Limamin G-R-A

Limamin G-R-A

Share

Barka da zuwa offficial page ɗin ƴaƴan masu kuɗi na (Yusuf Musa Bin Baz) Addini cikin hikima. Kalamai masu taɓa zuciya. Ilimi. Faɗakarwa. Nishaɗi. Danna Follow ☀️

01/02/2024

ALƘAWĀ'IDU AL-ARBA'U DARASI NA {1}

Alhamdulillah Yauma muna cikin wata risala daga cikin rasā'il na Sheikh Muhammad bin Abdulwahab me suna Alƙawā'idu Al-arba'u. nan ma dai wasu irin ƙawā'id ne guda huɗu da Malam ya amfanar da mu su a ƙoƙarinsa na amfanar da al'ummar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.

kai tsaye zamu shiga cikin risālar domin jin wace irin tsaraba Malam ya kawo mana! Allah kaɗai nake roƙo yai wa malam rahama yasa ya huta yai mana albarka baki ɗaya.

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah me rahama me sadar da rahamar ga bayinsa

أَسْأَلُ اللهَ الْكَرِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَتَوَلاكَ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ.

Ina roƙon Allah me karamci Ubangijin al'arshi me girma ya jibinci lamarin ka duniya da lahira.

وَأَنْ يَجْعَلَكَ مُبَارَكًا أَيْنَمَا كُنْتَ، وَأَنْ يَجْعَلَكَ مِمَّنْ إِذَا أُعْطِيَ شَكَرَ، وَإِذَا ابْتُلِيَ صَبَرَ، وَإِذَا أذَنبَ اسْتَغْفَرَ. فَإِنَّ هَؤُلاءِ الثَّلاثُ عُنْوَانُ السَّعَادَةِ.

Sannan: ya saka ka me albarka a duk inda kake, ya kuma saka ka cikin waɗanda in Allah ya basu za su gode masa, idan kuma ya jarabce su za su yi haƙuri, idan sun yi zunubi za su nemi gafarar Ubangiji, saboda waɗannan nau'ikan mutanen uku: sune Address na dacewa.
---------------
{To kaga wannan sai a aƙidar Ahalussunnah: kai da kake karatun kai akewa wannan addu'ar! Allah yai maka kaza..... yai maka kaza}......
______________
اعْلَمْ أَرْشَدَكَ اللهُ لِطَاعَتِهِ: أَنَّ الْحَنِيفِيَّةَ مِلَّةُ إِبْرَاهِيمَ: أَنْ تَعْبُدَ اللهَ، وَحْدَهُ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ ﴾ [الذاريات: 56].

Sheikh Yace: Ka sani Allah yai maka rahama da yi masa biyayya: cewa “Alhanafiyya” miƙaƙƙiyar hanya ita ce hanyar Annabi Ibrahim: ka bautawa Allah, shi kaɗai kana me tsarkake addini gare shi, k**ar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa

{ وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ } [الذاريات:56]. Bamu Halicci Mutum da Aljanu ba sai dan su bauta mana.
___________
AL'IMĀMU ASSA'ADIY RAHAMATULLAHI ALAIHI CIKIN TAFSIRINSA TAISÍRI KARÍMIRRAHMĀN FÍ TAFSIRI KALĀMIL-MANNĀN YACE!

( وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ )

الذاريات (56)

هذه الغاية، التي خلق الله الجن والإنس لها، وبعث جميع الرسل يدعون إليها، وهي عبادته، المتضمنة لمعرفته ومحبته، والإنابة إليه والإقبال عليه، والإعراض عما سواه، وذلك يتضمن معرفة الله تعالى، فإن تمام العبادة، متوقف على المعرفة بالله، بل كلما ازداد العبد معرفة لربه، كانت عبادته أكمل، فهذا الذي خلق الله المكلفين لأجله، فما خلقهم لحاجة منه إليهم.

