ADC Nigeria

ADC Nigeria

Share

Weds Media Images And Videos

21/05/2026

Hon. Ismail Aliyu Alkanawy ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC a matsayin dan takarar Majalisar Tarayya, bayan gudanar da zaben kato bayan kato.

Wannan nasara ba ta mutum daya ba ce, nasara ce ta daukacin yayan jam’iyya da masu fatan ganin cigaba da kyakkyawan shugabanci a Gwale. Muna mika godiya ta musamman ga shugabanni, magoya baya da duk wadanda s**a bada gudunmawa wajen ganin an gudanar da zaben cikin lumana.

Haka kuma, Hon. Ismail Aliyu Alkanawy yana kira ga sauran abokan takararsa da su zo a hada kai, a rungumi juna cikin fahimta da mutunta juna, domin a ci gaba da tafiya tare don ganin jam’iyyar ADC ta samu gagarumar nasara a babban zabe mai zuwa.

Alkanawy Reporters
21/05/26

15/05/2026

Hon. Isma’il Aliyu Alkanawy ya kai ziyarar girmamawa ga Rotimi Amaechi a gidansa dake Abuja, inda ya gabatar masa da form dinsa na neman takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Gwale. Ziyarar ta nuna kudurin sa na neman goyon baya da shawara daga manyan ‘yan siyasa domin kawo cigaba a karamar hukumar Gwale idan Allah ya bashi dama.

Alkanawy Reporters

Photos from ADC Nigeria's post 12/05/2026

A madadin Hon. Ismail Aliyu Alkanawy, muna sanar da daukacin al’ummar karamar hukumar Gwale da ma jihar Kano baki daya cewa, Hon. Ismail Aliyu Alkanawy ya sayi Form din tsayawa takara domin neman kujerar Majalisar Tarayya karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Wannan mataki na zuwa ne bayan tuntuba mai zurfi da al’umma da kuma nazari kan bukatar samar da sahihin wakilci mai anfani da ci gaban al’umma. Hon. Alkanawy ya kuduri aniyar kawo sauyi, tare da mayar da hankali kan ci gaban matasa, inganta rayuwar al’umma da kuma kare muradunsu a matakin kasa.

Muna kira ga daukacin al’ummar Gwale da su bai wa wannan tafiya goyon baya domin cimma burin samun wakilci nagari. Allah ya bamu nasara

Nagode.
Mustapha Dukawuya
Media Aide
Hon. Isma'il Aliyu Alkanawey

Photos from ADC Nigeria's post 10/05/2026

Kira ga al’ummar Gwale!💥💥💥💥

Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye domin kawo sauyi na gaskiya, mu chanza irin mulkin kama-karya da ya jefa al’umma cikin ƙangin bautar rayuwa a Gwale.

Mu haɗa kai mu zaɓi jajirtacce, nagari, matashi mai kishin talakawa, wanda ya cancanta ya wakilce mu da gaskiya da amana.

Hon. Ismail Aliyu Alkanawey
Dan takarar Majalissar Taraiya, Gwale Federal Constituency Na Jam’iyyar ADC

Tafiyar nasara, tafiyar sauyi!
Mu kwato ‘yancinmu, mu gina makomar Gwale mai haske.

Gwale sai Hon. Ismail Aliyu Alkanawey!
ADC sai nasara!

03/05/2026

ADC Ta Fitar Da Time table na zabukan Fidda Gwani Da Zasu Gabatar Gabanin Zaben 2027

Photos from ADC Nigeria's post 08/10/2025

A Tafiyar mu ta ADC Allah Bai Daura Mana Shakka ko Tsoron Wani Dan Jam'iyyar ba😎

Bamu Fara Domin mu daina ba💯
Bamu Fara Domin Muji Tsoron Wani Ba🥺

Munfara Tun 2023 Kuma Zamuyi Nasara 2027
Nigeria Itace Burin mu Domin Kowa yabar Gida Gida Yabarshi✊ Kasar mu abar alfaharin mu Nigeria 🇳🇬

ADC Arise and shine Nigeria ✊

08/10/2025

ADC

Photos from ADC Nigeria's post 03/07/2025

HML❤️

Photos from ADC Nigeria's post 30/06/2025

Kai Jama'ah 😂

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano