Arsenal zallah by H .A .D

Arsenal zallah by H .A .D

Share

Love Arsenal

12/09/2022

Thomas Partey ya dawo daukar horo ya atisaye Cikakke kafin karawa Arsenal da Brentford.

01/09/2022

Deadline Day!

Yau za'arufe kasuwar musanye yan wasan ƙwallon ƙafa a nahiyar turai.

Mekuke fatan ganin Arsenal tayi?

Ku kasance damu.

✍️✍️✍️
Prince Tije

01/09/2022

Arsenal na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Aston Villa Douglas Luiz a cewar wani rahoto safiyar yau.

-News Sky Sport

Rabi'u Umar

29/08/2022

Arsenal na zawarcin dan wasan Shakhtar Donetsk Mykhaylo Mudryk a matsayin dan na shida da take da burin kawowa a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta Wannan Lokacin . Kocin Gunners Mikel Arteta Tabbatar cewa yana bukatar dan wasan tsakiya Mai kai hari a cikin tawagarsa.

Lucas Paqueta ya kasance babban burin Arteta amma Arsenal ba ta da niyyar biyan Olympique Lyon farashin fam miliyan 55 Hakan yasa dan Wasan zai koma West Ham, Amma kungiyar Shakhtar Donetsk ta sanyawa Mudryk kudi fam miliyan 17 kuma a yanzu Gunners na duba yiwuwar kai tayin shi

Mykhaylo Mudryk ya buga wa Shakhtar wasanni 28, ya zura kwallaye biyu kuma ya taimaka sau goma Dan wasan tsakiya kwararren dan wasa ne wanda zai iya taka leda a wurare da yawa a fagen gaba amma galibi ya fi son bangaren hagu.

29/08/2022

Leicester na neman kusan £35-40m ga Yourri Tielemans. Arsenal ba ta da niyyar biyan irin wannan kudin ga dan wasan da ya rage shekara guda a kwantiraginsa.🔴🇧🇪



Arsenal ta nemi bayani akan Mykhaylo Mudryk.

Tattaunawa akan Neto yana da rikitarwa sosai, Wolves suna buƙatar sama da £50m.



Crystal Palace na son ci gaba da rike Zaha kuma ba za ta siyar da shi ba sai dai in sun sami kudin Mai yawa


"Tony Cascarino"

"Odegaard shine Kevin de Bruyne na . Ya mallaki komai. Babu abin da ba zai iya yi ba,

Kungiyar Southampton na matsawa kan daukar Ainsley Maitland Niles daga Arsenal. [


A HuKumance: An nada Paul Tierney alkalin wasan da zai hura Wasan Arsenal da za ta kara da Manchester United a Old Trafford ranar Lahadi, tare da Lee Mason na VAR. #

Chelsea da Leicester sun cimma matsaya kan Fofana, kungiyoyi na rububin O'Riley - BBC News Hausa 27/08/2022

Chelsea da Leicester sun cimma matsaya kan Fofana, kungiyoyi na rububin O'Riley - BBC News Hausa Chelsea ta cimma matsaya da Leicester City kan sayen dan baya Wesley Fofana, yayin da manyan kungiyoyi ke son Matt O'Riley na Celtic da Denmark.

Arsenal ta farko a bana da ta ci wasa uku a jere ta hau teburin Premier - BBC News Hausa 20/08/2022

Arsenal ta farko a bana da ta ci wasa uku a jere ta hau teburin Premier - BBC News Hausa Kungiyar Arsenal ta ci gaba da sa kaimi a kokarin taka rawar gani a kakar bana, inda ta doke Bournemouth da ci 3-0 ranar Asabar.

17/08/2022

Kungiyar OGC Nice dake ƙasar France nason dan wasan Arsenal wato Nicolas Pepe a matsayin aro.

Source: [L' EQUIPE]

✍️✍️✍️
Prince Tije

12/08/2022

MENENE PRIMIER LEAGUE FANTASY?

Dazu nasaka Link akan cewa munbude group na Fantasy duk wadda yake buga game na Fantasy sai ya Joining domin mu fafata.

Wasu suna tambaya akan menene Fantasy? Ya kuma ake buga game na Fantasy?

Ku karanta har karshe!!

To da farko dai Fantasy wani Game ne da gasar Primier League ta fito dashi dan baiwa masu kallon gasar Primier League damar wasa kwakwalwar su.

Wannan Game basai ansaka kudi ake bugashi ba. Bakuma kudi ake samu dashi ba.

Fantasy Wasa ne wadda da zai baka damar zaban yan wasa da kake bukata a gasar Primier League.

Duk wani dan wasa da yake buga gasar Primier League to akwai sunansa acikin wannan wasan.

Da farko idan kayi rijista da Fantasy zasu baka kudi £100m. Note: wannan kudi ba cire shi za'ayi a kashe ba, kar wani yafara tunanin shikenan yayi kudi.

Taya zanyi Rijista? Kuje Playstore ku Downloading Official App na Primier League zakuga Fantasy aciki sai kuyi Rijista.

Wannan £100m yan wasa zaka siyo dasu, wadda zaka hada team naka harda yan Benchi.

Kowana dan wasa yana da darajarsa wani £5m. Wani £4m. Wani har £10m suna kaiwa.

Ga yadda tsarin wasan yake...

Kamar wasan gobe...

Zaka iya siyan Ramsdale a matsayin Goal Keeper ka,

Ka dauko irin su Cancelo na man City su Arnold da sauran manyan yan wasan baya dae.

Haka zalika zakaje tsakiya ka dauko irin su De Bruyne da sauransu.

Idan akaje Attackers zaka iya dauko irin su Gabriel Jesus, sallah da kane.

Note: £100m. Dari kawai aka baka, da zarar ka sayi yan wasan da darajarsu ta haura £100m to bazaiyiwu ka buga game din ba.

Idan ka haɗa Team naka me yayi saura?

Misali: Ramsdale shine Goal Keeper ka, idan wasan Gobe Arsenal tayi Cleansheet to zaka sami points (Maki) sosae akan Ramsdale.

Idan Cancelo na Man City yana cikin Defence naka, sai yayi kokari s**a sami Cleansheet ko kuma ancisu amma shi yaci kwallo ko yayai Asists to kana da maki akansa.

To duk dan wasan da yayi kokari a cikin first Eleven naka zaka sami Points akansa.

To Points naka suna kara yawa ana kara maka yawan kudin da zaka hada team daga £100m zuwa wani abu.

Har akai matsayin da zaka iya hada team din da kakeso.

To dalilin bude group Shine...

Yadda Table na gasar Primier League yake to haka group din zai kasance.

Duk wadda yafi yawan Points shine na daya a table har zuwa karshen gasar Primier League dae.

To wasu group din suna saka kyauta idan an kammala gasar Primier League din duk wadda yazo na daya da na biyu da na uku ana basu kyauta.

Wannan shine Fantasy.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Lagos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Hyderabad
Lagos
09066025176