Abu Jandal Assalafiy
ﻣَﻦْ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﺮِﻑُ ﻟَﺎ ﺣَﺘَّﻰ ﻳُﻘَﺎﻝَ ﻟَﻪُ ﻟَﺎ ﻓَﻬُﻮَ ﺃَﺣْﻤَﻖُ
30/04/2025
A wannan ya'r rayuwar In har salama kake so a Rayuwaka da mutane, dole ka koyi banza da wasu, dole ka tilasta wa kanka manta wasu, wasu ka daina damuwa da maganarsu ko Cecekucensu, dole ka dena yi dansu ka kuma dena damuwa da yabo ko kushensu at all, dole ka hana kanka Kutsawa cikinsu, haka in su sun kutso ka naɗe harshenka karka faɗa musu sirrinka sanan ka toshe kunnenka Kar kaji Sirrinsu.
Ka dena yadda kai zurfi cikin yarda da mutane, Domin baka san hakikaninsu ba, Gwargwadon Zurfin dakai a yarda da wani, gwargwadon Zurfin Raɗaɗin da zakaji inyaci Amanarka.
Bahaushe yace; "Ɗan Adam me wuyar gane hali, Amma ba gaskiya bane! In da zuciya ɗaya kake mu'amala da kowa da sannu rahamar Allah zata yaye maka hakikanin mutane a lokacin da ka shiga Ƙunci ko buƙata, na lura da yawa kawai kau da kai ake, Toh kai ka dena, ka karɓi zahirin mutum in ya nuna maka fuskarsa ko dan ka gujewa wannan drama. Ka huta lafiya, In Allah ya yadda zaka mori zaƙin farin ciki koda duk duniya ke ihu a bakin kunnenka.
yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Idan Allah ya Soka da Alkairi,
Sai yasa ka Zamto mai Tuna sa a koda yaushe.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Lokoja Road Rigasa Kaduna
Kaduna South
