Baban gida mafaka

Baban gida mafaka

Share

I'm business Man

04/07/2026

Cikakkiyar Kissar Ummul Banin (A.S.) Bayan Karbala

Ummul Banin (Fatima bint Hizam al-Kilabiyya) ita ce matar Imam Ali (A.S.) kuma mahaifiyar Hazrat Abbas (A.S.), Abdullah, Ja'afar da Usman. Dukkan waɗannan 'ya'ya nata sun yi shahada tare da Imam Husaini (A.S.) a Karbala.

Lokacin da Imam Husaini (A.S.) ya nufi Karbala, Ummul Banin ta zauna a Madina. Kafin tafiyar, ta yi wa 'ya'yanta wasiyya da su kasance masu biyayya ga Imam Husaini (A.S.) kuma su kare shi da rayukansu.

Bayan faruwar masifar Karbala da dawowar ayarin fursunoni zuwa Madina, wani bawan Imam Husaini (A.S.) mai suna Bishr ibn Hadhlam ya shiga Madina yana sanar da mutane game da shahadar Imam Husaini (A.S.).

Da Ummul Banin ta ji hayaniyar mutane, sai ta fito tana tambaya:

> "Ya Bishr, me ka kawo na labarin Husaini?"

Sai Bishr ya fara cewa:

> "Allah Ya ba ki ladan hakuri kan shahadar ɗanki Abdullah."

Ummul Banin ta amsa:

> "Ban tambaye ka game da Abdullah ba. Ka gaya min labarin Husaini."

Sai Bishr ya ce:

> "Allah Ya ba ki ladan hakuri kan shahadar ɗanki Ja'afar."

Ta sake cewa:

> "Ina tambayarka ne game da Husaini."

Sai ya ba ta labarin shahadar Usman, ta sake maimaita tambayarta.

Daga nan ya sanar da ita shahadar Abbas (A.S.), wanda shi ne mafi shahara cikin 'ya'yanta. Duk da haka, Ummul Banin ta ci gaba da cewa:

> "Dukansu da abin da rana ta haskaka a kansa sadaukarwa ne ga Husaini. Ka gaya min abin da ya sami Husaini."

Lokacin da aka tabbatar mata da cewa Imam Husaini (A.S.) ma ya yi shahada, sai ta fashe da kuka mai tsanani tana cewa:

> "Yanzu ka yanke min jijiyar zuciyata. Duk 'ya'yana da abin da ke duniya fansa ne ga Husaini."

Wannan magana ta nuna irin girman soyayyarta ga Imam Husaini (A.S.) da biyayyarta ga Ahlul Baiti (A.S.).

Makokinta a Madina

Bayan dawowar ayarin Karbala, Ummul Banin ta kasance tana fita zuwa makabartar Baqi' tare da jikanta Ubaydullah ɗan Abbas. A can tana rera waƙoƙin makoki kan shahadar Abbas da Imam Husaini (A.S.).

04/07/2026
29/06/2026

ACIKIN TAPIAR BAUTAR DA TACIKA DA AZABA😭

Lokacin da ake tapiar da iyalan Imam Husaini (A.S.) amatsayin bayi ahannun azzaluman Banu Umayya, ana kaisu daga gari zuwa wani gari.Da rana ta faɗi, dare ya yi, sai ayarin ya tsaya na ɗan lokaci, Lokacin da s**a so su ci gaba da Tapia, sai s**a ga mashin da aka ɗora kan shugaban shahidai, Imam Husaini (A.S.), ya tsaya cak a cikin ƙasa, ba ya motsi ko kaɗan.
Mai ɗauke da kan, tare da wasu daga cikin mutanen Banu Umayya, s**a yi ƙoƙarin cire mashin, amma duk s**a kasa.
Abin ya ba su mamaki ƙwarai.

Me ya sa mashin ya ƙi motsawa?
Sai s**a tafi wajen Imam Zainul Abidin (A.S.) s**a tambayeshi abin da ya faru da kuma abin da zasuyi.Sai Imam ya umarci Sayyida Zainab (A.S.) data duba yara, ta tabbatar babu wanda ya ɓace.Sai Sayyida Zainab tafara ƙirga yaran ɗaya bayan ɗaya.Data gama, sai ta lura cewa ƙaramar 'yar Imam Husaini (A.S.), Sayyida Ruqayya (A.S.), wadda ake kira Fāɗima ƙarama, bata cikin ayarin.Saita sanar da Imam Zainul Abidin (A.S.).

