Vision FM Kano

Vision FM Kano

Share

VISION FM KANO 92.5
SAMAR MUKU DA SAHIHAN LABARAI A KODA YAUSHE SHINE MURADIN MU. MIKIYA MAI HANGEN NESA

18/07/2026

‎Comrade Mujahid Muhammad, ya yi kira ga Soja Boy da ya janye kalamansa kan jihar Kano tare da bai wa al’ummar Jihar haƙuri.

‎A cikin wata sanarwa, Mujahid Muhammad ya ce kalaman da Soja Boy ya yi, na cewa “a duk faɗin Najeriya babu inda ake da ’yan luwadi k**ar Jihar Kano,” ba su da hujja kuma sun ɓata sunan al’ummar jihar.

‎Ya ce ya na magana ne a madadinsa da kuma duk wani mutumin kirki a Jihar Kano, inda ya buƙaci Soja Boy ya janye kalaman tare da neman afuwa cikin sa’o’i 24.

‎Mujahid Muhammad ya ƙara da cewa idan ba a janye kalaman ba tare da neman afuwa ba, zai ɗauki matakin shari’a.

Photos from Vision FM Kano's post 17/07/2026

CIKIN HOTUNA: Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf tare da Sanata Rufa'i Sani Hanga a ofishin Gwamnan dake Abuja.

📸 Arewa Updates

16/07/2026

‎Wallahi, a duk faɗin Ƙaramar Hukumar Kabo, babu wanda zai musanta irin ayyukan ci gaba da Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume, yake aiwatarwa a dukkan mazabu da ƙauyukan yankin. Ayyukansa suna bayyana a fili, kuma al'umma na ganin sauye-sauyen da aka samu.

‎Saboda haka, ina kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya ci gaba da bai wa Hon. Lawan Najume cikakken goyon baya a cikin wa'adin mulkinsa, domin ci gaba da kawo ayyukan alheri ga al'ummar Kabo da kuma ƙara ƙarfafa nasarar jam'iyya a zaɓen 2027.

‎Daga:
‎Comrade Salisu Abubakar
‎Secretary,
‎Zango Kabo Youth Development Association
‎(RCHP, B.Sc., M.Sc., PGDCHE)

16/07/2026

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Hon. Kabiru Alhassan Rurun ya raba takin zamani guda 2,635 ga manoma dake mazabun da yake wakilta domin tallafa musu wajen inganta fannin noma a kananen hukumomin.

16/07/2026

Idan da zan shiga Jam'iyyar APC, to zan tallata Gwamna Abba, wujiga-wujiga ma kuwa! domin a siyasa komai na iya faruwa a kowane lokaci...

Sanata Rufa'i Sani Hanga
‎Sanatan Kano ta Tsakiya.

📸Danuwa Rano TV

16/07/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Jamʼiyyar APC na ƙasa Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai wa Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rufaʼi Sani Hanga ziyara a gidansa dake Abuja, bayan wasu kalamai da Hanga ya furta dake nuna k**ar ya bar siyasar gidan Kwankwaso.

Me za ku ce?

📸 Arewa Updates

15/07/2026

‎Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana’ar tura fina-finai da waƙoƙi (downloading) a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar. Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan gano cewa wasu masu gudanar da sana’ar na amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da s**a saɓa wa tarbiyya.

‎Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahidden Aminuddeen, ya bayyana cewa ba za a ƙara amincewa da ci gaba da irin wannan sana’a ba. Ya kuma ce an umarci jami’an Hisbah su k**a duk wanda aka samu yana gudanar da ita domin gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka.

‎Hukumar ta yi kira ga al’ummar Kano da su ba ta haɗin kai wajen tabbatar da bin wannan umarni, tare da taimakawa wajen kare tarbiyya da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.

15/07/2026

Martanin Gwamnan Kano ga Dan takarar Gwamna na jam'iyyar NDC Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Photos from Vision FM Kano's post 15/07/2026

CIKIN HOTUNA: An cire hotunan Kwankwasiyya da alamomin jam'iyyar NDC a ofishin Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rufa'i Sani Hanga.

📸: SIYASARMU TV

15/07/2026

Jagoran Darikar Ƙadiriyya, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya kai ziyarar goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a Abuja. Wannan ita ce ganawa ta farko a hukumance tsakanin shugabannin biyu, inda Sheikh Qaribullah ya taya gwamnan murnar nasarorin da gwamnatinsa ta samu tare da yi masa addu'ar samun ƙarin hikima, lafiya da dacewa wajen jagoranci.

‎Shehin malamin ya yaba da ayyukan ci gaban da gwamnatin Kano ke aiwatarwa musamman a fannonin gine-gine, ilimi da lafiya, yana mai ƙarfafa gwamnan da ya ci gaba da wannan kyakkyawan aiki. Haka kuma ya tabbatar masa da ci gaba da addu'o'i da goyon bayan mabiya Darikar Ƙadiriyya domin zaman lafiya, haɗin kai da cigaban Kano da Najeriya baki ɗaya.

‎A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Sheikh Qaribullah bisa wannan ziyara, yana mai cewa hakan alama ce ta kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da shugabannin addini. Ya kuma roƙi mabiya Ƙadiriyya da sauran ƙungiyoyin Musulunci su ci gaba da yi wa Kano da Najeriya addu'ar zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da haɗin kan ƙasa, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin da za su amfani al'umma.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Guda Abdullahi
Kano
700101