Wannan itace maƙura, wadda akanta aka Halicci mutum da aljan, aka kuma aiko da manzanni su yi kira gare ta, ita ce bauta, wadda ta ƙunshi sanin Allah da son sa, da komawa gare shi! da fuskantarsa, da kuma kauda kai daga wanda ba shi ba, hakan kuma ya ƙunshi sanin Allah madaukakin sarki, domin ita cikar bauta, ta tsayu ne wajan sanin Allah.

Kai bari ma duk lokacin da bawa ya kara sanin ubangijinsa, zaka samu bautarsa tafi cika da k**ala, to akan wannan ne Allah ya halicci Mutum da aljan, bawai ya halicce su ne dan wata buƙatarsa gare su ba.

فَإِذَا عَرَفْتَ أَنَّ اللهَ خَلَقَكَ لِعِبَادَتِهِ؛ فَاعْلَمْ أَنَّ الْعِبَادَةَ لا تُسَمَّى عِبَادَةً إِلا مَعَ التَّوْحِيدِ، كَمَا أَنَّ الصَّلاةَ لا تُسَمَّى صَلاةً إِلا مَعَ الطَّهَارَةِ، فَإِذَا دَخَلَ الشِّرْكُ فِي الْعِبَادَةِ فَسَدَتْ، كَالْحَدَثِ إِذَا دَخَلَ فِي الطَّهَاَرِة،

Malam Yace: idan kasan cewa Allah maɗaukakin sarki ya halicce ka ne dan ka bauta masa, to ka sani cewa ita fa bauta ba'a kiran ta da bauta sai da Tauhidi, k**ar yadda Sallah bata yi wu wa sai da tsarki, idan shirka ta shiga bauta to bautar ta ɓaci, k**ar hadasi ne idan ya shiga tsarki.

فَإِذَا عَرَفْتَ أَنَّ الشِّرْكَ إِذَا خَالَطَ الْعِبَادَةِ أَفْسَدَهَا، وَأَحْبَطَ الْعَمَلَ، وَصَاَر صَاحِبُهُ، مِنَ الْخَالِدِينَ فِي النَّارِ. عَرَفْتَ أَنَّ أَهَمَّ مَا عَلَيْكَ مَعْرِفَةُ ذَلِكَ لَعَلَّ اللهَ أَنْ يُخَلِّصَكَ مِنْ هَذِهِ الشَّبَكَةِ،

Yace: idan kasan cewa in shirka ta cakuɗu da bauta ɓata bautar take, ta kuma lalata aiki, ma'abocin ta kuma ya kasance cikin waɗanda zasu dauwama cikin wuta {in be tuba ba} To ka sani mafi girman abinda yake kan ka shine sanin wannan lamarin ta iya yi wu wa Allah maɗaukakin sarki ya tsare ka daga wannan sakā.
_________
{Anan Sheikh yana son nusantar da kai ne cewa ka san abunda yake wajibi gare ka ko Allah ya kare ka daga faɗawa shirka. Wannan dalilin yasa kaga yana bada Misalai.

ka sani cewa idan shirka ta shiga bauta: bautar tana ɓaci k**ar yadda in hadasi ya shiga alwala alwalar ta samu Matsala}.

Yusuf Musa Bin Baz

1-feb-2024.

13/01/2024

Maimakon doguwar hirar da kuke da budurwa a waya ku saka wani darasi na addini mana.

13/01/2024

Kana matashi amma baka da alaƙa da karatun addini! Sai budurwarka tai ma tambayar ka tsaya kana zare ido. Dan Allah Samari muje tsoron Allah wannan rayuwar da muka sa ta gaba zata ƙare bamu cimma wani abu ba in bamu lura ba.

11/01/2024

Mutum ne kun san shi yana sai dai kayan miya ya dena ya dawo kayan ƙamshi da marmari kanunfari/Masoro/Goruba/magarya/adu'a/kwakwa/DSS, kai harda kayan ƙamshi na shayi. Yanzu kuma ya dawo sai da maganin Gargajiya, Kuma ku ɗin dai kune kuke ce masa Doctor, kuke tura matanku da ƴaƴan ku ya baku magani harda Magunguna na sirrin {OZA ROOM}. Tambayar anan shine: Yaushe ya rikiɗe ya zama Doctor! kodai ita sana'ar da ka ake shigar ta!