Sai Imam ya ce wa azzaluman Banu Umayya:
Kan mahaifina Husaini ba zai motsa daga nan ba har sai ansami wannan yarinyar.Sai s**a fita suna nema, amma basu sameta ba.
Sai Imam yace musu Kubi inda idanun kan mahaifina suke kallon.Da s**a nufi wannan ɓangaren, sai s**a tarar da ƙaramar Ruqayya tayi barci a ƙarƙashin inuwar wata dabino.
Ta yi barcin ne saboda tsananin gajiya, dukan da aka yi mata, da kuma zafin yashin hamada, bayan ta gaji da tafiya da ƙananan ƙafafunta tana neman ayarin.

Sai ɗaya daga cikin azzaluman Banu Umayya yazo ya tasheta da harbin ƙafa, sannan ya ƙara dukanta da bulala.😭Da aka dawo da ita cikin ayarin, Sayyida Zainab (A.S.) ta rungume ta, ta share mata hawaye, ta kwantar mata da hankali.alokacin ne mashin dake ɗauke da kan Imam Husaini (A.S.) ya motsa daga inda ya tsaya.
Amincii ya tabbata ga marainiyar Husaini mai rauni, wadda taɓace daga ayari.
Amincii ya tabbata ga Uwar gidanmu Sayyida Ruqayya (A.S.), wadda aka zalunta kuma tayi Shahada 😭.

Lura: Wannan labari y

Photos from Baban gida mafaka's post 19/06/2026

MENENE MAKOMAR DORKIN IMAM HUSSEINI (A.S)?😭

AKWAI ZAFI SOSAI AKARANTA DA HAKURI👏😭

Da farko, ya dace a sani cewa dokin Imam Husaini (A.S) yana daga cikin dawakan da s**a kasance mallakin Annabi Muhammad (S.A.W.A). An ruwaito cewa:
Lokacin da aka kashe Imam Husaini (A.S), dokinsa ya fara yin ƙara da kururuwa yana ratsa gawarwakin da ke filin yaƙi ɗaya bayan ɗaya. Sai Umar bn Sa'ad ya gan shi ya ce wa mutanensa: "Ku k**a wannan doki ku kawo mini shi." Kuma wannan dokin yana daga cikin dawakan Manzon Allah (S.A.W.A).

Mawallafi Jawad Muhaddithi ya ce:

Zuljanah shi ne sunan dokin Imam Husaini (A.S) wanda ya hau a ranar Ashura. An kira shi Zuljanah ne saboda saurin gudunsa. Bayan Imam Husaini ya fāɗi ƙasa, dokin ya riƙa kare shi, yana kai hari ga mayaƙan maƙiya har ma ya kashe wasu daga cikinsu. Imam Husaini ya ci gaba da yaƙi a kansa gwargwadon ƙarfinsa, amma daga ƙarshe ya faɗo daga bayansa a ƙasar Karbala. Bayan shahadar Imam, dokin ya jiƙa gemunsa da jininsa, sannan ya nufi sansanin iyalansa yana yin ƙara tare da buga ƙasa da ƙafafunsa domin ya sanar da su shahadarsa. Da mata s**a ga haka, s**a fahimci cewa Imam Husaini ya yi shahada, sai kuka da kururuwa s**a tashi.
Bayan haka, malamai sun kawo ra'ayoyi daban-daban game da abin da ya faru da dokin Imam Husaini (A.S)

Ra'ayi na farko:
Dokin ya bugi kansa a ƙasa har ya mutu.
An ruwaito cewa bayan ya shafe goshinsa da jinin Imam Husaini (A.S), ya ruga zuwa sansanin mata yana yin ƙara, yana bugun kansa a ƙasa a gaban alfarwa har sai da ya mutu.

Ra'ayi na biyu:
Dokin ya jefa kansa cikin kogin Furat (Euphrates) ya ɓace.
An ce wani mutum mai suna Abdullah bn Qais ya ga dokin yana gudu bayan mutane sun kasa k**a shi. Ya kai hari gare su, sannan ya nufi kogin Furat, ya yi tsalle ya shiga tsakiyar kogin, daga nan kuma ya nutse, kuma ba a sake sanin labarinsa ba.

Ra'ayi na uku:
Dokin yana tare da Imam Mahadi (A.S).
Wasu malamai sun ce akwai yiwuwar dokin da Imam Husaini ya hau shi ne wanda daga baya ya ɓace a kogin Fura

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano