Yusuf Abdulazeez
An artist, health record/ information manager ,education icon and political activist
30/04/2026
Da ɗumi-ɗumi: Kotun Koli ta bai wa David Mark nasara a shari’ar sa da Nafi’u Bala
Kotun Koli ta Najeriya ta yanke hukunci a shari’ar da ke tsakanin David Mark da Nafi’u Bala, inda ta bai wa David Mark nasara Amatsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa.
Kotun ta kuma yi watsi da wasu muhawara da aka gabatar a gaban ta, tana mai cewa ba su da muhimmanci ga shari’ar kuma ba su da tasiri wajen yanke hukunci.
Wannan hukunci na nuni da kawo ƙarshen takaddamar da ta dade tana jan hankalin jama’a a tsakanin ɓangarorin biyu.
Ku biyo mu domin jin cikakken bayani kan yadda shari’ar ta kaya.
30/04/2026
Masha Allah Alhamdulillah ,Allah ya Kara Dora Adalci Alan zalunci
Kotun Ƙoli ta amince da shugabancin David Mark da sauran shugabannin jam'iyyar ADC.
Ƙarin bayani na nan tafe...
25/04/2026
25/04/2025
TikTok · mister_jee5 49.9K likes, 904 comments. Check out mister_jee5’s video.
21/04/2025
🚨Gwamnatin Jihar Kano zata rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da Masarautar Morocco a fannoni daban daban, domin samar da makamashi, noma, kasuwanci da sauran wasu muhimman ɓangarori domin farfaɗo da tattalin arziƙin Jihar Kano.
Ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mai Magana da Yawun gwamnan Kano, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa yace, wannan na zuwa ne bayan ziyarar zuba jari da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranta zuwa ƙasar Morocco, inda s**a gana da hukumomi da dama na ƙasar.
Tawagar ta gana da manyan hukumomin Morocco, ciki har da Hukumar Samar da Makamashin wutar lantarki mai Ɗorewa ta ƙasar Morocco (MASEN), Hukumar OCP Africa, da Cibiyar Kasuwanci ta Casablanca.
Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano, Jabir Ali Dan'Abba, ya bamu labarin cewar yarjejeniyar za ta kuma shafi gano masu saka jari, hanyoyin samar da kuɗaɗe, da sabbin fasahohin ajiya da rarraba makamashi cikin sauki, musamman don amfanin masana'antu a Jihar Kano.
Tawagar ta ƙunshi masu baiwa gwamna shawara da Masu taimaka masa a fannoni daban daban.
Ziyarar na nuna babban ci gaba a ƙoƙarin Jihar Kano na neman haɗin gwiwar ƙasashen duniya don bunƙasa masana’antu, makamashi mai tsafta da ci gaban noma mai ɗorewa a Jihar Kano.
Click here to claim your Sponsored Listing.
