Shafin Dr.Ibrahim Idris Jos
public
NI BANGA ANFANIN SUKAR CIRE RUBUTUN LARABCI DA WASU MALAMAI DA MUTANE SUKE TAYI BA,BA TARE DA DALILAN SHARI'A BA.
...Kune kuke wulakanta larabcin da masu karantar dashi a najeriya...
Dr.Ibrahim Idris Jos.
Galibin mutane sun kasa gane cewa mune ainihin masu wulakanta Addini da yaren larabcin sannan idan wani yayi sai muyita surutu mara anfani, amma kafin naci gaba da wannan jawabi inaso mai karatu ya amsa wadannan tambayoyi.
(1) Nawa kake biyan kudin makarantar boko na yaranka.
(2)Nawa kake biyan kudin islamiya na yaranka.
(3)Nawa kuke biyan albashin malaman Addini ko mai karantar da larabcin da bakwa so a goge a kudin Najeriya.
(4)Tsakaninka da Allah kana son Danka ya zama mai karantar da Larabci da kur'ani a tsawon rayuwarsa.
(5) Nawa kake sayan littafai na boko.
(6)Nawa kake sayan littafan larabci ko na musulunci.
(7) kuma shin sharadi ne sai anyi rubutun larabci a jikin kudin da musulmi da wanda ba musulmi ba zai kashe.
(8)Kuma kai wane gudunmawa ka bayar wurin tallafawa yaran larabcin.
(9) kuma musulmi nawa ne yanzu idan rikici ya hadasu suke zuwa kotun musulunci wanda kasar najeriya ta bada cikakken damar hakan,wanda yanzu an rage daukan Alkalai na shari'ar musulunci saboda musulmi mafi yawa basa zuwa.
Sannan a mahangar shari'a babu wani ra'ayi daga magabata ko wani nassi na Alkur'ani ko hadisi da akace sai anyi rubutun larabci a jikin kudi, Don wannan maslahar duniyace wanda ta shafi musulmi da wanda ba musulmi ba.
Kuma a tarihin kudin najeriya an sanya larabci ne a jikin kudin saboda a wancan lokaci mutanen arewacin najeriya basusan wani rubutu ba sai na ajami, amma tsakani da Allah yanzu mutum nawa ne s**a iya fahimta da rubuta ajami da dole sai an sanyashi a jikin kudi.
Abun bakin ciki har wasu malamai sun futo suna la'antar masu wannan ra'ayi.to ya kamata mu rinkayin komai akan doron ilmi na shari'a.
Kuma duk masu wannan s**a idan kaje gidansu basa koyar da iyalansu ajamin sai boko, kuma ma'anar rubutu a iya karantashi, idan mafi yawan mutanen najeriya kusan kashi 90 basa iya karanta ajami to menene anfanin sanyashi.
Allah ya datar damu akan daidai.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
D100t
Jos
