Maso uwa ya so dandanta

Maso uwa ya so dandanta

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Maso uwa ya so dandanta, Health/Beauty, Abuja.

11/07/2025

Manxon Allah S.A.W Yace Wanda Yakeso Allah Da Manxonsa Su So Shi To Yayi Gsky Wurin Xance Yakuma Chika Amana Kuma Kada Ya Cuci Makocinsa.

27/01/2022

Duk Abinda Kukeyi Ku Bari Ku Karanta Domin Zai Amfane Ku...



Bismillahir-Rahmanir-Rahim.....

Lallai haquri wata irin kyauta ce da bawa ke samun kusanci ga Mahaliccinsa, sannan kuma abu ne mai matuqar wahala ga bawa, duk wanda Allah Mad'aukaki ya azurta da wannan kyuata to, ya samu alkhairin duniya da lahira, zai samu kusantar Mahaliccinsa da kuma taimakonsa.
Allah ya bayyana wa bayinsa cewa zai jarabce su da Ibtila'i daban-dabam, a al'amuransu na rayuwa a karan kansu da kuma dukiyoyinsu, babu mai rabo face wanda ya yi haquri cikin dukkan al'amuransa, sannan kuma ya cigaba da bautawa Allah cikin so da Qi.
Allah Ta'ala Yana cewa:
( ﻭﻟﻨﺒﻠﻮﻥﻢﻛﺑﺸﻲﺀﻣﻦﺍﻟﺨﻮﻑﻭﺍﻟﺠﻮﻉﻭﻧﻘﺺﻣﻦ ﺍﻟﺄﻣﻮﺍﻝ ﻭﺍﻟﺄﻧﻔﺲﻭﺍﻟﺜﻤﺮﺍﺕﻭﺑﺸﺮﺍﻟﺼﺎﺑﺮﻳﻦ)

Ma'ana: (Wallahi zamu jarabce ku da abubuwa na daga tsoro da yunwa, da tawayar dukiya, da (asarar) rayuka, da tsirrai (kayan abinci), kayi bushara ga masu haquri).
[Surat Al-Baqara : 155] Su wane ne masu haquri? Sai Allah Ta'ala Yace:

( ﺍﻟﺬﻳﻦﺇﺫﺍ ﺃﺻﺎﺑﺘﻬﻢﻣﺼﻴﺒﺔﻗﺎﻟﻮﺍ ﺇﻧﺎ ﻟﻠﻪﻭﺇﻧﺎ ﺇﻟﻴﻪﺭﺍﺟﻌﻮﻥ)

Ma'ana: (Sune wad'anda idan musiba ta same su sai s**e: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un (Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma).

Surat Al-Baqara:156. 'Dan'uwa idan wata musiba ta same ka kana furta wannan kalma? idan har kana furta ta da zarar wata musiba ta same ka take to, albishirinka da kasancewa cikin masu haquri.

06/04/2020

A kwai wasu makwabta guda biyu kuma abokan juna, daya talaka daya attajiri. To, ranan nan sai attajirin ya tashi yin kyauta sai ya nemi shawarar talakan cewa: “Malam Tanko, kyauta nake son yi wa wani talaka, shin ko na saya masa gida ya tashi daga gidan haya, ko na saya masa mota ya dinga neman abinci da ita, wanne kake ganin zai fi?” Sai talakan nan ya ce: “Alhaji, ka san talakawa ba a iya musu, kawai ka ba shi Naira dubu goma ya ja jari.” Jin haka shi kuma attajirin sai ya ce: “Da shawararka zan yi amfani.” Nan take ya zaro Naira dubu 10 ya ba shi, ya ce: “Daman kai ne zan yi wa kyautar ba wani ba!

06/04/2020

Wani saurayi ne yaje gaishe da sirikansa. Bayan ankaishi falo sun gaisa da sirikan nasa, da yan’uwan budurwar, sai aka kawo masa cin~cin da drinks.

Amma yaki sha akayi juyin duniya dashi dan yaci cin~cin din nan amma yaki ci. Sai iyayen yarinyar da yan uwanta s**a fita tsakar gida s**a barshi s**a ce

“kila kunyarsu yakeji shiyasa yaki ci” itama yarinyar tace bari inbaka guri kaci. Sai itama ta fita, sai ya dauki kwanon cin~cin din ya juye rabi a cikin hularshi, ya maida ita. Bayan ta dawo yace mata zai tafi tace kadai ki cin komai yace mata na koshi ne. Me zai faru, ya fito tsakar gida suna bankwana da iyayenta, kawai sai yaci karo da igiyar shanya, aikuwa hula ta fado sai ga cin~cin Shaaaaaaa!. yana zubowa sai gayenka ya karkace yace “ikon Allah yau kuma ruwan cin~cin akeyi.

HAHAHHAHHHAHHAHHA

06/04/2020

Wata tsohuwace tahau mashin din wani dan achaba zai kaita unguwa. Inda zai kaita naira arba’in ne a ke kaiwa tace yataimaka naira ashirin ne gareta yace tahau bakomi. Ke tsohuwa dakika hau mashin kikaji anata tsula wuta dake saita rasa inda zata rike dan karta fado kawai taji wasu marikai guda biyu daga kasa ashe siginoni ne tsohuwarnanko tarikesu gamgam da taji an kara shiga gargada garam!Garam! Saita kara makalkale siginonin nan daga karshe dai kamin akaita inda zata sauka duk ta kakkarya siginonin mashin dinnan sai da dan achabar nan yakaita bayanta bashi ashirin din saita mika mishi siginonin tace karbi yaro abubuwan rikewar taka basuda kwari!!! Dan achabarnan yayi shiru yana kallon tsohuwarnan. Yarasa abinda zaiyimata yahuce karshe yace to dan allah iya taimaka ki rike minsu muje wajan me mashin din karya ce dagangan na karyasu sai kiyi masa bayani. Tsohuwa tace bakomi da yadauketa yayita zuba gudu saida yayi tafiyarda ko naira dari da hamsin bazata maida tsohuwar nan ba sannan ya tsaya yaceta sauka bayan tasauka yakalleta yace yar banza kudin siginata yaja mashindinshi yatafi yabar tsohuwanan tsohuwa tafashe dakuka tace Allah ya isa, yaro kwarankwatsa naira goma taragemin.

29/03/2020

SIFFOFIN SAYYADA FADIMA

Nana Fadima ta kasance ma'abociyar kyau da kwarjini da kamewa Nana Aisha tace Nana Fadima ta fuskanto tana tafiya sai naga tafiyarta irin ta mahaifinta Annabi Muhammad saw An karbo daga Nana Aisha tace ban taba ganin mutum 💕💕💕💕💕Mai murna da magana irinta k**ar Fadima Nana Aisha tace Nana Fadima tayi k**a da Annabi saw a tafiyarta da zamanta da komai

29/03/2020

Dakai nake mai karatu, Allaah yajikanka
Ya gafartamaka kai da iyayenka
Yaa Allaah kahada fuskokinmu a Aljannatul firdauss

28/03/2020
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Abuja