The Secretary Zaria LG
This is the official page of the Office of the Council Secretary, Zaria Local Government
16/07/2026
A yau, Sakataren karamar hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), wanda ya wakilci Shugaban karamar hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya ci gaba da aiwatar da manufar gwamnatin karamar hukumar ta bude kofa ga jamaโa tare da karษar mutane da kungiyoyi daban-daban a ofishinsa.
Daga cikin bakin da ya karba akwai ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ (๐๐๐๐
) karkashin jagorancin Umar AbdulโAziz. Kungiyar ta gabatar da kanta tare da bayyana manufofinta da ayyukanta, wadanda s**a hada da koyar da sanaโoโi, tallafa wa marayu, da kuma taimaka wa marasa galihu. Haka kuma, sun nemi hadin gwiwa da goyon bayan karamar hukumar domin bunkasa ayyukansu na ci gaban matasa da ayyukan jin kai.
A wata muhimmiyar ganawa kuma, Sakataren ya karษi tawagar matasa daga Unguwar Fatika, wadanda s**a kai masa ziyarar gaisuwa tare da gabatar da kansu, sannan s**a nemi tallafin ilimi ga wasu daga cikin alโummarsu. A take, Sakataren ya amince da biyan kudin rajistar jarabawar NBAIS ga mata bakwai (7), domin ba su damar ci gaba da karatunsu da kuma kyautata makomarsu.
Hakazalika, Sakataren ya karba ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐โ๐โ๐ ๐๐ ๐๐๐๐, wata sabuwar kungiyar mata da aka kafa domin koyar da sanaโoโi da karfafa tattalin arzikin mata. A yayin ziyarar, kungiyar ta gabatar da manufofinta tare da sanar da nada Sakataren a matsayin Ubangidanta, bisa laโakari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tallafa wa mata da ci gaban alโumma.
Wadannan ganawa da muโamaloli sun sake nuna irin salon shugabanci da gwamnatin karamar hukumar Zaria karkashin jagorancin Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga) ta runguma, gwamnatin da ke bude kofofinta ga kowa, tana sauraron koke-kokensu tare da daukar matakan da s**a dace. Ta hanyar tallafa wa ilimi, karfafa matasa, hada kai da kungiyoyin mata da na alโumma, gwamnatin na ci gaba da aiwatar da shirye shiryen da ke kawo ci gaba da inganta rayuwar alโummar Zaria.
Kadan daga cikin ayyukan alkhairi da manyan nasarori da tsare tsaren ci gaba da s**a shafi rayuwar alโummar Zaria da Kaduna na Mai Girma Gwamna Senator Uba Sani, kamar yadda Super Secretary, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), kullum yake bayyanawa masoya.
Ku kalla, ku saurara, ku kuma yada domin jamaโa su san abin da gwamnati ke aiwatar.
Uba Sani Sau Biyu Neโ๏ธ
15/07/2026
Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), a yau ya karbi bakuncin mutane daban-daban da kungiyoyi a ofishinsa, a matsayin wani bangare na ganawarsa ta yau da kullum da alโumma da kungiyoyi daga sassa daban-daban na karamar hukumar.
Daga cikin wadanda ya karba akwai ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐
๐๐๐๐ ๐๐๐๐ (๐๐จ๐ฅ๐ฅ๐ข๐ง๐ ๐๐ง๐ข๐ญ ๐๐๐๐๐๐ซ๐ฌ) ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐, wadanda s**a kai masa ziyarar girmamawa domin nuna godiya bisa kyawawan ayyukan da yake yi. Sun bayyana cewa sun dade suna jin labarin kokarinsa da tasirin shirye-shiryensa a sassa daban-daban na alโumma, wanda ya sa s**a zo domin su yaba masa da kansu. Har ila yau, tawagar ta sake jaddada goyon bayanta da cikakken biyayyarta ga jamโiyyar APC.
Sakataren ya kuma karbi bakuncin mambobin ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ (๐๐ฐ๐๐ซ๐๐๐ข ๐๐๐ญ๐ฎ๐ค๐ ๐๐จ๐ฎ๐ญ๐ก ๐๐๐ฏ๐๐ฅ๐จ๐ฉ๐ฆ๐๐ง๐ญ ๐๐ฌ๐ฌ๐จ๐๐ข๐๐ญ๐ข๐จ๐ง), wadanda s**a ziyarce shi domin nuna godiya bisa irin goyon bayan da yake bai wa matasa, tare da neman tallafi ga wasu daga cikin matasan alโummarsu.
