TARIHI DA AL'ADU

TARIHI DA AL'ADU

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from TARIHI DA AL'ADU, Health/Beauty, Rijiyar lemo, Kano.

25/05/2022

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar sarakuna.

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a ƙarshen karni na 19 Scramble for Africa, ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani Addis Ababa a 1886.

Mahaifin Taytu ShI ne Ras Betul Haile Maryam, yana cikin dangin Semien da ke mulki da s**a yi iƙirarin zama zuriyar Daular Annabi Sulemanu AS ta hannun Sarkin sarakuna Susenyos I. Kawun Taytu shi ne shahararren jarumin kabilar Amhara, Wube Haile Maryam, wanda shi ne hakimin lardi sannan kuma mai ci kuma mai mulkin larduna; Tsegede, Weilkat tigray da kuma Eritrea. Mahaifiyar Taytu, Yewibdar, ta fito daga wani babban jigo a yankin Gonder.

Ilimi

Babu wasu bayanai da s**a nuna cewa Sarauniya Taytu ta halarci makaranta; duk da haka, an koya mata karatu da rubutu cikin harshen Amharic da Ge'ez. Wannan abu ne mai wuyar gaske, ganin cewa a cikin wannan lokaci da wuya mata su sami ilimi. An yi imanin cewa an koyar da ita diflomasiyya, siyasa da tattalin arziki.

Ana daukar Taytu Betul a matsayin daya daga cikin shahararrun shugabannin Habasha, mata ce ga sarkin sarakuna Menelik II. Ta taka rawa wajen murkushe 'yan mulkin mallaka na Italiya ita ce kuma ta kafa birnin Addis Ababa.

Wace ce Taytu Betul?

Taytu Betul wata mace ce 'yar kasar Habasha mai kima da daraja wadda tare da mijinta sarkin sarakuna Menelik II s**a yi mulkin Habasha daga 1889 zuwa 1913. Ana tuna ta saboda jajircewarta da adawa da kuma nasarar da ta samu a kan sojojin Turawan mulkin mallaka na Italiya da kuma karfin ikonta a kotun sarki. Ita ce ta zabi yankin da a yau ya zama babban birnin Habasha ta kuma sanya masa suna Addis Ababa.

Wace ce Taytu Betul kafin ta zama Sarauniyar sarakuna?

An haifi Taytu Betul cikin iyalan sarauta masu karfin tasiri wadanda ke da dangantaka da daular Sulaimaniya wajen shekarar 1840 ko 1851 a cewar wasu majiyoyi a Debre Tabor wanda ba shi da nisa da kogin T

25/05/2022

Ruwan Teku Ya Koro Kunkuru Mai Kai Biyu Waje.

An sami wani karamin kunkuru mai kai biyu a Tsibirin Hatteras da ke gabar teku a Jihar Karolina ta Arewa (North Carolina) a kasar Amurka.

An gano kunkurun mai kai biyu ne a bakin teku a karo na biyu a ’yan makonnin da s**a gabata.

Shafin Facebook na Cape Hatteras National Seashore ya wallafa bidiyon kunkurun bayan gano wannan karamar halitta a gabar tekun North Carolina.

Wani masanin ilimin halittu, Will Thompson ya ce irin wadannan halittu suna da yawa fiye da yadda ake zato.

Thompson ya ce, “Gaba daya kananan halittu da ake kyankyashewa kamar kunkuru a Cape Hatteras National Seashore da duniya baki daya, ba sabon abu ba ne a gan su da kai biyu.”

“Muna ganin nakasassu a halittu a kowace shekara a zababbun wuraren da suke gabar teku, a yayin da ake aikin hakar rami.”

Ya tabbatar da cewa, halittar kunkurun ba wani abin mamaki ba ne.

Thompson ya ce, kyankyasar da alama an yi ta ce cikin koshin lafiya kuma an fitar da kwan ba tare da wata matsala ba a cikin tekun.

Wannan shi ne karo na biyu cikin ’yan makonni da aka ga kunkuru mai kai biyu a Amurka.

An kuma gano wani abu a Edisto Beach State Park a tsibirin Edisto a Kudancin Karolina.

