ATR hausa

ATR hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ATR hausa, Health/Beauty, Bala Ali, Accra.

18/11/2024

Jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso wanda ya faɗi hakan a Kano ranar Lahadi ya kuma zargi hukumomi a Najeriya da ƙoƙarin durƙusar da harkokin kasuwanci a arewacin ƙasar ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.

18/11/2024

Rikicin ƙabilanci ya sa an katse hanyoyin waya da intanet a jihar Manipur ta India

Ƙarin bayani - https://trib.al/fiGE566

Photos from ATR hausa's post 18/11/2024

An k**a likitan dake kula da "yan bîndīgâ idan s**a ji raúni ko basu da lafiya.

18/11/2024

Jami'an tsaro fiye da 43,000 ne ke samar da tsaro a zaɓen Ondo

Karin bayani - https://bbc.in/3O8YIBr

18/11/2024

Mutanen da aka ceto daga hannun ‘yan bindigar su 58 waɗanda s**a haɗa da mata 23 da maza 35 an k**a su ne a ƙaramar hukumar Ɗan-Musa ta jihar Katsina a hare-hare daban-daban.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/40NifP9

Photos from ATR hausa's post 17/11/2024

Dan takarar shugaban kasa a ghana kuma shine vice president a kasar ghana

Photos from ATR hausa's post 17/11/2024

An daura auren yar gidan kwankwaso amma babu wani Dan a. p . c ko guda daya

Photos from ATR hausa's post 11/11/2024

Sarki Charles da Yarima William da ƴan siyasa na cikin waɗanda s**a halarci bikin tunawa da mazan jiya da ake yi duk shekara a birnin Landan.

Dubban mazan jiya da fararen hula ne s**a karrama sojojin da s**a rasu a yaƙin duniya da sauran rigingimu.

11/11/2024

Hakan na zuwa ne bayan sabon koci Ruben Amorim ya yanke shawarar ƙin ci gaba da aiki da Van Nistelrooy a matsayin mataimakinsa.

Van Nistelrooy ya koma United ne a matsayin maitamakin koci a watan Yuli a kan kwantaragin shekara biyu inda ya samu nasarori uku da canjaras ɗaya a wasanni huɗu daya jagoranci kulob ɗin.

28/10/2024

Yayin da wasu jihohin s**a amince da biyan N70,000 ɗin, wasu kuma sun ci alwashin biyan sama da hakan.

28/10/2024

Ɗan wasan na Man City ya doke Vinicius da Bellingham na Real Madrid don lashe kyautar ta bana.

Rodri ya ɗauki gasar cin kofin nahiyar Turai da Sifaniya da kuma Gasar Firimiya da Man City.

Wannan ne karon farko da wani ɗan wasa daga gasar ta Ingila ya lashe kyautar tun 2008.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Accra?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Bala Ali
Accra