Mata Iyayen Al'umma

Mata Iyayen Al'umma

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mata Iyayen Al'umma, Health/Beauty, Kano, Kano.

11/02/2026
11/02/2026

Allah kasa muna cikin wadan da zasu riski Watan Ramadan suna masu Imani da Aikin nagari, Amin

03/02/2026

UWA

" Ita uwa ta ganka ma a zaune a dakin ta,
dadi ta ke ji. Duk girman ka "

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
( Hafizahullah )

Bin Mu'az Fago

01/02/2026

DUNIYA TAZO KARSHE KAMAR YADDA MANZON ALLAH ANNABI (SAW) YA FADA!

YACE! Idan Karshen Duniya yazo Zakaga Alamu Kamar haka:”*

*1.Masu Kudi Zasu Zama Marasa Godiyar Allah.*

*2.Ana gasar Gina Manyan Gidaje.*

*3.Baiwa Zata Zama Sarauniya.*

*4.Zina Zata Zama Abin Kwalliya Ga Al'ummah.*

*5.Za'a Yawaita Zubar Da Jinin Salihan Bayi.*

*6.Azzaluman Mutane Zasu Zama Shuwagabanni.*

*7.Lokaci Zai Zama Gajere,(Da Zarar Gari Ya Waye Sai Kaga Dare Yayi).*

*8.Zakaga Dan uwa Yana Gudun Dan Uwansa.*

*9.Addinin Musulunci Zai Kasu Kashi-Kashi.*

*10.Malaman Addini Zasu Zamo Masu S0n Duniya Da Abinda Ke Cikinta.*

*📌Innalillahi Wa innah Ilaihi Raju'un... Tabbass Wadannan*
*Alamomin Sun Bayyana Dikkansu📍*

*🤔 Ni Yanzu Tinanina Yaushe Zan Mutu Yau Ko Gobe...?*

*Kashe Ni Za'ayi, Ko Rashin Lafiya Zanyi, Ko Hatsarin Mota Zanyi, Ko Zan Fada Cikin Rami In Mutu?, Ko Gobara Ce* *Sanadina, Ko Kuma Haka Kawai Zan Mutu....*
*Allahu A'alam.*

*Allah Kasa Muyi Kyakkyawan Karshe Allah Kasa Mu Mutu Da Kalmar Shahada Amin summa Amin!*

*Idan Na Taba Zaluntar Ka/Ki Ina Neman Gafarar Ka/Ki Kafin In Koma Ga Allah Domin Naji Allah Yace Baya Yafe Laifin Dake Tsakanin Bawa Da Bawa.*

*Tunatarwa*
*Ankawo Facebook ka iya,*
*Ankawo WhatsApp ka iya,*
*Ankawo Instagram ka iya,*
*Ankawo Twitter Ka kware,*
*ko wane irin Chatting Ka iya.*

*Shin Ka kware wajen karanta Alqur'ani da sanin Tajwidin sa?*

*Kuma duk yarigasu jimawa a duniyar nan.*
*Dan uwa hakika akwai babbar asara idan baka iya karanta Qur'ani ba ko daidai da hizif 1 ne.*

*Manzon Allah (S.A.W) ya ce*:- *Azumi da Qur'ani suna ceto*
*ranar Alqiyama ga ma'abotansu.*
*Yan Uwa mu kasance ma'abota Qur'ani ba ma'abota social media ba.*,,

TUNA TARWA CE. 🙏

Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah 💕

01/02/2026

Tasirin zunubi wajen kawo cikas ga rayuwar ɗan Adam

Zunubi na da babbar illa ga rayuwar ɗan Adam, tun daga zuciya, zamantakewa, har zuwa rayuwar addini. Ga wasu muhimman tasirinsa:
1. Rashin kwanciyar hankali a zuciya
Zunubi na jawo damuwa, tsoro, kunya da nadama. Mutum kan rasa salama a zuciyarsa saboda jin laifi ko tsoron sakamakon abin da ya aikata.
2. Nisanta mutum daga Allah
A addini, zunubi na sa mutum ya yi nisa da Allah, addu’o’insa su rage ƙarfi, ibada ta yi masa nauyi, kuma imani ya fara rauni.
3. Lalacewar ɗabi’a
Idan mutum ya saba da zunubi, hankali da kunya kan ragu. Abin da a da yake gani a matsayin ba daidai ba, daga baya sai ya fara ganin kamar abu ne na al’ada.
4. Matsaloli a zamantakewa
Zunubi kamar ƙarya, cin amana, zalunci ko hassada na jawo rikici tsakanin mutane, karya amana, da rushe dangantaka a cikin iyali da al’umma.
5. Tasiri ga rayuwar yau da kullum
Wasu zunubai (kamar shaye-shaye, sata, ko zina) na iya jawo talauci, cututtuka, matsalolin doka, ko rasa mutunci a idon jama’a.
6. Illar a tsawon lokaci
Idan ba a tuba ba, zunubi kan tara duhu a zuciya, ya sa mutum ya kasa bambance tsakanin gaskiya da ƙarya, har ya kai ga lalacewar rayuwa gaba ɗaya.

Kammalawa:
Zunubi ba wai kawai laifi ba ne, illa ce ga rayuwar mutum gaba ɗaya. Amma abin da ke da muhimmanci shi ne tuba na gaskiya, neman gafara, da ƙoƙarin gyara hali, domin hakan na dawo da kwanciyar hankali, albarka, da kyakkyawar rayuwa.

Allah ya raya zuciyar mu da imani ya ƙarɓi tubanmu.

01/02/2026

MUHAWARA: Shin Kana Ɗaya Daga Cikin Kanawa Da Zasu Sake Zaɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf A Matsayin Gwamnan Jihar Ta Kano A Zaɓen 2027 ?

A Kafta....

01/02/2026

Najeriya ce kasa ta biyar da ta fi yawan Musulmi a fadin duniya a kididdigar da Insider Monkey ta fitar a 2025.

15/01/2025

RANA TA BIYU

MARKAZ KHULAFAIIRASHIDIN

"Da Hausa ya kamata a rika koyarwa a makarantu," Gwamna Bago ga gwamnonin Arewa 15/01/2025

"Da Hausa ya kamata a rika koyarwa a makarantu," Gwamna Bago ga gwamnonin Arewa Gwamma Muhammed Umar Bago ya shawarci gwamnonin Arewa su maida Hausa ya zama yaren da za a rika koyar da ɗalibai a makarantun firamare da sakandire.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano
Kano