Fateemah Tv
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Fateemah Tv, Kano.
Fateemah TV
Gidan labarai, nishaɗi da tallace-tallace cikin gaskiya da kwarewa.
📺 Labarai
🎭 Nishaɗi
📢 Tallace-tallace
📩 Domin tallata hajarka a tuntube mu
https://www.youtube.com/@FatimaAbubakar-b7p
10/07/2026
SCHOLARSHIP: Shugaban Karamar Hukumar Buji,nNajeeb Falalu Ya Biya Kuɗin Karatu Ga Dalibai 197 Har Su Kammala Karatu
Shugaban Karamar Hukumar Buji a Jihar Jigawa, Arc. Najibullah Falalu, PhD, ya amince da cikakken ɗaukar nauyin biyan kuɗin karatu na dalibai 197 ‘yan asalin karamar hukumar, a ƙarƙashin Shirin Taimakon Dalibai na Matawalle, MSSP, har zuwa kammala karatunsu.
Cikin waɗanda s**a ci gajiyar shirin akwai dalibai 14 na fannin lafiya a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha da ke Jahun, dalibai 41 a Kwalejin Ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare, da kuma dalibai 142 a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Jama’are.
A cikin sanarwar da ya fitar, Arc. Falalu ya bayyana cewa wannan mataki zai tabbatar da ci gaba da karatun daliban ba tare da wata matsala ta kuɗi ba, kuma yana nuna ƙudirin gwamnatinsa na gina Mutane Musamman Matasa ta hanyar basu Ilimi.
Ya ƙara da cewa shirin ya yi daidai da Tsarin Aiki na Matsayi 12 na Gwamna Malam Umar Namadi, wanda ya sanya ilimi a matsayin ginshiƙi na cigaba mai ɗorewa a jihar.
“Ba za mu gaji ba wajen saka jari a ilimi, domin shi ne mafi girman jari da za a iya yi wa makomar al’ummarmu da cigaban Karamar Hukumar Buji,” in ji shi.
Juma'at Kareem ❤️
10/07/2026
Kotu Ta Soma Sauraron Ƙarar Da Gwamnatin Kano Ta Shigar Kan Zargin Wata Budurwa, Fati Cele Da Kashè Saurayinta.
Fateemah Tv
10/07/2026
AMEEN ya Allah
10/07/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Kira Da A Daina Fargaba Game Da Cutar Ebola Domin Ta Kafa Kwamitin Faɗakarwa Kan Tunkarar Cutar
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar wa da 'yan Nijeriya cewa a halin yanzu babu wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar Ebola (EVD) a ƙasar nan, yana kira ga jama'a da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati kaɗai.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wajen taron farko na Kwamitin Faɗakarwa na Ƙaramin Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Shirin Tunkarar Cutar Ebola da Barazanar Sababbin Matsalolin Lafiyar Jama'a.
Ya ce, "Ina so in tabbatar wa da 'yan Nijeriya cewa a halin yanzu babu wani mutum da aka tabbatar da ya kamu da cutar Ebola a Nijeriya. Sai dai abubuwan da ke faruwa a wasu sassan Afrika sun sake tunatar da mu cewa babu ruwan cututtuka masu yaɗuwa da iyakokin ƙasashe."
Idris ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa Kwamitin Shugaban Ƙasa, yana mai bayyana matakin a matsayin ɗaukar matakin rigakafi domin kare lafiyar 'yan Nijeriya ta hanyar kyakkyawan shiri, haɗin kai da kuma ɗaukar matakai cikin gaggawa.
Ya jaddada cewa faɗakarwa za ta taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da duk wani yanayin gaggawa da ya shafi lafiyar jama'a.
Ya ce, "Sahihan bayanai da ake fitarwa a kan lokaci kuma bisa hujjojin kimiyya na ceton rayuka, yayin da yaɗa ƙarya da ji-ta- ji-ta ke iya lalata amincewar jama'a tare da hana gudanar da ingantaccen martani."
Ministan ya tunatar da jama'a cewa nasarar da Nijeriya ta samu wajen daƙile cutar Ebola a shekarar 2014 ta samo asali ne daga shugabanci nagari, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, ingantaccen tsarin sa ido da kuma ci gaba da wayar da kan jama'a.
Ya ƙara da cewa Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta riga ta fara gangamin wayar da kai a faɗin ƙasar nan ta amfani da saƙonnin kiwon lafiya da aka amince da su, waɗanda aka tsara tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaki da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC).
Ya ce, "Saƙon mu ga 'yan Nijeriya dole ne ya kasance a bayyane: babu tabbataccen mutum da ya kamu da cutar Ebola a Nijeriya; babu dalilin fargaba; gwamnati ta shirya tsaf kuma tana ci gaba da sanya ido."
Idris ya buƙaci 'yan ƙasa da su kiyaye tsafta, su gaggauta sanar da hukumomin lafiya idan sun ga alamomin da ake zargin na cutar ne, tare da dogaro da bayanan da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar kaɗai.
Daga cikin manyan baƙi da s**a halarci taron akwai Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin; Ministan Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Harkokin Sararin Samaniya, wanda Mataimaki na Musamman kan Sadarwar Zamani, Saka Olugbenga, ya wakilta; Darakta Janar na Hukumar Yaƙi da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC), wanda Dakta Tochi Okwor ya wakilta; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu; Shugaban Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya; Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku; Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya na shiyyar Arewa, Hamza Idris; da sauran manyan baƙi..
10/07/2026
🕌✨ Juma'at Kareem ✨🕌
May Allah (SWT) accept our prayers, forgive our sins, and fill our hearts with peace, mercy, and endless blessings.
May this blessed Friday bring good health, happiness, success, and prosperity to you and your family. May Allah answer all our sincere supplications. Ameen.
— Fateemah Tv 📺
10/07/2026
🕌✨ Juma'at Kareem ✨🕌
May Allah (SWT) accept our prayers, forgive our sins, and fill our hearts with peace, mercy, and endless blessings.
May this blessed Friday bring good health, happiness, success, and prosperity to you and your family. May Allah answer all our sincere supplications. Ameen.
Juma'at Mubarak to all Muslims.
— Fateemah Tv 📺
10/07/2026
A Cikin Waɗannan Gwamnonin da S**a Mulki Jihar Gombe, Wa Kuke Ganin Ya Fi Kawowa Jihar Gombe Ci Gaba?
🗳️ Ku bayyana ra'ayinku a sashen sharhi cikin mutunci da girmama ra'ayin juna.
Fateemah TV 📺
09/07/2026
MASHA ALLAH TVET Training allowance ya koma 30k maimakon 22,500 Naira Amma dai wanda yacika sharadi zaici gajiyar shirin akwai tsare tsare masu tsauri dole kowa yaje sau 5 a sati Attendance sau 2 a rana 🤣🤣
09/07/2026
Na Taɓa Faɗawa Ƴan Bindiga Cewa Su Kashe Ƴan Uwana Dake Tsare A Hannunsu, Saboda Ni Ba Zan Biya Kuɗin Fansa Naira Milyan 300 Ba, Inji Gwamna Dauda Lawal.
Fateemah Tv
Click here to claim your Sponsored Listing.