11/12/2023

ALJAMI'U LI'IBADATILLAHI WAHDAHU {1}

Halƙa ta Farko “1”

Wannan risāla me suna a sama itama risala ce daga cikin rasā'il na Allama Fadeelatu Sheikh Muhammad bin Abdulwahab rahamatullahi alaihi. Alhamdulillahi gata dai ƙarama a yawan shafuka! Amma kāfí ce wajan isar da saƙo kuma shāmila ce saboda ɗimbin ilimomin da ta ɗēbo! Allah kaɗai nake roƙo ya amfanar da mu Musamman mu ƙananun ɗalibai da abinda ke cikin ta.

الرسالة السابعة الأصل الجامع لعبادة الله وحده

بسم الله الرحمن الرحيم

فإن قيل: فما الجامع لعبادة الله وحده؟ قلت: طاعته بامتثال أوامره واجتناب نواهيه.

Malam Yace idan aka ce mene ya tattaro bautar Allah madaukakin sarki ? Ni Muhammad bin Abdulwahab sai nace yi masa biyayya ta hanyar aikata umarninsa da nisantar abinda yai hani ne.
______
{{Wannan shine: saboda haka ba komai bane cikin bautar Allah sai umartuwa da umarninsa da hanuwa da hanawarsa! Duk abinda Allah ya umarce ka da shi to haka Allah yake so ayi! a matsayin ka na bawa baka da zaɓi akai.}}

{Shi yasa ka kalli sunan risālar! الجامع لعبادة الله وحده Ma'ana abinda ya tattaro bautar Allah maɗaukakin sarki.}

فإن قيل: فما أنواع العبادة التي لا تصلح إلا لله تالى؟ قلت: من أنواعها: الدعاء والاستعانة ١ والاستغاثة، وذبح القربان، والنذر، والخوف، والرجاء، والتوكل، والإنابة، والمحبة، والخشية، والرغبة والرهبة، والتأله، والركوع، والسجود، والخشوع، والتذلل، والتعظيم الذي هو من خصائص الإلهية.

Malam Yace idan aka ce mene Nau'ikan bauta wadda ba yadda za'ayi bauta ta yi wu sai da su? Sai nace na daga ciki akwai Addu'a!

{Wanda ita dama addu'a Allah har cewa yai duk wanda yai girman kai wajan barin kiran Ubangijinsa sai ya shirgar da shi wutar jahannama yana ƙasƙantacce! duba suratu Ghāfir}.

Malam Yaci gaba da cewa Akwai Neman taimakon Allah {Wannan yana Magana ne cikin abinda ba wanda yake da iko kansa sai Allah} Akwai neman ce! {shima cikin abinda ba wanda yake da ikonsa sai Allah! Misali k**ar neman ceton da za'ai ranar alƙiyama! kaga bame iko kan haka sai Allah}.
_______
Da yanka { shima dan samun kusanci ga Allah} da bakance! {Shine kaiwa Allah alƙawarin in kaza ya same ka za kai kaza ko za kai azumi ko wani abu da yai k**a da haka! duka wannan nau'i ne na bauta}.

Da jin tsoron Allah maɗaukakin sarki! {Ma'ana irin tsoron da babu wanda za'ai wa shi sai Allah} da fatan haɗuwa da Allah da fatan abinda ke gurinsa na ni'ima, da tawakkali ga Allah {shine ka miƙa lamarinka gaba ɗaya gare shi shine zai juya komai}.

Da komawa gare shi {Saboda sama da ƙasa babu me yi maka sai shi ɗin} da yin soyayya dan shi! {dan Anan ake ƙulla Alwalā'u walbarā} da jin tsoronsa, da tsoron abinda ke gurin sa na azaba da fatan abunda ke gurinsa na aljanna, da kaɗai ta shi da bauta, da yin ruku'u dan shi, da yin sujjada dan shi, da nutsuwa dan shi, da ƙasƙantar da kai ga Allah {ma'ana ka nuna kai ba kowa bane} da girmama shi wanda hakan yana daga cikin ƙeɓantattun abubuwa na bautar Allah.

