Arewa Youth Alliance
Developing of Arewa youth, such as Education, Work, Employment, Corruption, Peace.
02/11/2025
MUSULMI DA KIRISTOCIN AREWA....
Mu kula sannan muyi taka tsan tsan a wannan lokacin da Amurka tare da kasashen yamma s**a dasa mana tarko suke ta kokarin ganin mun faɗa cikkn tarkon domin su samu damar kwasar ganimar RARE EARTH da Allah ya h**e mana a yankin Arewa...
Arzikin RARE EARTH dake jibge a yankin Arewacin Najeriya na daga cikin abubuwan da Amurka ta sanyawa idanu....
RARE EARTH ELEMENTS DA AKE DASU A AREWA...
1 Tantalum (Ta) - Ana samunsa a Plateau, Nasarawa, Bauchi, da Kaduna States. Yana cikin rare earth metals masu muhimmanci.
2 Niobium (Nb) - Yana cikin columbite ore, ana samunsa a Plateau, Nasarawa, Kogi.
3 Lithium (Li) - An gano shi a jihaar Nasarawa Yana da tasiri sosai.
4 Beryllium (Be) - Ana samunsa a wasu yankuna na Plateau State.
5 Cesium (Cs) - Yana tattare da tantalite-columbite deposits a Nasarawa da Plateau.
6 Rubidium (Rb) - Ana samunsa tare da sauran rare earth elements a Plateau.
7 Thorium (Th) - Rare earth element ne mai aikin rediyo (radioactive), ana samunsa a Plateau da Bauchi States.
Cerium, Lanthanum, Neodymium - Waɗannan suna cikin Lanthanide series na rare earths, kuma an gano su a wasu wurare na Jos Plateau...
Idan muka kalli jihohin da ake sanun wadannan albarkatun na Rare Earths masu tasiri a duniya, zamu ga a jihohin tsakiyar Arewa inda kiristoci suke da yawa, hakan ne yasa Amurka ta fara wannan batun na halaka kiristoci domin ta haifar da rashin zaman lafiya sai tayi amfani da majalisar dinkin duniya wajen kafa dokokin da zasu basu damar shigowa Nigeria da sunan samar da zaman lafiya ...
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Ibrahim H Lawal, Muhammad K Ahmad, Baba Gana Ali Kolo, Kabeer Adam
16/04/2025
Ina fata mutane na gane bambanci tsakanin mawaki da maroki.
Yayin da wasu ke comparing Idris Abdulkareem da Rarara, ya kamata mu fahimci cewa akwai bambanci mai yawa tsakanin musical artist da maroki. Mawaki irin su Idris Abdulkareem na amfani da waka don fadakarwa, karfafa gwiwa, da tunkarar matsalolin al’umma. Wakokinsa suna da manufa da saƙo mai amfani ga ci gaban kasa.
Maroki kuma na amfani da waka don yabon shugabanni ko neman farin jini, yawanci ba tare da la’akari da gaskiya ko amfanin jama’a ba. Idan waka ta zama hanya ta neman lada ko kudi, to an kauce daga asalin manufar waka.
Mu rika tantance bambanci. Ba duk mai waka ne mawaki ba.
10/08/2024
Bello Habib Galadanci i.e. Dan Bello touches everyone, but Bashir El-Rufai warned him against criticizing the rulers.
Dan Bello seems to be raising public awareness, some of them suspect that he is bringing things that have no convincing evidence.
Although he did not mention anyone's name, some APC supporters started calling the security forces to arrest Dan Bello.
13/03/2024
Kasata Nigeria Kenan Yanzu Ba'aso Mutum Yafadi Gaskiya To Takawa Mufarka Yakata Mugane Yadda Shuawa Gabaninnmu Maciya Amanan Kasa Suke Ciutamu Akasan Nan: Misali Ga Nagarcencen Sanate Ahmed Ningi Yafadi Andakatar Shi:. Allah Yatona Asirin Maciya Amanan Kasa Amin
06/12/2023
Arewa Youth Alliance!! Muna Meka Ta'aziyamu Ga Yan Jahar Kaduna dakuma Gwamnatin Kaduna, Wanda Sukarigamu Gidan Gaskiya Allah Yajikansu Da Rahama Amin.......
16/08/2023
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar wasu sojojin ƙasar da helikwaftansu ya faɗo a cikin jihar Neja, a matsayin 'babbar asara mai tayar da hankali' ga Najeriya.
