Rayuwar Arewa Ayau
YA ALLAH KAI MUKE ROKO DUK WANDA YA HANA KASAR MU CIGABA ALLAH KADAUKE MANA SHI KOWAYE✍️
10/07/2025
GA KIRA – ZUWA DUKKAN ‘YAN SANDA DA MASU RITAYA!
Kwanan nan … za ku daina barci cikin bakin ciki.
Kwanan nan … za ku daina karɓar cin zarafi a matsayin ƙaddara.
Kwanan nan … za ku farka da ƙarfi — a matsayin ‘yan sanda ba bayi ba.
1. Ku ne kuka ɗauki bindiga lokacin da ƙasa ke ci gaba da ci da wuta.
2. Ku ne aka yi wa alkawari — amma aka bar ku da fanshon tozarci.
3. Ku ne aka faɗa wa: “Zamu duba ku.” Amma har yau babu komai sai shiru da mutuwa cikin talauci.
Yanzu lokaci ya yi.
Ba don siyasa ba. Ba don jam’iyya ba. Ba don wani shugaba ba.
Sai don mutunci.
Sai don yaranku da ke jira a gida.
Sai don zaman lafiya da kuka sadaukar da rayuwar ku a kai.
✊🏽 Ku fito! Ku tsaya! Ku faɗa!
Mu haɗu a gaban majalisa — ba da bindiga ba, ba da fada ba — amma da GASKIYA.
Gaskiyar da ke da ƙarfi fiye da duk wata ƙarya da gwamnati ke gaya mana.
*Wannan ba zanga-zanga ba ce kawai —
Wannan isar da saƙo ne daga ran wadanda aka ci amanarsu.
Daga ran wadanda s**a fi kowa saka rayukansu a cikin hadari don a zauna lafiya.
Daga ran wadanda yanzu sun gane: idan ba mu tsaya ba, ba wanda zai tsaya mana.
📅 Ranar Zanga-Zanga: 21 Yuli, 2025
📍 Wurin Taro: Gaban Majalisar Tarayya, Abuja
Idan kaima mai saka uniform ne da aka yi watsi da kai… kai officer ne da aka mantar da kai… ko kai mai son ganin adalci ne — wannan kira naka ne.
✊🏽 Dan Bello | Muryar Wanda Aka Manta Da Shi
10/07/2025
80 SUN MUTU. AMMA ANA CEWA NIGERIYA LAFIYA KALAU?
A Plateau, an yi wa ‘yan sa-kai 70 kwantan bauna, an kashe su.
A Jihar Neja, 10 kuma sun mutu.
Duk cikin ’yan kwanaki — a dai-dai lokacin da Gwamnatin Tinubu ke cewa “Najeriya an samu tsaro.”
Muna jajantawa iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu.
Sun koma ga Allah suna kare al’ummarsu — wadda gwamnati ta ƙi karewa.
Amma mu tambayi kanmu:
Ina bayanan leƙen asiri?
Ina taimakon gaggawa?
Ina gwamnatin da su ke rasa rayukansu don karewa?
Duk da wannan masifa, muna cewa:
Babu janyewa daga aikin tsaron al’umma.
Domin idan mun ja da baya, su ne s**a yi nasara.
Saƙon ‘Yan Gaskiya zuwa Gwamnati:
Kada ku ƙidaya gawawwaki kawai.
KU ƘIDAYA GAZAWARKU.
Kuma ku gyara — ko ku ja gefe.
✊🏽 Ga jama’a: Ku kasance masu lura. Ku haɗu. Ku shirya. Kada ku dogara da alkawuran banza.
Karfin Jama’a - Sabuwar Duniya
01/07/2025
Bello Turji ya tabbatar da cewa Bashir Maniya ne ya kashe dan uwansa, Kachalla Yellow Danbokolo, amma yaransa sun fille kan Maniya - Karanta cikakken rahoton a sashen sharhi.
Hoto: (X)
A cikin unguwanninmu, makarantu da ƙauyuka — wani mummunan al-amari na faruwa:
Mutane sun fara sabawa da wahala.
Rufin asibiti na kwararo ruwa? “Da sauki, ai muna ma da asibitin.”
Yaro yana zaune ƙasa a aji? “Kai muma haka muka girma.”
