Annabiyil ummi, wa ala A~li Muhammadin k**a barakta ala a~li Ibrahim Fil Alamina innaka hamidun majid".
الألباني (ت 1420)، صحيح الجامع 670 • حسن • أخرجه أحمد (17113)، وابن أبي شيبة في «المصنف» (3370)، وعبد بن حميد في «مسنده» (234)، وابن خزيمة (711)
5. Daga Abi Sa'id Al-Kudry رضي الله عنه ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Kuce:
Allahumma salli ala Muhammadin Abduka warasulika, k**a sallaita ala a~li Ibrahim, wabarik ala Muhammadin Abduka warasulika wa ala A~li Muhammadin, k**a barakta ala Ibrahim, wa ala Ali Ibrahim".
الأل
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
FAGE

27/05/2025