A ranar Litinin ne wasu sojojin ƙasar s**a mutu lokacin da jirgin da suke ciki ya faɗo a ƙauyen Chukuba kusa da ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja a tsakiyar Najeriya.
Tinubu ya ce sojojin na kan aikin hidimta wa ƙasarsu ne lokacin da s**a gamu da ajalinsu.
Tun farko rahotanni sun ce jirgin na aikin kwashe sojojin da s**a jikkata ne a fagen daga don kai su asibiti, lokacin da ya faɗo ƙasa, tare da kashe waɗanda ke cikinsa.
Wannan dai, shi ne karon farko da gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa a kan mutuwar sojojin ƙasar da kafofin yaɗa labarai s**a yi ta ba da rahotanni a jihar Neja.
Sanarwar Shugaba Tinubu dai, ta bayyana sojojin a matsayin "jajirtatu waɗanda ba su kula da hatsarin da za su shiga ba, a ƙoƙarin kare ƙasarsu da tabbatar da ganin al'ummominsu sun samu zaman lafiya".
"Yayin da muke alhinin mutuwarsu, za mu ci gaba da tuna gudunmawarsu, ba wai a matsayinsu na sojoji kawai ba, har ma da kasancewarsu gwaraza waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu domin samun zaman lafiya da tsaron ƙasarmu", in ji Tinubu.
Shugaban ƙasar ya ce "mun yaba da sadaukarwa da jajircewar da s**a yi wajen kare ƙasarmu".
"A madadin ƙasarmu, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan sojojin, da babban hafsan tsaron ƙasa, da babban hafsan sojin sama da babban hafsan sojin ƙasa, da babban hafsan sojin ruwa, da kuma illahirin rundunar sojin Najeriya", in ji shugaban ƙasar.
Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da wata sanarwa ranar Litinin tana tabbatar da faɗuwar jirgin helikwaftan ƙirar MI-171, wanda ta ce ya je ne don kwashe waɗanda s**a rasu ko kuma s**a jikkata.
A cewarta, jirgin ya faɗo ne da misalin ƙarfe 1 na rana bayan ya tashi daga Makarantar Firamaren Zungeru a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
11/08/2023
Shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Bola Ahmed Tinubu, ya ce akwai yiwuwar daukar kowane irin mataki ciki har da amfani da karfin soja a matsayin abu na karshe don warware halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.
09/08/2023
Shugaban Majalisar Datawan Najeriya, Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka, inda ya sanar da cewa majalisar ta tura wa mambobinta 'kuɗin more hutu'
A lokacin zaman majalisar na ƙarshe kafin tafiya hutu, Akpabio ya ce “Da zarar an rantsar da Sanata Umahi a matsayin minista, za mu sake tsara shugabancin majalisar.”
Sai ya ce “Domin more hutunmu, Akawun majalisa ya tura ɗan wani abu a asusun ajiyar kowannenmu.”
Bayan ya yi furucin ne ɗaya daga cikin ƴan majalisar ya matsa kusa da shi, don fargar da shi cewa ana nuna zaman nasu kai-tsaye ta talabijin.
Daga nan ne sai Akpabio ya yi saurin warware maganar tasa, inda ya ce “Na janye kalaman da na yi. Ina nufin shugaban majalisa ya tura maku addu'ar fatan shan hutu lafiya da kuma fatan yin tafiya lafiya a dawo lafiya.”
Babu dai tabbacin game da adadin abin da aka tura wa ƴan majalisar, musamman ma yadda albashinsu da kuma sauran kuɗaɗen alawus ɗinsu duk abubuwa ne da babu hakiƙanin bayani a kai.
09/08/2023
Ƙungiyar dattawan Arewa na neman Ecowas ta cire wa Nijar takunkumai
Ƙungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum (ACF), ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta cire takunkuman da ta saka wa Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji s**a yi.
A makon jiya ƙungiyar ta ACF ta soki batun aiki da ƙarfin soji da kungiyar Ecowas din ta ce za ta yi idan sauran matakai sun gagara.
Dattawan sun kuma yaba wa ƴan majalisar dokokin Najeriyar da s**a yi watsi da maganar aiki da karfin sojin.
Latsa hoton ƙasa don sauraren tattaunawar da sakataren ƙungiyar ACF, Mallam Murtala Aliyu
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Yan Majalisu Street Kawo Kaduna
Kaduna
9000108