Ɗan siyasa ya wawure biliyoyi? “To ai lokacinsa ne, duk haka su ke.”
Yanzu haka yin shiru ya tashi daga tsoro — ya zama al’adar mutanen Arewa.
Amma a sani:
Lokacin da ka yarda da zalunci a matsayin kaddara, to kana taimakawa ne wajen gina gidan da zalunci zai samu wajen zama.
1. Mu ‘Yan Gaskiya ba mu yarda da shiru ba.
2. Muna magana a lokacin da kowa yayi gum.
3. Muna daukar mataki a lokacin da kowa ya koma gefe ya na kallo.
4. Muna tashi tsaye a lokacin da ragowa s**a durƙusa.
🗣️ Dan Bello yace:
“Idan kowa yayi shiru, to zalunci zai samu gidan zama.”
✊🏾 Karfin Jama’a – Sabuwar Duniya
DOKOKIN HALAYEN ‘YAN GASKIYA
Idan ka na so a yi wannan gwagwarmaya da kai, to dole sai ka bi wadannan dokokin, kuma ka zama misali.
1. Amana (Riƙon Amana)
“Mu masu riƙon amana ne — amanar mutane, da ƙasa, da gaskiya.”
• Kada ka taɓa cin amanar jama’a.
• Abin da ka faɗa, sai ka tsaya a kai.
2. Kunya (Hankali da Ƙasƙantar da Kai)
“Ba girman kai muka zo da shi ba — amma gaskiya ne silar darajar mu, ba abun hannunmu ba.”
• Ka saka kaya masu tsafta, ka faɗi magana da kalamai na dattako, ka yi halayya na gari da ƙasƙantar da kai.
• Ka girmama kanka da wasu — ko da matsayinsu ya bambanta da naka.
3. Tsanaki (Tarbiyya da Kamun Kai)
“Dan Gaskiya ba ya halin banza — ko da ba a kallonsa.”
• Ka sarrafa harshenka da hikima, ka danne fushinka, ka guji girman kai.
• Kai sabon tauraron al-umma ne — ka kasance da halaye masu daraja.
4. Girmama Manyan da Ƙanƙan da Kai (Girmamawa)
“Gwagwarmaya ba ƙeta ba ce, kuma ba rashin kunya ba ne”
• Ka girmama manya, malamai, da abokan gwagwarmaya — ko da ra’ayinku ya banbanta.
5. Ƙaunar Al’umma
“Dan Gaskiya yana ƙaunar al’umma fiye da kansa.”
• Ka yi hidima, ka kare jama’a, ka ɗaga jama’a — ba tare da jiran yabo ba.
• Kada ka raina, ka cutar, ko ka muzanta masu rauni da wadanda ka fi.
6. Tausayi da Gafara
“Gwagwarmayar mu ba za ta wuce gona da iri ba. Gyara ta zo yi ne, ba ragargaza al-umma ba.”
• Ka gabatar da tsokaci da gyara a cikin hikima, ba da zagi ba ko cin fuska ko munanan kalamai ba. Babu cin mutunci, babu addu’a da fatan banza.
• Ka yafewa mutum idan ya dace, amma kada ka yafe zalunci.
7. Zama da Mutunci
“Ko a cikin fushi, mutuncinmu ba ya zubewa.”
• Kada fushi ya rushe halayenka.
• Ba kawai yaƙi kake da tsohon tsarin ba ne — kana gina sabo ne.
Karfin Jama’a - Sabuwar Duniya
05/06/2025
Ina tare da Dan Bello.
Wannan ba tambari ba ne kawai — alamar murya ce, alamar farkawa ce.
Karfin Jama’a – Sabuwar Duniya.
Idan kana tare damu, sanya wannan a profile ɗinka.
Shugaba Trump ya saka haramcin ne bayan harin da aka kai wa wasu 'yan Isra'ila a Amurka da ke gangami kan waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, inda Trump ɗin ya ce ya ce lamarin na da alaƙa da shigowar 'yan kasashen waje da ba a tantance su yadda ya kamata ba.
Never mind 🌬
Nigeria 🇳🇬 Sai dai gyaran Allah
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Makarfi Road By Shanono
Kaduna
@
