Elaaj Sirrin Tarbiyya

Elaaj Sirrin Tarbiyya

Share

Tarbiyyar yara • Hikimar aure • Gina iyali nagari. Shawarwari masu amfani domin kawo waraka da natsuwa a cikin gida.

05/07/2026

Jama'a kuyi nazarin hotunan da nasa a comment Section.
Me kuka fahimta akan su 🤔?

05/07/2026

Dan Allah duk wanda yaga wannan rubutun yayi sharing domin kuma zaku iya kasancewa sanadiyar gyaruwar wasu 🙏

Iyaye da yawa suna kuka a ɓoye ciki zukatan su saboda tarbiyyar yaran su 😢.

Menene mafi girman ƙalubalen da kuke fuskanta wajen tarbiyyar yaran ku? 🤔👇

Ku rubuta a comment Section, zan duba in bada shawara ga kowa In sha Allah.

04/07/2026

Idan kana da yaro mara jin magana, kuskure mafi girma da zakayi shi ne ya kasance baka karanta wannan post din ba.

Idan kuna son ilimin dabarun tarbiyya yara da mafita ga matsalolin ma'aurata kuyi following wannan page din na Elaaj Sirrin Tarbiyya domin kada ku rasa darussa masu amfani.

Zamu fara asalin program akan dabarun da zakayi idan kana da yaron ko wani dake baka ciwon kai game da matsaloli kamar haka

1. Rashin kunya
2. Rashin girmama iyaye
3. Rashin son karatu
4. Yawan amfani da TV ko waya
5. Rashin hakuri
6. Rashin tausayi
7. Rarya
8. Sata
9. Shaye-shaye
10. Zina da dangogin ta
11. Kungiyar banza
12. Rashin addini
13. Yawan faɗa
14. Rashin tsafta
15. Son duniya
16. Kwaikwayon mutanen banza
17. Rashin jin magana ko rashin zama kurum
18. Matsalolin shirka

Idan akwai wata matsala da kuke fama da ita wacce ban kawo ba sai ku sanya ta a comment section.

Please kuyi sharing domin ceton sauran al'umma.

27/06/2026

Wannan magen tafi da yawan wasu iyaye yin abinda ya dace. Yaren da magen zata gane kenan. Ƙoƙarin gyaran da tayi shine yayi min dadi. Amma a naka yaren, kada kai kayi duka. 😄

25/06/2026

Soon zan zo muku da Labarin yadda wasu iyaye s**ayi nasarar tarbiyantar da yaran su cikin hikimar aiki da TV da Waya
🧐

25/06/2026

PART 3: 🧐 Idan TV da wayar salula sun fara karɓar ragamar tarbiyyar yaran mu... shin akwai hanyar da za mu dawo da ita ba tare da faɗa, tsawa ko rikici ba?

A Part 1 mun fahimci cewa ba a haifi yaro da son TV ko waya ba. A hankali ake koya masa.

A Part 2 kuma mun ga yadda wasu abubuwan da muke yi domin nuna ƙauna zuwa ga yaran mu suke ba TV da wayar salula damar karɓar aikin tarbiyya daga hannun mu ba tare da mun sani ba.

Yanzu tambayar ita ce:

🤔 Shin akwai hanyar da za mu dawo da wannan ragama ba tare da fada, tsawa, ko rikici ba? Amsar ita ce: Eh.

Amma dole ne mu fahimci cewa ɓarnar da ya ɗauki shekaru tana faruwa, ba zata gyaru cikin dare ɗaya ba.

Ga wasu matakai masu muhimmanci:

1. Ku Fara Da Kanku Kafin Ku Fara Da Yara

Yaro yana kallon abin da kuke aikatawa fiye da abin da kuke faɗa.

Idan muna son ya rage amfani TV da waya, dole mu tambayi kanmu:

"Ni kaina yaya alakata take da TV da waya?"

Ba za mu iya hana abin da muke aikatawa kullum a gaban sa ba.

Tarbiyya tana farawa ne daga zama abin koyi.