Jami’ar wurin shakatawa na Jihar Karolina ta Kudu a cikin wata sanarwa a Facebook ta bayyana yadda jami’an da suke aikin tono kasa kwana uku zuwa biyar s**a yi nasarar gano kunkurun.

Za su iya kiyasta kyankyasar da s**a fito daga bawonsu da wadanda s**a mutu don tantance yuwuwar habakar rayuwarsu a masaukinsu kamar yadda ya kamata.

Yayin da suke haka daya daga cikin masaukan kunkurun, sun samu wadanda aka kyankyashe guda uku a cewar sanarwar, amma dayansu ya fi fice.

“Yayin da suke tantancewa a ranar Laraba da ta gabata, masu aikin sa-kai sun samu.

kyankyasar kunkuru masu rai a tekun uku, har yanzu suna cikin dakin bincike, amma daya da aka kyankyashe ya fito waje saboda yana da kai biyu!

An taba gano wasu da aka kyankyashe masu kai biyu a Jihar Karolina ta Kudu a shekarun da s

25/05/2022

TARIHIN WINSTON CHURCHILL.

A tarihin Winston Churchill ya kasance wani babban dan siyasa ne, kuma jagora wanda ya zama Firaministan Ingila shekarar 1940 zuwa 1945, da kuma 1951 zuwa 1955.

A tarihi Winston Churchill ya kasance dan Jam’iyyar siyasa ta Liberal daga bisani kuma Conservative wanda a karkashin su ne yaci zabe a matsayin dan Majalisar Dokokin Ingila inda ya wakilci gundumomi daban-daban wanda s**a hada da Oldham, Manchester North West, Dundee, Epping, da kuma Woodford, duk a tsakanin shekarun1900 to 1964.

A harkar siyasar duniya kuma, a tarihin Winston Churchill yayi suna a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin duniya a zamanin sa. Mafi shaharar abin da yayi a duniya shine na kasancewa daya daga cikin jagororin yaki wanda s**a yaki Hit-ler a lokacin Yakin Duniya na biyu.

Farkon Rayuwa Tarihin Winston Churchill.

An haifi Winston Churchill a ranar 30 ga watan Nuwamba, 1874, a Blenheim dake yankin Oxfordshire, a kasar Ingila. Mahaifin sa sunan sa Lord Randolph Churchill wanda ya kasance basarake. Yayin da mahaifiyar sa kuma sunan ta Jennie Churchill wadda asalin iyayen ta suke yan asalin Amurka.

A tarihin Winston Churchill yayi karatu a Makarantun St. Georges, Brunswick, da kuma Harrow. Daga bisani kuma ya shiga Makarantar Sojoji ta yayan Sarauta wadda a turance ake kira da Royal Military Academy, dake Sandhurst daga shekarar 1893 zuwa 1894.

Aikin Soja a Tarihin Winston Churchill.

Winston Churchill ya fara aikin soja a matsayin second lieutenant a Gungun Sojojin Ingila dake Aldershot a shekarar 1895. Haka kuma a shekarar ya fara fita filin yaki lokacin da aka tura shi domin taya sojojin Spain rigima a yayin Yakin neman Yancin kasar Cuba.

A shekarar 1896, an tura Churchill zuwa kasar India domin yin wasu ayyukan soja. Sannan kuma daga baya yayi aiki a matsayin dan jaridar soja mai kawo labari a yakin da sojojin Ingila s**a yi daban-daban a kasashen India, Sudan, da kuma Afirka ta Kudu.

Harkar Siyasa da Mulki.

A tarihin Winston Churchill tun ya

13/04/2022

YAKE-YAKEN SARKIN KANO DABO.

Yake-Yaken Sarkin Kano Dabo sun kasance wasu yake-yake ya kaddamar domin tabbatar mulkin sa da kuma kasaitar Kasar Kano. Sarkin Kano Dabo ko Ibrahim Dabo ya kasance Sarkin Kano wanda wasu suke ganin cewa yafi kowane Sarki tasiri a jerin Sarakunan Kano guda hamsin da bakwai. Dalilai da yawa kuwa sune s**a hadu s**a bawa Sarkin Kano Ibrahim Dabo matsayi na musamman a jerin Sarakunan Kano. Babba ko kuma daya daga cikin dalilan kuwa shine kasancewar Sarkin Kano Dabo kasaitaccen mayaki kuma wanda ya gwabza yake-yake musamman domin tabbatar da Masarautar Kano a matsayin Masarauta daya sakamakon tawaye da ya fuskanta a farkon hawan sa gadon Sarautar Kano.

