Comr.Abdulfatah bala
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Comr.Abdulfatah bala, Kano.
26/11/2025
ALAMOMI 15 DA KE NUNA ZA KA YI NASARA A RAYUWA
1. Ba Ka kwaikwayon mutane ko bin dokokin su:
Ba ka yin abu don kawai kowa yana yi. Kana da naka tsarin kuma kana yin abin da ya dace da kai, ba abin da al'umma ta tsara maka ba.
2. Kana Riƙe da Addini da Ibada
Ba ka barin komai ya sha gabanka wajen bautar Allah. Ka san cewa nasara ta hakika tana hannun Allah ne, don haka kake ba shi muhimmanci fiye da komai.
3. Kana Kyautatawa Iyayenka
Ka dauki iyayenka a matsayin tsani na samun nasara. Addu'arsu ita ce makaminka. Kana yi musu biyayya da kyautatawa a kowane lokaci domin samun albarkarsu.
4. Ba Ka Dogaro Da "Motivation" Kawai
Kana aiki ko da jikinka baya so. Disiplin shi ne abin da ke kai mutum ga nasara a lokacin da karfin gwiwa ya ragu.
5. Faduwa Darasi Ce A Gare Ka
Idan ka samu matsala, baka karaya. Maimakon haka, kana duba inda aka yi kuskure ka gyara don ka dawo da karfi.
6. Ba Ka Neman Yabon Mutane
Ba ka damu da abin da mutane za su ce game da zabinka ba. Kana yin abin da ya dace ne don kanka, ba don a yaba maka ba.
7. Kana Jin Dadin Zama Kai Kadai
Ba ka jin tsoron kadaici. Kana amfani da lokacin da kake kai kadai wajen yin tsare-tsare da inganta rayuwarka.
8. Ka Fi Kowa Aiki Tukuru
Yayin da wasu ke barci ko hira, kai kana aiki. Nasara aiki ake mata, ba kyauta ake bayar da ita ba.
9. Kana Daukar Kasada
Tsoro baya gina gida. Kana sa hannun jarinka da karfinka akan abin da ka yarda zai haifar da ɗa mai ido, duk da hadarin da ke ciki.
10. Abokanka Kadan Ne Amma Ingantattu
Ba ka tare da mutanen da ba su da amfani a rayuwarka. Idan mutum ba ya kara maka ci gaba, bashi da gurbi a rayuwarka.
11. Kana Mai Da Hankali Kan Neman Kudi
'Yanci yana zuwa ne da samun dukiya. Ka san cewa idan ka mallaki tattalin arzikinka, ka mallaki rayuwarka.
12. Ba Ka Bata Lokaci Wajen Korafi
Idan matsala ta taso, kana neman mafita ne ba wai zama kana kukan abin da ya faru ba.
😎comr Abdulfatah Bala
we are together my friend
Comradeship for best future
Click here to claim your Sponsored Listing.