Bayan tattaunawa da kungiyar, Sakataren ya amince da ba su gurbi a cikin shirinsa na tallafawa alโumma da zai gudana nan ba da jimawa ba, domin bai wa wasu daga cikin mambobinsu damar cin gajiyar shirin.
Yayin da yake gode wa tawagogin biyu bisa ziyarar da s**a kai masa, Sakataren ya bukace su da su ci gaba da hada kai domin ci gaban alโummominsu. Ya kuma tabbatar musu da cewa ofishinsa zai ci gaba da marawa duk wani kyakkyawan tsari da shiri baya, musamman wadanda ke inganta rayuwar matasa, ci gaban alโumma, da kuma muradun alโummar Karamar Hukumar Zaria baki daya.
14/07/2026
A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karbi bakuncin kungiyoyi, Cooperative Sicieties, da sauran masu ruwa da tsaki a ofishinsa, a wani bangare na ci gaba da huldarsa da alโummar karamar hukumar.
Baki na farko da s**a ziyarce shi su ne ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐
๐๐๐๐๐๐, inda s**a nuna godiyarsu ga Sakataren tare da tattauna yanda zasu hada gwiwa tsakanin kungiyarsu da gwamnatin karamar hukumar domin samun cigaba ga alโummarsu.
Sakataren ya kuma karbi bakuncin mambobin ๐
๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐, inda s**a gabatar da kungiyarsu, s**a bayyana ayyukansu tare da neman shawarwari kan yadda za su ci gaba da bunkasa.
Haka kuma, ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ (๐๐๐), wata kungiya da ta kunshi matasa masu tasowa a fannin waka, masu kirkirar bidiyoyin TikTok da sauran masu tasiri a kafafen sada zumunta, sun kai masa ziyara domin nuna goyon bayansu ga wannan gwamnati tare da bayyana aniyarsu ta shiga harkokin siyasa da ci gaban alโumma.
Mambobin ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ su ma sun kai ziyarar ban girma domin nuna godiyarsu ga Sakataren bisa irin goyon bayan da yake bai wa alโumma, inda s**a kuma mika masa hoto da s**a tsara da kansu a matsayin kyautar girmamawa.
Hakazalika, ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ sun ziyarci Sakataren domin nuna godiyarsu tare da gabatar da ayyukan da suke gudanarwa a cikin alโumma. A martaninsa, Sakataren ya ware musu gurbi biyar domin mambobin kungiyar su amfana da shirin tallafa wa alโumma da zai kaddamar nan ba da jimawa ba.
Sakataren ya kuma halarci taro tare da Shugaban Karamar Hukumar, da shugabannin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) da sauran maโaikatan lafiya na fadin Karamar Hukumar Zaria. Taron ya mayar da hankali kan hanyoyin magance matsalolin da ke fuskantar cibiyoyin kiwon lafiya domin inganta ayyukan lafiya ga alโumma. A yayin taron, Shugaban Karamar Hukumar ya karfafa gwiwar maโaikatan lafiya da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da jajircewa, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin karamar hukumar za ta ci gaba da ba bangaren lafiya kulawar da ta dace.
Daga bisani da yamma, Sakataren ya raka Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), wajen ziyarar taโaziyya, gaisuwar marasa lafiya, da kuma duba ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a sassa daban-daban na Zaria karkashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.
A jawabinsa, Sakataren ya gode wa dukkan kungiyoyi da mutanen da s**a ziyarce shi bisa irin kauna da goyon bayan da s**a nuna masa da kuma wannan gwamnati. Ya tabbatar musu cewa kofofin Sakatariyar Karamar Hukumar Zaria a bude suke ga duk wani mazauni, kungiya ko hadakar alโumma da ke da kyawawan manufofin da za su taimaka wajen ciyar da Zaria gaba. Haka kuma, ya bukaci alโummar Zaria da su ci gaba da bai wa gwamnatin Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga) cikakken goyon baya, yana mai jaddada cewa gwamnati na samun nasara ne idan ta yi aiki tare da alโummar da take jagoranta.
Tare zamuyi Nasara InshaAllah
Congratulations to tea Vendors ๐
Another massive empowerment by the Secretary is set to commence this August. Under the Mai Canter Micro Empowerment 2.0 initiative, where 500 tea vendors across Zaria will receive empowerment support.
11/07/2026
WEEKLY RECAP
This week, the Secretary to Zaria Local Government Council, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), continued to translate leadership into meaningful action through strategic interventions in education, infrastructure. Guided by the vision of the Executive Chairman, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), the week was defined by prompt responses to community needs, practical solutions, and effective project supervision.