Don haka ne Yake-yaken Sarkin Kano Dabo s**a kasance wasu muhimman abubuwa da s**a faru a tarihin Kasar Kano wanda suke bukatar a dinga tunawa da su.

Yan Tawaye a Farkon Sarautar Sa.

Bayan da Sarkin Kano Sulaimanu ya rasu a shekarar 1819, sai masu bukatar zama sarakunan Kano s**a bayyana tare da nuna bukatar su. Wasu daga cikin masu son sarautar Kano a lokacin sun hada da wanda sun kasance shugabannin kaddamar da Jihadi a Kano. Misali, shugaban Kabilar Fulani Dambazawa wato Malam Inusa Dabon Dambazau da kuma Malam Mandikko shugaban Kabilar Fulani Jobawa duk sun nemi a basu Sarautar Kano amma ance Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya tsallake su tare da nada Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano saboda ilmin addini da shi Dabon yake da shi.

Sai dai ance nadin da Sarkin Musulmi ya yi wa Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano ya bata wa wadannan manya da sauran wasu a gefe rai. Saboda haka wasu daga ciki s**a fara yin kokarin tawaye. Don haka ne a kokarin sa na dinki barakar dake kokarin bayyana, Sarkin Kano Dabo ya aikawa da dukkanin dagatan Kasar Kano tare da makwabtan Sarakuna wasika yana sanar da su kasantuwar a matsayin Sarkin Kano. Sai dai ance a lokacin da takardar Sarkin Kano Ibrahim Dabo ta ishe daya daga cikin manyan dagatan Kasar Kano wato Sarkin Fulanin Arewacin Kano kuma Sarkin Fulanin D

Photos from TARIHI DA AL'ADU's post 13/04/2022

YADDA MUKAYI DA NZEOGWU BAYAN YA KASHE SARDAUNA INJI MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR GUMI. ALLAH YA GAFARTA MASA.

K**ar karfe hudu na asuba ranar juma'a aka bugo mun waya bayan na dauka sai naji ministan ilimi be na Arewa Alhaji Isa Kaita. Ya cemun sojoji fa sun yi Juyin mulki, har an kai ma gidan Sardauna hari kamar yadda yace mun duk manyan jami'an gwamnati sun buya. Yace mun ya yi magana da Hassan Katsina, amma Hassan dai a lokacin yace mai babu abun da zai iyayi. Hassan yace mai a wannan lokacinma yana ganawane da bujirarrun sojojin. Isa Kaita, yace mun ya kamata ni inje gidan Sardauna in ganema idanuna abunda ke faruwa.

Bayan na kintsa nayi sallar subahi, na kuma K**a hanya na nufi gidan Sardauna, naje na ishe gidan anyi kaca-kaca, da shi alamu kuma sunnuna anyi amfani da manyan makamai wurin lalata gidan. Har lokacin da na Isa gidan hayaki Ne a turnuke. Sai wasu tsirarun sojoji ne a tsaye da bindigogi a hannunsu, ko ina tsit. Haka na wucesu na kutsa kaina cikin gidan, ina shiga naci Karo da gawar firimiya a kwance a filin da ake aje motoci na gidan.

Nan danan nace a dauki gawar a kaita gidan, Sarkin Musulmi, dage unguwar Sarki, Sardauna, da shi da uwargidansa Hafsat duk An kashesu.

Bayan mun gama kintsashi, rana Kuma ta fara dagowa nine na Sallaci duka gawarwakin. Ina sane Kuma da cewa anyi babban rashi Kuma dai nan kurkusa abune mawuyace a samu kamarsa.

