Husaini sahal
Husaini sahal
24/03/2026
Duk inda akaje aka dawo dai, ke mace ce wadda rayuwarki take bukatar tsantseni da kulawa akoda yaushe.
Yana da kyau ki sani cewa Jikinki ba kayan gwaji bane, da zaki baiwa ko wanne fasiki damar gwajin soket da sunan soyayya ba.
A matsayin ki na 'ya mace Shin a ina kika bar darajarki da mutunciki ?
Shin menene abunda saurayi zaiyi miki na rayuwa wanda iyayenki bazasu iya yi miki shi ba, ? Da har zaki bashi damar keta miki ragar mutunci kawai Saboda yayi miki karyar cewa yana sonki kuma zai aure ki.Yau wasu ‘yan mata suna banzatar da kansu da sunan soyayya.
Wallahi Ina mamakin yadda wasu matan suke mika jikinsu ga samari, suna zaton hakan shine soyayya.
Ya kamata mata ku sani cewa sufa Wasu samarin ba soyayya suke nema a wajenku ba, Magana ce ta bukata kawai, idan saurayi ya ganki yaji yana sha'awarki zaiyi maza ya lallabo da sunan soyayya, ya samu ya lallaba ki ya zare zaren yaci gaba da tafiya.
Shiyasa idan naga mace mai son abun duniya sai naji ina tausayin ta, Saboda yadda samari suke mai da ita motar haya kowa ya ganta a hanya kawai tarewa zaiyi ha hau.
Saboda haka Ina mai baku shawara tun kafin lokaci ya kure muku mata masu baiwa samari dama suna taba jikinku da sunan soyayya daku nake Wallahi muyiwa kanku fada duk namijin da kika sake kika baiwa dama yasan yadda k**e, to Ina mai tabbatar miki bazai aure ki ba, Wannan ita gaskiyar magana.
Ita Soyayya ta gaskiya tana tare ne da girmamawa, hakuri, da niyyar aure ba amfani da yaudara ba wajen cimma MURADUN marasa kyau ba.
Yana da kyau Ki kare kanki, Ki kare daraja kanki sannan Ki guji duk wanda yake neman jikinki kafin ya nemi zuciyarki da mutuncinki, Domin kuwa ke ba abar wasa bace ke daraja ce da allah ya shimfida sharuda kafin mallakarki.
Rubutuna na gaba zanyi shine akan .....!!
Daga karshe ina rokon ubangiji allah ya shiryar damu bisa tafarkin dai dai ya yafe mana kuskuren mu amin ya rabbil alamin 🤲
awacreation ✍️
21/01/2026
Tinkiya Uwar Timɓele, Bakisan Gariba Kace a Gaba 🚶🚶🚶🚶🚶🚶
Tsoro Na Kada Su gama Cinye wasan nasu Tun kafin A Tafi Knockout, Ana Fitowa a Musu irin na Liverpool 🤡
03/12/2025
KARDA mu MANTA da MATATTU 💔🥹
Kada ku manta da ƴan uwanku matattu Dan Allaah kuna saka su cikin addu’ar ku.
Allah Ya gafarta musu, Ya sanya su cikin Aljanna.
Domin babu abinda suke buƙata a wajen mu sai Addu'ar mu — walau iyayene, ƴan uwan mu ne, malaman mu ne, matayen mu ne, mazajen mu ne, yaran mu ne, Abokan mune, ƙawayenmu ne, ko na wa suke a wajen mu
Dan Allaah karda muna mantawa da su.
Dan Allaah ƴan uwa masu Albarka kada ku manta dasu domin yau suna cikin kabari su kaɗai.
Ba tare da kayaba,
Babu dukiya bare mota ko fitila.
Babu iyali a tare da su, kowa shi kaɗai zai zauna a cikin ƙabarin sa.
Abin da ya rage musu shi ne addu'ar ku kawai.
Wallāhi daga lokacin da kuka binne su — s**a fara fuskantar tashin hankalin da ake cikin ƙabari — sannan kuma duk addu'a guda ɗaya zinariya ce a wurin su , sai dai munyi buris dasu.
Dan Allah muna saka su cikin addu'a — ko babu naka wanda ya mutu, kana. Saka ƴan uwa musulmai domin watarana mune zamu mutu.
Mu ma muna tuna da cewa watarana duk zamu kasance cikin halin da suke a Yanzu.
Zamu kwanta a cikin duhun ƙasa, zamu bar duk abin da muka tara.
Ya Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe😭💔
Allah ka gafarta wa waɗanda s**a riga mu gidan GASKIYA, ka sanya masu ƙabarin su ya zama mai haske sannan ka sanya su cikin Aljannar Firdausi.
Allahumma Ameen 🥹 💚
Ahky Ameer ✍️
23/11/2025
Kawai rumfar s**a cire s**a siyarwa 'yan gwangwan amma sunce gyara s**ayi 😭
20/11/2025
Yanzu mene abunyi kenan🤔
19/11/2025
Acikin ziyarar da yariman ƙasar saudiyya (Muhammad Bin Salman) yakai wa shugaban America, yariman yana cewa:
"Osama Bin Laden" yaci amanar ƙasar saudiyyah
"Osama Bin Laden" ya kai harin (9/11) ne domin ya rosa kyakkyawar alaƙar dake tsakanin America da ƙasar Saudiyyah
Zasu kunyata Osama ta hanyar kyautata alaƙarsu da America, tare da zuba hannun jari mai ƙarfi domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Saudiyyah da tsaro
Hakazalika yariman Saudiyyah ya shaidawa shugaba "Donald Trump" cewa, zasu yaƙi mutane masu tsatstsauran ra'ayin addini muslunci a ƙasar Saudiyyah domin hana yaɗuwar mutane masu ra'ayi irin na "Osama Bin Laden"
Jaridar Newsweek America 🇺🇸
14/11/2025
Mun kammala da Hadiza Gabon yau, ranar Lahadi kuma zamu kara da Kabiru na Congo.
Allah ya dora mu akansa shima 😂
Sojan nan ya burgeni wallahi, acikin izza da sanin muhimmancin aikinsa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
KANO
