MS GARO

MS GARO

Share

Sani Aminu Garo
Proudly Nigerian
Patriotic
Interest in politics
Graduate from K.U.S.T WUDIL

Photos from MS GARO's post 16/05/2026

KODA TAKARA KO BABU!!!

FAHAD DANKABO SUPPORT ORGANISATIONS(F.S.O.) GWARZO/KABO!!!

MUNATARE DA MAGAJIN JARMA!!!

A Mamadin duka Shugabanchin wannan ƙungiya na kabo/Gwarzo, tunda ga matakin mazaɓa har zuwa local government, da Kuma membobi sama da dubu ɗaya (1000).

Muna Amfani da wannan dama domin jaddada mubayi,a ga Mae jagora Hon (FAHAD ADAMU DANKABO), a kowanne irin hali da Kuma lokachi, koda takara ko babu.

Jagora ya nunawa duniya cewa shine jajirtaccen jagora Kuma Shugaban juyin juya hali a siyasar wannan zamanin ta gwarzo/Kabo Kuma ɗaya tamkar da dubu Wanda ya tsaya Shi ƙadai domin ƙwatowa Al,umma hakkinsu da kuma futar dasu daga halin dasu keciki na rashin nagartaccen wakilchi Kuma haƙiƙa ya nuna juriya da dattako akan abubuwan dasu ka faru, Kuma ya tabbatar da ƙudi basune a gabansa illa wannan takara ta Al,umma ce Kuma donsu akeyi Kuma baza a dena ba har Sai an ƙwato musu haƙƙinsu Kuma an tabbatar da abunda sukeso, Kuma ya tabbatar ba don kansa yakeyi ba Sai don mu da ku da Al,ummar yankin baki ɗaya, Wanda a kodayaushe yana faɗa rashin yin shine sauƙinsa Amma ganin halin da Al,umma suke ciki yasa dole a samun Jagoran da zai shiga gaba domin Samar da Canji a wannan yankin.

Kuma mun gamsu da manufofinka da tsare tsarenka, da gogewarka, da iliminka, da basirarka , da kuma jajircewarka da irin manufofi dakake dasu akan wannan yankin namu na alheri, Mun gamsu cewa zaka iya Kuma Zaka Samar da kyakyawan yanayi a siyasar wannan zamanin domin kawo gyara da Canji ga Al,ummar mu.

Wanda Idan da mutane sun san irin tanadin da ka yi musu da ko ƙudi a kache su bayar su zaɓeka zasu bayar domin kyakyawar zuciyarka da ƙudirinka ga wannan yankin.

Kuma wannan tafiya ba a Fara don a dena bah, yakasanche wata mafarin Tafiya mai tsayi da ta ke da ƙalubale da wahala da tsaunuka da kuma rashin fahimtar siyasar wannan zamanin ta mutanenmu,. Amma karshe za a yi nasara da ƙarfin Ikon Allah Kuma nasara gagaruma daza ta daɗe tana wanzuwa domin an gina tafiyar akan doron matasa masu

Photos from MS GARO's post 13/05/2026

Alhamdulilahi,

A Safiyar Yau Kenan Daga Malam Aminu Kano International Airport.

Na Raka Dan uwana Kuma Abokina Sadeeq Garo,

Domin Tafiya kasa Mai Tsarki Don Gabatar da Ibadar Aikin Hajji na wannan shekarar,

Muna addu,a Allah yasaukesu Lapiya Yasa ayi Ibada ƙarbabbiya ameen.

Photos from MS GARO's post 09/05/2026

Alhamdulilahi Alhamdulilahi,

Bro, fav cousin, age mate, living together in any circumstances,

Lokachi yayi,

Muna addu,a Allah s.w.t. yasa albarka a cikin wannan haɗin ya kaimu lokachin da ran mu da lapiyar mu.

Mu shaida wannan muhimmiyar rana,

Layi Kuma naja😂😂

08/05/2026

Jagora Fahad Adamu Dankabo

Allah ya iyamana duk abinda baza mu iyaba
Cikin sauki ameen,

Photos from MS GARO's post 30/04/2026

Alhamdulilahi Alhamdulilah,

A Yau Mai Girma Jagoran Hon Fahad Adamu Dankabo.

Ya Mika takardar buƙatar tsaya takara ta Danmajalissar tarayya Mai wakiltar gwarz da kabo a kakar zabe Mai zuwa ga shugabannin jam, iyyar A.P.C. a matakin karamar hukumar Kabo da kuma gwarzo.

A Wani irin Salo na ban mamaki daya kasanche mutum na farko da ya nuna buƙatar hukumanche,

Kuma taron yasamu halartar, shuwagabanni daga Kowanne ɓangare na wannan yankin da Kuma

Kungiyoyin matasa da Mata da kuma kuma yan gwagwarmaya masu son ganin wannan yanki yasamu wakilchi na gari a majalissar ƙasa.