Akan hanyata ta dawowa gida daga wurin jana'izar Sadauna, na wuce gun-gun mutane sun taru sunata alhinin abunda ya faru. Bayan na samu natsuwa abubuwa sun koma kamar yadda suke ranar komawa aiki na shirya kamar kullun na tafi wurin aikina. Ina cikin ofishina da safe sai ga motar sojoji, Cike da sojoji, ta shigo harabar wurin aikina. Wasu daga cikin sojojin s**a sauko a mota s**a tambayi inda ofishina yake. Bayan sun shigo ofishina s**ai mun gaisuwa irinta ta girmamawa, s**a ce an turo su Ne Su tafi dani maigidansu Nzeogwu, yana son ganina.

Kuma zan shiga motarsu ne tilas su tafi dani amma zan iyasa wani cikin m

13/04/2022

TARIHIN ZUWAN LARABAWA DA TURAWA KANO.

A shekara ta 1453 miladiyya, a zamanin sarkin kano Yakubu dan Abdullahi Barja, sarkin kano na goma sha shidda a mulkin kanawa, wadansu larabawa mutanen kasar Gadamus masu fatauci s**a zo daga Tarabulus (Libya), s**a sauka a kano. Sune larabawan farko da s**a fara zuwa kano.

Da saukar wadannan fatake, sai s**aje wurin sarkin kano Mallam yakubu, a jujin ‘yan Labu, Watw unguwa Kano, a lokacin ba’a gina gidan sarautar kano na yanzu ba, s**a ce da sarki a cikin harshen larabci su fatake ne, suna so su zauna a kano domin suyi ciniki.

A wannan lokaci kuwa, limamin kano Mallam Muhammadu Hashimu ne yake fassarawa sarkin kano abinda wadannan fataken larabawa ke fada a matsayin tafinta. Daga nan sai sarkin kano yakubu yayi farin ciki kwarai da gaske, sannan yace da shamakin kano ya kaisu sararin nan dake yamma da unguwar Garke watau Dandali, suyi gidaje su zauna acan.

Sabili da wadannan mutane suna da jar fata, sai mutanen kano s**a sa musu suna Turawa. Don haka koda larabawan s**a zauna a wannan wuri, sai mutane s**a sanyawa wurin Dandalin Turawa. Dalilin sunan dandalin turawa kenan yau kusan shekaru 553 kenan.

Tun daga wancan lokaci ne larabawa s**a cigaba da zuwa kano fatauci. K**ar misali akwai Yamalawa mutanen Yamen, da larabawan Tunis duk sun je kano, amma kowadanne akwai nau’in kasuwancinsu.

Su Larabawan Libya mafi yawan abinda suke siyarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan kamshi da kayan zaki.

Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga lokacin da aka soma samar da kasuwanci a Kano. A zamanin da, mutanen kano sunfi riko da noma fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar da sana’o’i na gargajiya misalin rini, jima, kira da sak’a. Wadannan su s**a haifar da ainihin kasuwanci, domin mutum zaiyi abu ya siyar ga jama’a.

Koda yake, a wancan lokacin, ba’a fara amfani da kudi ba a kano, ana yin cinikin furfure ne, watu ban gishiri in baka manda.

Daga baya ne lokacin da fatake larabawa ko Asbinawa da Agalawa s**a zo kano,

15/03/2022

Rose Chibambo, Ladi Kwali da Tawhida Ben Cheikh su ne kawai matan Afirka uku da s**a taba shiga cikin takardun kudi.

Sarauniya Elizabeth II ita ce macen da ta fi fice a duniya, a cewar bayanan.
Sarauniyar ta bayyana a kan takardun kudi daban-daban a wasu kasashe 19.

Wani bincike da kamfanin bayar da lamuni na Sweden Advisa yayi nazari akan takardun banki na duniya 1,006 na yanzu kuma ya gano cewa kashi 15% ne kawai ke nuna hotunan mata. A halin da ake ciki, maza ne ke da wakilcin da ake gani kusan kashi 88 cikin 100 na kudaden duniya, wanda hakan ya haura zuwa kashi 91 cikin 100 idan ba za mu hada da wadanda ke dauke da sarakunan Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta biyu ba.

Wani karin haske game da binciken ya gano cewa babu wani kudi mafi karfi a duniya a shekarar 2022, wanda kowannen su ke yawo a kasashen Afirka, da ya nuna mace.