2. Uba Da Uwa Su Zama Tsintsiya Madaurin ki Daya

Daya daga cikin manyan kura-kuran gidaje shi ne iyaye suna ba da saƙonni mabambanta.

Uba ya hana wani abu, Uwa ta amince.

Ko uwa ta hana, Wani a gida ya ƙyale.

Yaro zai rikice.

Dole ne iyaye su zauna su cimma matsaya ɗaya akan dokokin amfani da TV da waya.

3. Kada Ku Yi Gaggawar Kwace Waya

Wasu iyaye suna kuskuren kwace waya cikin fushi.

Yaro da ya saba da abu tsawon lokaci ba zai canza cikin minti ɗaya ba.

Maimakon haka, a rage lokaci a hankali.

A yau awa huɗu, Gobe awa uku.

A ci gaba har sai an samu daidaito. Gyara mai ɗorewa yana buƙatar hikima fiye da fushi.

4. Ku Samar Da Lokutan Da Gida Zai Dawo Gida

Akwai wasu lokuta da ya kamata a Kashe TV, waya kuma a aje ta a gefe.

Misali:

• Lokacin cin abinci.
• Lokacin hira da iyali.
• Kafin kwanciya barci.
• Lokacin ibada.

Waɗannan lokuta ne da ke gina kusanci tsakanin iyaye da yara.

5. Kada Ku Bar TV Ko Waya Su Yi Tarbiyya Su Kaɗai

Ku san abin da yaran ku suke kallo, Ku san wanda suke bi kuma Ku san irin saƙonnin da suke karɓa.

Lokaci zuwa lokaci ku zauna tare da su. Ku tattauna abin da s**a kalla.

Ku tambaye su:

"Me ka koya daga wannan?"

"Shin wannan ya dace da addininmu da tarbiyyarmu?"

Hakan yana koya musu tunani kafin kwaikwayo.

6. Ku Samar Da Madadi Mai Amfani

Yaro ba zai bar abin da yake so ba idan ba a ba shi wani abu mafi amfani ba.

Ku ƙara:

• Karatun Al-Qur'ani tare.
• Labarai masu tarbiyya.
• Wasanni.
• Ayyukan gida.
• Ziyartar dangi.
• Lokutan hira.

Sau da yawa yaro ba waya yake nema ba, Kulawa yake nema.

7. Kar Ku Manta Da Addu'a

A ƙarshe, zuciyar yaro tana hannun Allah.

Muna yin iya ƙoƙarin mu, amma shiriya daga Allah take.

Ku yawaita yi wa yaran ku addu'a.

Ku roƙi Allah Ya sanya su zama sanyin idaniya a gare ku.

Saƙon Ƙarshe

Iyaye masu daraja...

Wata rana waɗannan yara za su girma.

Ba za su tuna yawan bidiyon da s**a kalla ba.

Ba za su tuna yawan wasannin da s**a yi ba.

Amma za su tuna ko iyayen su sun zauna tare da su.

Za su tuna ko an saurare su.

Za su tuna ko an nuna musu ƙauna.

TV da wayar salula na iya jan hankalin yaro na ɗan lokaci.

Amma babu abin da zai maye gurbin ƙauna, lokaci, da tarbiyyar iyaye.

Allah Ya taimake mu wajen sauke amanar da Ya ɗora mana.

24/06/2026

Part 2: 🤔 Me zai faru idan na ce wasu daga cikin abubuwan da muke yi domin nuna ƙauna ga yaran mu ne ke sa TV da wayar salula s**a fara karɓar aikin tarbiyya daga hannun mu?

A Part 1 mun fahimci cewa ba a haihuwar yaro da son waya ko TV, a hankali yake koyon hakan.

Amma yanzu tambayar ita ce:

🤔 Me yake sa wasu yara su kasa rabuwa da waya, yayin da wasu kuma suke iya amfani da ita yadda ya dace?

Sau da yawa, amsar tana cikin wasu kura-kurai guda bakwai da muke yi a gida ba tare da mun sani ba. Ku biyo domin sanin wadannan kura-kuran.

1. Yin Amfani Da Waya Domin Dakatar Da Kuka Ko Hayaniyar Yaro. Wannan yana daga cikin kura-kuran da aka fi yawan yi.

* Yaro ya fara kuka, Sai a ba shi waya.

* Yaro ya fara hayaniya, Sai a kunna masa cartoon.

A wannan lokacin muna tunanin mun warware matsalar. Amma a zahiri muna koya wa ƙwaƙwalwar yaron cewa:

"Idan kana cikin damuwa ko rashin natsuwa, mafitar ka ita ce waya."

A hankali yaro yana fara dogaro da waya domin samun farin ciki ko natsuwa maimakon koyon yadda zai sarrafa yanayin zuciyar sa idan yana cikin damuwa.

2. Rashin Sanya Dokoki Da Iyaka Tun Da Wuri Akan Amfani da Waya

A wasu gidaje babu lokacin TV, Babu lokacin waya, Babu sanya iyaka akan abin da za a kalla.

Kullum lokacin kallon ne da zarar akwai wutar nepa ko kuma ba'a lura da me ake kallo.

Gaskiyar magana ita ce:

Yaro ba zai iya koyon sarrafa kansa ba idan babu wanda yake koya masa inda iyaka take.

Iyaye ne ke da alhakin tsara iyakokin da za su taimaka masa ya yi amfani da fasaha cikin hikima.

3. Iyaye Ma Waya ta tafi da Tunanin su

Yaro yana koyon abu ne ta gani kafin magana.

Idan kullum yaro ya ga:

* Uba yana kan waya.
* Uwa tana kan waya.
* Kowa yana kallon waya.

To saƙon da zuciyar sa ke karɓa shi ne:

"Waya ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwa."

Ba za mu iya koyar da abin da ba mu aikata ba. Yara suna kallon rayuwar mu fiye da yadda suke sauraron maganganun mu.

4. Barin Intanet Ta Koya Masa Abin Da Ba Mu Sani Ba. A da iyaye ne ke zaɓar abin da yara za su kalla.

Yau kuma a wasu lokuta algorithm ne yake zaɓa musu.

Misali a YouTube ko Facebook idan yaro ya shiga bidiyo na ɗaya, to ko wane video zai iya biyo wa na biyu (ko na kwarai ko na banza).

A hankali yana kallon abubuwan da iyayen sa ba su ma san suna wanzuwa ba.

Tambayar ita ce:

🤔 Idan ba mu san abin da yake kallo ba, ta yaya za mu san irin tunanin da ake gina masa?

5. Rashin Zama Da Yara

Wannan wani sirri ne da iyaye da yawa ba sa lura da shi.

Wasu lokuta matsalar ba waya ba ce. Matsalar ita ce babu wanda yake da lokaci domin yaro.

Yaro yana buƙatar:

A saurare shi, a yi hira da shi, a yi wasa da shi, a ji abin da yake damun sa.

Idan bai samu wannan kusanci daga iyaye ba, zai fara neman abin da zai cike wannan gurbi.

Sau da yawa kuma TV ko waya ce ke shiga wannan wurin.

6. Rashin Samar Da Madadin Waya

Wani lokaci muna son rage amfani da waya.

Amma babu wani abu da muka maye gurbinta da shi.

Babu karatu, Babu wasanni, Babu ayyukan gida, Babu wata sana'a ko wani abu da zai shagaltar da yaro.

Idan aka cire waya ba tare da madadi ba, zaiyi wahala a samu abinda ake so.

Domin an cire abin da yake sa shi nishaɗi, amma ba a ba shi wani madadin ba.

7. Barin Waya Ta Maye Gurbin Zama Da Iyali

Wannan yana daga cikin manyan kura-kuran da ba a cika lura da su ba.

A wasu gidaje: Uba yana kan waya, Uwa tana kan waya da saura yara, kowa yana kan waya.

Kowa yana gida amma babu wanda yake tare da wani saboda hankalin ya koma kan waya.

A hankali hira tana raguwa, Fahimtar juna tana raguwa da kuma dangantaka tana raguwa.

Alhali tarbiyya tana rayuwa ne a cikin kusanci, tattaunawa da zama tare.