Muna godewa kowa da yasamu halartar wannan gagarumin gangami da ma masu fatan alheri,

Allah yasa wannan mataki yazama alheri ga Mae girma jagora, da Al,ummar wannan yankin baki ɗaya ameen.

HON FAHAD ADAMU DANKABO FOR MEMBER HOUSE OF REPRESENTATIVE KABO /GWARZO KANO STATE 2027.

Magajin Jarma Alherine!!!

Sponsored by fahad Dankabo support organisations,,,

22/04/2026

Alhamdulilahi,

Your Hardwork and Patience is truly paid of Sir,

Congratulations Sir,

Allah yayi Riko da hannayenka ameen.

Photos from MS GARO's post 20/04/2026

( A HUKUMANCHE)!!!

A yau Mai Girma Jagoran Hon Rabiu Sayyadi Kazode, tsohon dantakarar majalissar jiha a kakar zaɓen data gabata Kuma tsohon Jagoran Jam iyyar P.D.P.

A Yau a mazaɓar sa ta masanawa a gaban duk kan dubban masoya da magoya ya baya an shaida kammala komawa jam,iyyar( A.P.C.) a wannan Rana Mai Albarka,

Akwae dukkan Shugabanchi tunda ga matakin mazaɓu harzuwa karamar hukuma Kuma sun yarda sun aminche.

Muna addu,a Allah yasa Hakan yazama alheri ga jagora, damu da ma karamar hukumar mu da jihar mu baki daya ameen.

09/04/2026

Innalillahi Wa Inna Ilahin Rajiun,

Allah yayiwa kakanmu Alh Umar Sule Garo Rasuwa Yanzu Haka (Wanda aka fi Sani da( ummaru dabai).

Za ayi jana,izar Kamar yanda addini ya tanada a gidansa dake garo tsohon gida kusa da gidan Inuwa Custom,

Muna addu,a Allah yajikansa yagafartamasa yasa aljannah makoma ameen da Duk sauran iyayenmu ameen,,,

Photos from MS GARO's post 07/04/2026

(TARON MASU RUWA DA TSAKI NA JAM, IYYAR P.D.P A MATAKIN KARAMAR HUKUMAR KABO)!!

A Mamadin Mai Girma Jagoran Jam iyyar P.D.P, A Matakin karamar hukumar Kabo( Hon Rabiu Sayyadi Kazode.). Kuma tsohon dantakarar majalissar jiha a Zaɓen da ya gabata na 2023.

A Yau 07/04/2026 ƙarƙashin shugabancin jam, iyyar P.D.P. a matakin karamar hukumar Kabo.

Mai Girma shugaban Jam iyya (Hon Aminu Garba AAK). Ya Jagoranchi taron masu ruwa da tsaki daya gudana a mazaɓar Garo, Wanda taron ya haɗa duka shugabannin jam, iyya a matakin karamar hukuma da duka shugabannin mazaɓu goma damu Ke dasu da Kuma sakatarorinsu da shugabannin matasa da Mata, da Yan social media da duka masu ruwa da tsaki na gidan siyasar jagora Hon Rabiu Sayyadi Kazode.

An tattauna muhimman batutuwa Kamar haka,

1) An tattauna halin da jam, iyyar p.d.p. take ciki tun daga faɗin kasa zuwa jiha da matakin ƙananan hukumomi.

2) An tattauna akan batun siyasar gidan Mae girma jagora Hon Rabiu Sayyadi Kazode.

3) An tattauna Domin samar da makoma ga dukkan magoya baya duba da yanayin da akeciki a yanzu.

4) An cimma matsaya cewa duka Shugabanchin wannan jam,iyya tundaga
matakin mazaɓa Har karamar hukumar Suna tare da Mai girma jagora da duk irin matsaya da ya ɗauka anan gaba.

5) A karshe an jinjinawa masoya da magoya baya duba da irin goyon baya ba dare ba rana acigaba da hakuri da juriya, yayinda ake jiran saƙon mai Girma jagora akan matsayar sa da zai futar anan gaba kaɗan.

Muna addau,a Allah yasa wannan matsaya da jagora zai futar ta zama alheri ga shi garemu da dukkan Al,ummar karamar hukumar kabo Ameen.
(TARON MASU RUWA DA TSAKI NA JAM, IYYAR P.D.P A MATAKIN KARAMAR HUKUMAR KABO)!!

A Mamadin Mai Girma Jagoran Jam iyyar P.D.P, A Matakin karamar hukumar Kabo( Hon Rabiu Sayyadi Kazode.).
HON RABIU SAYYADI KAZODE FOR MEMBER HOUSE OF ASSEMBLY KABO LOCAL GOVERNMENT KANO STATE 2027!!!

Announce by Party Local Government P.R.O.II Sani Aminu Garo for Party Local Government Chairman,
Hon Aminu Garba AAK!!!

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Garo Sabuwar Unguwa
Kano
111111