Muhammad Hamza Yahaya Smart

Muhammad Hamza Yahaya Smart

Share

Always Remain calm what belongs to you will be yours no matter what the situation is.

18/09/2024

Abinda Ya Kamata Ku Fahimta Akan Case Ɗin Seaman Abbas Ta Fuskar Tsaro

Daga Datti Assalafiy

Case din Seaman Abbas ya fara ne da cewa, an turasu wani special operation a jihar Taraba karkashin jagorancin Kwamandansu MS Adamu.

Watarana sai wani abu ya faru, Kwamandan su Abbas ya kira Sojojinsa, kowa yana nan sai Seaman Abbas ne baya nan yaje Sallah, bayan ya dawo Kwamandan ya haushi da fada yace a kwace bindigarsa.

Kamar yadda matar Abbas ta fada, anan ne Abbas yaki bada bindiga, har a gurin kokarin kwace bindigarsa bindigar ta tashi, sai Kwamandan ya zargeshi da laifin yunkurin kashe shi, akan wannan dalili ne MS Adamu yayi sanadin zaman Abbas a kurkuku na tsawon shekaru 6.

Mu Duba Abin Ta Fuskar Tsaro 👇

(1) A dokar aikin Soja da Police, idan ka je Armoury (dakin ajiyar makamai) kayi signing na bindiga da sunanka da Force Number/AP Number ko Service Number ka fita bakin aiki, to ko Shugaban Sojoji ko Shugaban 'yan sanda bai da ikon yace zai karbi bindigarka, sai idan ka mayar da bindigar kayi signing na returning of Arms, wanda yake da wannan ikon karban bindigarka ko baka dawo da ita ba shine General Commander in Chief... wato Shugaban Kasa.

(2) Idan kai jami'an tsaro da ka dauki bindiga daga Armoury sai Oganka yace ka bashi, sai kayi wauta ka bashi, idan yaje ya boye bindigar kuma yace baka bashi ba, kai za'a tuhuma ba shi ba, domin sunanka ne ke kan bindigar a cikin takadda na Movement of Arms.

(3) Shiyasa idan Soja ko Police ya dauki bindiga ya tafi bakin aiki, sai aka kashe shi aka dauke bindigarsa, farkon abinda za'a fara tambaya shine ina bindiga? domin a ka'idojin aikin bindiga tafi rayuwar jami'an tsaro muhimmanci, dalilin fadin hakan shine, ai rayuwarka kai kadai aka rasa, ita kuma bindigar za'a iya zuwa a kashe dubban mutane da ita, wannan kenan!

(4) Idan kun fahimci wannan jawabi da nayi a sama, zaku fahimci cewa Seaman Abbas yayi daidai da ya hana Kwamandansa karban bindigarsa, sam bai yi laifi ba anan.

(5) Kurkuku (Cell) na 'yan sanda da Sojoji Guard room ko Quarter Guard bai da maraba da dakin kwanan non-commission officers (jami'an tsaron da basu kai matakin one star ba) za'a iya kulle Soja ko Police a cell dinsu har yayi ritaya, ba laifi bane duk a cikin aiki ne, Civilian ne dokar Kasa tace kar a kulleshi a Cell fiye da awa 48 ba tare da an kaishi Kotu ba, idan kun fahimci wannan kulle Seaman Abbas da akayi a cikin Cell na Sojoji ba laifi bane a ka'idar aikin.

(6) Soja da Police basa zuwa Kotun da ake kai fararen hula, domin suna da nasu Kotun, Sojoji suna da Kotun da ake kira da Court Marshall yayin da Police suke da Kotun da ake kira Orderly Room Trial, ba'a yiwa jami'in tsaro tuhuma a Kotu idan bai da lafiya, tsare Seaman Abbas a Cell tsawon shekaru 6 zai iya zama laifi idan anci zarafinsa ta hanyar azabtarwa ko an hanashi neman magani, domin ba za'a iya masa trial alhali bai da lafiya ba.

(7) Tsarin Kotun Sojoji Court Marshall yana da matukar wuyan sha'ani, Soja yana shafe tsawon shekaru yana jiran Trial ba'a masa ba, wannan yana daga cikin kuskure ko babbar matsala dake faruwa a gidan Soja, Soja yayi kwana 40, wata uku, shekara daya a kulle cikin kurkuku wannan ya zama ruwan dare, saboda aiki ne mai tsauri gaskiya, musamman idan anyi rashin dace da mugun Oga.

(8) A karshe muna fata kadiyyar Seaman Abbas zata bude wani sabon babi da zai kawo gyara mai ma'ana game da cin zalin da Manyan Jami'an tsaro suke yiwa kananan officers tunda yanzu Majalisar wakilai na tarayyar Nigeria ta shiga cikin lamarin.

Muna fatan Allah Ya tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria.

19/08/2024

Shirye-shiryen gudanar da sabuwar zanga-zanga sun yi nisa bayan gwamnati ta kasa biyan bukatun da aka nema - Karin bayani a sashen sharhi.

31/07/2024

KIRA GA GOVT. DAWO DA
INGANTA
BUDE ( )
DAI TA FARASHI

29/04/2024

Zalunci ne da haúka tuburañ ka baiwa Ma'aikaci albashin Nera dubu 30 tare da sanin baza ta ishe shi kwana talatin yana cin abinci da su ba, wai shin da wane irin kwakwalwa muke lissafi? Sheíkh Maqari Abuja Central Mosque

DAGA Shuaibu Abdullahi

19/04/2024

Alhamdulillah An sanya masa suna Muhd Al-Amin Allah ya rayashi akan tafarki madai daici, Allah ya Amintar dashi da dukkan alkhairi, Allah ya Albarka ci rayuwarsa 🤲🏻

23/03/2024

Guess the city 🤣

An ce a wani gari layi ake don a karbi sadakar wannan 😅

Ko meye gaskiyar wanga batu, nidai na fece 😂🏃

14/01/2024

Kano sabuwa kowa “murna” yakeyi Alhamdulillah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻

09/01/2024

Fatan alkhairi agreku friends & family🤝

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Kano City
Kano