Domin bikin watan mata na duniya, Business Insider Africa ta duba kundin takardun kudi na kasa da kasa, inda ya gano cewa kasashe 3 ne kawai daga cikin kasashen Afirka 54 s**a Buga mace a kan Takardar kudi matan Su ne Rose Lomathinda Chibambo ta Malawi, Ladi Kwali ta Najeriya, da Tawhida Ben Cheikh ta Tunisia.

Rose Lomathinda Chibambo fitacciyar 'yar siyasa ce a yankin Nyasaland na Birtaniya a shekarun da s**a kai ga samun 'yancin kai a matsayin kasar Malawi a 1964 da kuma nan da nan bayan haka. Ta shirya matan Malawi a yakin siyasa da suke yi da Birtaniya a matsayin wani karfi na siyasa da za a yi la'akari da shi wajen neman 'yancin kai. Ana kiran wani t**i a cikin birnin Mzuzu don girmama Chibambo, kuma har zuwa ranar 1 ga Janairu, 2012, ta bayyana akan takardar kudin Malawi 200 Kwacha.

Nigeria - Ladi Kwali (Naira 20)

Dokta Hadiza Ladi Kwali ta kasance daya daga cikin fitattun maginan tukwane a Najeriya, wadda ta shahara a duniya wajen gudanar da wasu nau’ikan tukwane na gargajiya a Afirka da na yammacin Turai. A bisa la’akari da nasarorin da ta samu da kuma kwazon da ta yi, gwamnatin Najeriya ta karrama kudin Naira 20 da hotonta,

12/03/2022

SOME HAUSA NATIVE NAMES AND THEIR MEANING:

▪️Delu, Kande: A girl born after the birth of many boys.
▪️Tanko: A boy born after the birth of many girls.
▪️Talle, Audi: A child born after the death of the father.
▪️Yelwa, Wadatau, Arzika, Goshi: A child born in the time of abundance wealth or blessings.
▪️Barau: A living child of a woman who has lost many kids at birth before him.
▪️Rani: A child born during dry season.
▪️Sodangi: A child who's shown loved by all family members after his birth.
▪️Bahago: A child who's noticed to be left handed.
▪️Qauna: Beloved.
▪️Magaji, Magajiya: Successor.
▪️Chindo: A child born with more than normal fingers or toes.
▪️Maidawa, Dawi: A male child born in a season of harvested plentiful bundles of Guinea-corn.
▪️Gero, Maigero: A male child who was born in a season of harvested abundant bondles of Millet stalks.
▪️Shekarau, Shekara: A baby who makes a year in his mothers womb.
▪️Aruwa, Ruwa, Anaruwa, Damuna,
Makau, Marka: A child who was born during rainning season or when it was raining cat and dog in a community.
▪️Hankuri: A baby noticed to be extremely patient.
▪️Nomau, Nanoma, Tanoma: A child who was born during farming season.
▪️Sarki: One who has King name.
▪️Maifari: A male child who was born during drought season.
▪️Yarima: Prince.
▪️Nagona: A child who was born at farm.
▪️Nasallah, Tasallah: A child born during Eid celebrations.
▪️Baƙo, Baƙuwa: A child who was born after the mother arrives as a visitor.
▪️Hana: A child who was born while the family is mourning the death of a family member.
▪️Bawa, Bayi: A child who was brought-up by another woman, that was not his mother.
▪️Tinau: A child who was born after his mother took long time before she concieve another pregnancy.
▪️Maikasuwa: A child who was born at market or on market day.
▪️Dangali: An only child in a family.
▪️Maikudi: A rich one or wealthy.
▪️Madugu, Madiga: A child who was in the process of travelling.
▪️Tagwaye, Tagwai, Biyu, Yan Biyu: A name given to one Hal

14/01/2022

Tarihin Rikicin Falasdinawa da Yahudawa.

Matsalar abin da ya shafi Yahudawa da dangantakarsu da gabas ta tsakiya dai wata aba ce mai dadadden tarihin gaske, domin kuwa tunkafin haihuwar Annabi Musa Alaihissalam, wato tun zamanin Annabi Ibrahim Alaihissalam , shi wanda yai rayuwa a wannan yanki da yanzu ake kira Falasdinu da Iraki da Siriya da Misra.