ودليل الدعاء قوله تعالى: {وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلا تَدْعُو مَعَ اللَّهِ أَحَداً} ٢

Dalili kan addu'a faɗin Allah maɗaukakin sarki inda yace “Dukkan guraben bauta na Allah ne kada ku kira wani tare da Allah” Suratu Jinni.
_______
Kamar yadda AL'IMĀMUL BAGĀWIY Ya kawo cikin Tafsirinsa yace gaɓɓan da ake nufi anan sune Tafukan hannu guda biyu! guiwa guda biyu! yatsu biyu na ƙarshen ƙafa! Sai kuma Goshi da Hanci a haɗe! idan ka lissafa bakwai kenan.

وقوله تعالى: {لَهُ دَعْوَةُ الْحَقِّ وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ لا يَسْتَجِيبُونَ لَهُمْ بِشَيْءٍ} ٣ إلى قوله: {وَمَا دُعَاءُ الْكَافِرِينَ إِلاَّ فِي ضَلالٍ} ٤.

Malam Yace Da kuma faɗin Allah maɗaukakin sarki inda Yace “ Gare shi kira na gaskiya yake! wanda suke kira ba shi ba ba zai iya amsa musu kiran nasu da komai ba” har inda Allah yake cewa “Addu'ar kafirai bata kasance ba face ɓata” Suratu Ra'ad.
_________
AL'IMÃMUL BAGAWIY YACE {لَهُ دَعْوَةُ الْحَقِّ ana nufin Tauhidi k**ar yadda ya kawo daga Aliyu bin Abi ɗalib. Abdullahi ɗan Abbas kuma yace ana nufin kalma لا إله إلا الله. Wasu malaman s**a ce ana nufin tsarkake bauta ga Allah maɗaukakin sarki. {A takaice dai in ka duba duka fassarorin suna shiga ciki}.

Har yaje ƙarshen ayar inda Yace «وما دعاء الكافرين» عبادتهم الأصنام أو حقيقة الدعاء «إلا في ضلال» ضياع Ma'ana bautar da kafirai sukewa Gumaka/ko kiran da suke musu kira na haƙiƙa! To hakan be kasance ba face ɓata/Hasara k**ar yadda yazo Cikin Tafsirul Jalalāini.
_________
ودليل الاستعانة قوله تعالى {إياك نعبد وإياك نستعين}

Malam Yace Dalili kan neman taimako {cikin abinda ba wanda yake da iko kansa sai Allah} ga faɗin Allah maɗaukakin sarki nan “Gare ka muke bauta Gare ka muke neman Taimako”

Jalãluddín Almuhallā da Jalāluddín Assuyúɗí s**a ce cikin TAFSIRUL JALĀLAÍNI Ma'ana muna keɓance ka da bauta da Tauhidi da mak**antan haka! Muna kuma neman taimakon ka cikin bautar da waninta. {Kaga kenan sauran lamurran duniya zasu shiga ciki wajan neman taimakon nasa}.
________
Saboda haka Ni me rubutu nake cewa wannan Gaɓa ce me matuƙar muhimmanci mu kula da ita ba'a neman taimakon kowa wajan abinda bashi da iko sai Allah! Saboda aikata hakan shirka ne wa lamarin Allah! Allah ya shiryar da Mu.

Yusuf Musa Bin Baz

11-12-2023.

26/11/2023

A matsayin ka na ɗan uwa ahlussunnah me da'awa be k**ata ace kana da wata matsala da ɗan uwanka Ahlussunah amma ka kasa faɗa masa dan a samu fahimta da dai-dai to ba.

26/11/2023

Samun yardar mutane abu ne da ba za ka taɓa samu ba! Haka tsarin mutane yake.

26/11/2023

Hasanul basari yace bamu taɓa ganin Faƙihin mutum yana jayayya ba.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kumbotso Road
Kano