๐ Kaku Community, Gyallesu Ward
During a community visit to Kaku in Gyallesu Ward, residents drew attention to the absence of a functional school, inadequate teaching personnel, and the lack of a polling unit.
Recognising the urgency of the situation, the Secretary immediately approved measures to strengthen access to basic education by:
โ
Personally engaging and sponsoring the salaries of four volunteer teachers.
โ
Donating two whiteboards, markers, and 100 exercise books.
โ
Providing teachersโ attendance/personnel registers.
๐ Supported Students of NAPAS, NUBA POLY
The Secretary also received EXCOS of the National Association of Polytechnic Accounting Students (NAPAS), NUBA Polytechnic Chapter, who appealed for assistance over deteriorating lecture halls caused by leaking roofs.
Following the engagement, immediate interventions were approved:
โ
Renovation of two leaking lecture halls, with work already in progress.
โ
Provision of new whiteboards to improve classroom teaching.
โ
Financial support of N50,000 to assist the association in its activities.
๐ Inspection of 130 Boreholes Rehabilitation Project
As part of his oversight responsibilities, the Secretary conducted an inspection of the ongoing renovation and rehabilitation of 130 motorised and hand pump boreholes across the 13 wards of Zaria Local Government. The project, initiated by the Executive Chairman, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), is aimed at restoring non-functional water facilities to improve access to safe and potable water.
During the inspection, he assessed the quality and progress of work at the following locations:
- Garejin Baba Kaduna Motorised Borehole โ Tukur-Tukur Ward
- Kofar Doka โ Kwarbai B Ward
- Kwanar Shahada, Jushi โ Kwarbai A Ward
- Kofar Gidan Marigayi Malam Mainasara โ Gyallesu Ward
The inspection focused on ensuring compliance with approved engineering specifications and Bills of Quantities (BoQ), maintaining quality standards, promoting transparency and accountability, and guaranteeing the timely delivery of durable water infrastructure for the people of Zaria. aria Local Government remains steadfast in its commitment to improving the lives of its people through purposeful leadership and measurable impact.
10/07/2026
A yau da rana, na samu damar gudanar da zagayen duba ayyukan gyare-gyare da sake farfado da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da kuma na famfon hannu guda 130 da ake aiwatarwa a gundumomi 13 na Karamar Hukumar Zaria. Wannan aiki, wanda aka kaddamar karkashin jagorancin Shugaban ฦaramar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), na daga cikin manufar gyara rijiyoyin da s**a daina aiki domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga Alโummar Zaria.
Wannan zagayen duba ayyukan na daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan Kwamitin Kula da Aiwatar da Ayyukan, wanda Mataimakin Shugaban ฦaramar Hukumar, Gwani Malam Abdullahi Abba Zaria, ke jagoranta, domin tabbatar da ingantaccen sa ido, kiyaye ingancin aiki, da kuma tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.
Bayan da kamfanin da aka ba kwangilar ya fara aiki a wurare daban-daban cikin kwanakin baya, na ziyarci wasu daga cikin wuraren aikin a madadin ฦaramar Hukumar domin duba yadda aikin ke gudana da kuma tantance ingancinsa. Wuraren da na ziyarta sun hada da:
* Rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana ta Garejin Baba Kaduna a Tukur-Tukur;
* Rijiyar Kofar Doka a Kwarbai B;
* Rijiyar Kwanar Shahada da ke Jushi a Kwarbai A; da
* Rijiyar Kofar Gidan Margayi Malam Mainasara a Gyallesu.
Manufar wannan ziyarar ita ce tantance matakin da aikin ya kai, tabbatar da cewa ana bin kaโidojin aikin da aka amince da su tare da Jadawalin Ayyuka da Kayayyaki (Bill of Quantities โ BoQ), da kuma tabbatar da cewa aikin yana gudana bisa ingantattun kaโidoji.
Wannan gagarumin shiri da Shugaban ฦaramar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya samar yana daidai da manufofin gwamnatin Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Senator Uba Sani, wadanda s**a mayar da hankali wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa da kuma rage wa alโumma wahalhalun rayuwa.
Muna ci gaba da jajircewa wajen gudanar da irin wadannan ziyarce-ziyarcen duba ayyuka akai-akai har zuwa kammala wannan aiki, domin tabbatar da cikakken bin kaโida da aka amince da su, inganta gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da samar da ingantattun ayyukan more rayuwa masu dorewa da za su amfani alโummar Karamar Hukumar Zaria.
Hon. Shu'aibu Abdullahi Maicanter
Council Secretary
Zaria Local Government
10th July, 2026
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Zaria