To Annabi Ibrahim Alaihissalam yana da “Yaya guda biyu sune Annabi Ishaq da Annabi Ismail.Su Yahudawa suna danganta kansu a matsayin “yayan Annabi Ishaq. Sukuma Falasdinawa suna danganta kansu a matsayin yayan Annabi Ismail. Wannan ya nuna kenan Yahudawa ma suna da tushe a wannan wuri kamar yadda Larabawa ma suke da shi. Saboda haka gabaki dayan su sun rayu a wannan wuri , rayuwa mai yawan gaske kafin mulkin mallaka daban-daban da s**a ringa faruwa, wadanda s**a zama sanadiyyar fatattakar wannan nan, wannan can, a kai ta dai fuskantar matsaloli. Saida takai a Duniya Yahudawa basu da matsuguni amma saboda tarihi yai halinsa , s**a shiga kasashe daban-daban na Duniya s**a zauna a ciki.

A lokacin yakin Duniya na daya ,kasar Israila ta shiga ayari ita da Birtaniya da Faransa da kuma kawayen su wadanda s**a yaki daular Usmaniyya wadda take da hedikwata a Turkiyya, wadda kuma take da karfin fada aji a kasashen Musulmi. Sakamakon haka sai wannan yanki gaba ki daya ya zamanto karkashin mulkin mallakar Birtaniya da Faransa da kawayen su. Yahudawa kuma a duk inda suke saboda su tsiraru ne sai s**a shiga kulle-kulle na yanda zasu kwaci kansu , su kuma mallaki kasar turawa ta koma hannun su. Wannan ya sa s**a fito da tsari guda biyu. Na farko dai shine tsarin shiga cikin siyasar kasashen Turawa. Na biyu tsarin kutsawa cikin tattalin arzikin su. Wadannan dalilai ya sa akan dole Turawan s**a tafi da su.

Daya daga cikin alkawarin da akai musu saboda gudun muwar da s**a bayar har aka ci nasara , shine za a sama musu guri da za su kafa daular su . Da farko an yi musu alkawari za a basu guri a Uganda tunda dai Birtaniya ce take mulkin

12/01/2022
12/01/2022

"Ni kuma tafsirina ba na duba takarda saboda haka Annabi yake yi, sannan haka ma manyan bayin Allah s**a yi.

"Idan mutane s**a tambaye ni me ya sa ba na rike takarda a tafsirina, ? sai na tambaye su cewa kuna rike kur'ani idan kuna karanta Suratul Ikhlas a sallah?

"Na san kur'ani saboda haka ba sai na rike shi ba idan zan yi tafisiri," in ji Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

09/01/2022

Tarihin Nufawa A Najeriya.

Yadda Kabalir Nupe S**a Fara Rayuwa Bayan Isowarsu A Kasar Najeriya Da Kasashen Su.

Nupe wasu kabilu ne da suke rayuwa a tsakiyar najeria kamar su Niger state, Kwara state, Kogi state da Abuja, Hausawa suna kiransu da sunan Dan Kabilar Banufe Yan Kabilar Nufawa wato wato masu yawa kenan.

Makotansu Gwarawa suna kiran da suna Anupeyi, kuma Yarbawa suna kiran su da suna Tapa (Takpa).

Akwai wasu yaruruka sama da biyar wadda suke karkashin Nupawa wato Kakanda, Dibo, Kupa, Gana Gana, Bassa Nge (Nupe Tako) wato su napawa na kudu masu zama a kasar Kogi.
Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa ‘Tarihi da Al’adun Mutanen Najeriya’ cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe da Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bida, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.

Amma binciken Dr. Sidi Tiwugi Shehi ya kawo ra’ayoyin masana da yawa saɓani da wannan. Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Ukba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabawa tare da zama a ƙasar Nupe.

Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara. Shi kuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa sune kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu) Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna ‘Social Symbiosis and Tribal Organisation.

Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da s**a gabata. Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda s**a jima a ƙasar Nufe har ma s**a kafa birnin Kutigi.

Rukuni na uku sune Benu, waɗanda s**a yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Rijiyar Lemo
Kano