Kabara online Hausa
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kabara online Hausa, Health/Beauty, 131 soran dinki, Kano.
21/06/2023
YANZU-YANZU: Gwamnan Kano Ya Mayar Da Rimin Gado Muƙamin Shugaban Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado muƙamin shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce mayar da shi kujerar ya samo asali ne don yin biyayya da hukuncin kotu.
Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado daga muƙaminsa bayan bisa ɓoyayyun lamura.
21/06/2023
YANZÚ - YANZÚ: Ań Báiwa Malamiń Addiniń Musuluncí Daké Jihar Kanó Shéikh Abubakar Lawań Triumph Awanni 24 Ya Fitó Da Bidiyoń Da Yacé Ƴań Tijjaniyya Súna Baútar Ƙabari Kó Ƙabarurrukań Waliyyansu Kó Ƙabarin Shehu Tijjani RTÁ Kó Ńa Shehu Ibarhím RTA) Kó Kúma Su Maká Shí A kótu.
Mé zakú cé?
19/06/2023
DUBUN WANI BARAWON MASHIN TA CIKA!!
Wannan shine Barawon Mashin din Babban Limamin CENTRAL MOSQUE na garin TORO LGA a Jihar Bauchi.
A labarin da mu kasa mu samu, yazo yayi satar sati uku da s**a wuce baa k**a shi ba.
Cikin iko na Allah sai ya dawo yau da niyyar daukan mashin din LADANIN Masallacin.
A daidai wannan lokaci YANZU HAKA YANA GENERAL HOSPITAL TORO bayan ya Sha Dan Karen doka.
Allah ya nuna masa karshen wadannan sacesace da muke fama dasu, Allah ya kara tona mana Asirin su.
📷 Mujahid Saleh Saad - Dan maliki
18/06/2023
Ranar Lahadi 18 ga watan Yuni, daidai da 29 ga watan Zul-Qadah ita ce ranar neman jinjirin watan Dhul-Hijjah 1444". Sakon – Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya NSCIA, Alhaji Sa’ad Abubakar ya umurci Musulmi da su duba jinjirin watan Dhul-Hijja na shekarar 1444 bayan hijira daga ranar Lahadi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Al’amuran Addini na Majalisar Sarkin Musulmi ta Sakkwato Farfesa Sambo Junaidu, ya ce Zul-Hijja shi ne na 12 kuma watan karshe a kalandar Musulunci da Musulmi ke gudanar da aikin Hajji na shekara-shekara da bukukuwan babban Sallah. - bikin el-Kabir.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana sanar da musulmi cewa ranar Lahadi 18 ga watan Yuni, daidai da 29 ga watan Zul-Qadah ita ce ranar neman jinjirin watan Dhul-Hijjah 1444".
Ya kara da cewa an bukaci al’ummar musulmi da su fara neman jinjirin wata a ranar Lahadi kuma su kai rahoto ga Hakimin gundumar ko kauye mafi kusa don tuntubar Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta yi addu’ar Allah ya taimaki dukkan musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini lafiya,
18/06/2023
YANZU-YANZU: 'Yan Sandan Jihar Zamfara Sun Dawo Da Motocin Da S**a Ɗebe Daga Gidan Tsohon Gwamna Jihar Zamfara Dr. Bello Matawalle
Daga Muhammad Kwairi Waziri
17/06/2023
WATÁ SABÚWA: Bankńn NIRSAL ya gargadi waɗanda s**a karɓi bashi daga bankin su biya kó kuma ya farauto kuɗin da ya basu da ƙarfin tuwo daga bankunan da suke ajiya ta hanyar amfani da fasahar GSI.
Mé zakú cé?
17/06/2023
An samu hatsaniya yayin da Kwamitin Rusau na Gwamnatin Kano ya je unguwar Salanta don rushe gine-ginen da ke filin Kwalejin Fasaha ta Kano a wannan dare.
Ƙarin bayani yana tafe.
16/06/2023
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ƙaddamar da motar lantarki da Mista Jelani Aliyu, babban daraktan / babban jami’in hukumar kula da kera motoci ta kasa (NADDC) ya gabatar a gidan gwamnati dake Abuja.
16/06/2023
Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Attajiri Alhaji Aliko Dangote a Fadar Shugaban Kasa dake Villa.
📷: Buhari Sallau
16/06/2023
Kotun kolin Saudiyya ta bukaci a duba jinjirin watan Dhul Hijah da yammacin ranar Lahadi 29 ga watan Dhul Qadah 1444 H, daidai da 18 ga watan Yunin 2023.
- KABARA ONLINE HAUSA
16/06/2023
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau ta umurci rundunar ‘yan sandan Najeriya da wasu mutane hudu da ke da hannu wajen kwace wasu motoci da wasu kayayyaki masu daraja daga gidajen tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da su dawo da su cikin sa’o’i 48.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
131 Soran Dinki
Kano