A Part 3, za mu tattauna hanyoyi masu amfani da iyaye za su bi domin Karɓo Tarbiyyar Yaran Su Daga Hannun TV Da Wayar Salula

23/06/2026

PART 1: 🤔 Shin ku ne kuke tarbiyyar yaran ku ko kuma TV da wayar salula ne s**a karɓa wannan aiki daga hannun ku?

Ina fatar abin da za ku karanta a yanzu zai sa ku sake tunani kan yadda tarbiyyar yara ta koma hannun TV da Wayar Salula.

Da farko, bari na tambaye ku wata tambaya.

🤔 Idan aka cire TV da wayar salula daga hannun yaron ku na kwana ɗaya kacal... Shin me zai faru? Shin zai ci gaba da wasa cikin walwala?

Ko kuwa zai shiga damuwa, ya fara kuka, ya kasa natsuwa, ko ya rika yawo yana neman waya?

Idan haka ta faru, to ku sani... Matsalar ba waya ba ce. Matsalar ita ce abin da wayar ta fara yi wa zuciya da tunanin yaron.

A yau, iyaye da dama suna ganin TV ko waya a matsayin abin da zai sa yaro ya yi farin ciki.

Idan yaro yana kuka, a ba shi waya.

Idan yana hayaniya, a kunna masa TV.

Idan ana son a huta, a ba shi cartoon.

A hankali...

Ba tare da mun lura ba...

TV da waya suna fara ɗaukar wani matsayi da Allah Ya dora wa iyaye na matsayin gina tunani, dabi'a da halayen yaro.

Dole mu fahimci cewa Yaro ba ya zaɓar abin da zai gina tunanin sa... Na gaba da shi ne suke zaɓa masa.

Ga Kuma Wata Tambaya:
Shin TV da Wayar Salula Mummunan Abu Ne?

Amsar itace A'a, ya danganta da wanda ke aiki da ita.

Kamar misalin wuƙa ce. Da wuƙa ake yanka kayan abinci, da ita kuma ake iya cutar da mutum.

Saboda haka, ba waya ko TV ne matsalar ba.

Matsalar ita ce:

* abin da ake kallo
* tsawon lokacin da ake kallon sa
* shekarun yaron
* da kuma ko iyaye suna kula da abin da yake shiga zuciyar sa.

Masana ilimin halayyar ɗan Adam sun bayyana cewa farkon shekarun rayuwar yaro su ne lokacin da ƙwaƙwalwa take gina hanyoyin tunani cikin sauri.

Abin da yaro ke gani, ji, da maimaitawa yana taka rawa wajen yadda halayen sa da yadda yake fahimtar duniya za su bunƙasa.

Idan yawancin lokacin yaro ya koma ga kallon TV ko waya ba tare da kulawar manya ba, wannan na iya rage lokacin tattaunawa, wasa, motsa jiki, da sauran abubuwan da suke da muhimmanci ga ci gaban sa.

A Part 2, za mu duba kura-kurai da iyaye da yawa suke yi ba tare da sun sani ba, waɗanda suke sa TV da waya su zama "mai renon yara" maimakon iyaye.

Wannan shi ne ɓangaren da zai sa mutane da yawa su sake duba yadda suke amfani da fasaha a gidajen su. Kar ku bari a barku a baya.

17/06/2026

📢 MATSALOLI 18 GAME DA TARBIYYA

Alhamdulillah, kamar yadda muka sani muna kan gabatar da Program din mu na kawo mafita akan matsaloli goma (18) sha takwas game da tarbiyya.

Cikin ikon Allah a yanzu munyi rubutu akan matsaloli gudu biyu kamar haka:

1. Rashin addini
2. Rashin girmama iyaye

A yanzu kuma matsala ta 3 da za muyi magana akai itace:

3. Illar Yawan amfani da TV 📺 ko wayar salula 📱

Dan haka kafin mu cigaba inaso na sani:

1. Me kuka karu da shi a programs din mu na baya?

2. Wace shawara kuke da ita zuwa ga Elaaj Sirrin Tarbiyya domin inganta wannan aikin?

Please kowa yace wani abu 🙏.

16/06/2026
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Abuja
840212