Al-ƙibular Arewa News
Hukumar Gudanar Wa Ta Wanan Shafin Mai Suna Guguwar Labarai Muna Godiya Ga Masu Bibiyar Mu A Koda Yaushe
27/08/2025
A gaɓar da ake saran Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai bayyana matsayarsa game da zaɓen 2027 a babban taron NWC na jam’iyyar NNPP da za a gudanar ranar Alhamis, ina da ra’ayi mai muhimmanci:
Ya dace Jagora Sen. Rabiu Musa Kwankwaso ya ci gaba da tafiya tare da Malam Aminu Ringim, duk irin sabon salo ko tafiya da za a ɗauka.
Idan har ya tabbata cewa jam’iyyar APC ce za a koma, to yakamata a tabbatar da mafita mai kyau ga Malam Ringim, kasancewar jiharsa ta Jigawa tana ƙarƙashin mulkin jam’iyyar APC.
Malam Aminu Ringim ya kasance ginshiƙi mai ƙarfi na tafiyar Kwankwasiyya a Jigawa. Tun daga lokacin da ya shiga tafiyar, an ga ƙaruwar ƙarfi, daɗaɗɗen gindin zama da karɓuwa a fadin jihar.
A yayin shirye-shiryen zaɓen 2027, idan har Malam Aminu Ringim bai samu takarar gwamnan jihar Jigawa ba a jam’iyyar APC, muna fatan ya kasance Ɗan takarar Deputy Governor, domin hakan zai ƙarfafa haɗin kan Kwankwasiyya a Jigawa tare da tabbatar da tasirin jagorancinsa.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
11/08/2025
Cikin Hotuna:
Jagoran jam’iyyar NNPP na jihar Jigawa, Malam Aminu Ringim, ya jagoranci tawagar manyan shugabannin jam’iyyar NNPP na jihar, inda s**a kai wa Jagoran Kwankwasiyya na ƙasa ziyara a gidansa da ke Miller Road.
A cikin jawabinsa, Malam Aminu Ringim ya yi tsokaci kan irin matsalolin da jihar Jigawa ta shiga a karkashin mulkin jam’iyyar APC daga koma bayan tattalin arziki, rashin ayyukan raya ƙasa, har zuwa taɓarɓarewar jin daɗin jama’a.
Ya kuma jaddada cewa, tafiyar Kwankwasiyya na samun gagarumar nasara a faɗin jihar Jigawa da ma Nijeriya baki ɗaya, inda ya tabbatar da cewa jama’a sun fara gane bambancin shugabanci na gaskiya da na ƙarya.
Kwankwasiyya ta zo da tsari na gaskiya, da adalci. Mutanen Jigawa sun fahimci cewa lokaci ya yi da za su rungumi tafiyar ci gaba,” in ji shi.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
06/08/2025
Idan Dr. Goodluck Jonathan ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2027, tasirin Peter Obi na iya fuskantar babbar barazana a siyasar Najeriya.
A zaɓen 2023, Peter Obi ya samu goyon baya mai ƙarfi daga Kiristoci, musamman daga yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, sakamakon rashin jin daɗi da s**a yi da tsarin Muslim-Muslim ticket na APC. Obi ya zama tamkar wakili da ya bayyana damuwar addini da kuma ƙalubalen da ‘yan yankin s**a fuskanta.
Amma idan tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan wanda shima Kiristi ne daga Kudu – ya dawo takara a PDP, akwai yiwuwar goyon bayan da Obi ya samu zai koma gare shi. Wannan ya dogara da tarihin Jonathan, nagartarsa a shugabanci, da karɓuwarsa a tsakanin masu ra’ayin damokradiyya da 'yan ƙasa da dama.
Abin da zai ƙara janyo hankalin jama’a shi ne idan jam’iyyar PDP ta cimma nasarar haɗa Dr. Goodluck Jonathan da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin shugaba da mataimaki. Wannan tsari zai ba PDP fa’ida ta Kudu da Arewa, da kuma haɗin kai na addini da ƙabila abu mai matuƙar tasiri a siyasar Najeriya.
Wannan haɗin gwiwa zai iya janyo karɓuwa ba kawai a Kudu ba, har ma da jahohin Arewa da dama, musamman ma a tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da kuma waɗanda s**a damu da cewar zaɓe na gaba ya kawo haɗin kai da daidaito a kasa.
Idan hakan ta tabbata, Peter Obi zai fuskanci matsanancin ƙalubale wajen riƙe matsayinsa a matsayin zaɓin "alternative" na gaba. Tasirinsa zai fuskanci ƙalubale daga manyan yan siyasa da s**a fi shi kwarewa da tarihi a kasa.
06/08/2025
Abubuwa 9 Da Kwamitin Binciken Belin Danwawu Ya Gano:
1. Tsayawa Beli Da Kanshi: Kwamishinan ne da kansa ya nemi zama mai tsaya wa wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
2. Rantsuwar Matsayi: Ya bayar da rantsuwa a kotu cewa kwamishina ne mai ci kuma zai bi duk sharuɗɗan beli.
3. Sanin Sharuɗɗan Beli: Ya fahimci cewa sai kwamishina mai ci ne kaɗai zai iya tsayawa mutum beli a ƙarƙashin waɗannan sharuɗɗa.
4. Rashin Bincike Da Tattaunawa: Bai yi cikakken bincike ko tantancewa kafin yanke shawarar tsayawa wanda ake zargi ba.
5. Sanin Nau’in Laifi: Ya san cewar laifin da ake tuhuma da shi na safarar miyagun ƙwayoyi ne.
6. Saɓawa Manufofin Gwamnati: Ya san da irin matsayar gwamnatin Kano kan yaƙi da safarar ƙwayoyi da laifuka a tsakanin matasa.
7. Babu Alaƙa Da Wanda Ake Zargi: Babu wata shaida da ke nuna yana da alaƙa da wanda ake zargi kafin batun belin.
8. Karɓar Kuɗin Rashawa: Babu wata alamar cewa an ba shi kuɗi ko wani abu don ya tsaya wa wanda ake zargi.
9. Biyan Kuɗin Beli: Bai bayar da kuɗin beli da ake zargi da su (₦5,000,000) ba — wannan iƙirari daga wanda ake zargi ne kawai.
Kamar yadda Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan yada labaran gwaman Kano ya wallafa.
03/08/2025
DAGA FADAR GWAMNATIN JIHAR KANO
TARO NA MUSAMMAN AKAN AL’ADUN HAUSA DA FULANI
A yau, daga cikin ginshiƙan raya al’umma da kare martabar tarihi, Fadar Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da taro na musamman domin tattaunawa da zurfafa fahimta kan al’adun Hausa da Fulani ginshiƙai biyu da s**a gina darajar Arewa tun ƙarni da ƙarni.
Wannan taro ya haɗa manyan masana tarihi, shugabanni na gargajiya, da matasa masu kishin al’adu, domin tabbatar da cewa abin alfahari na kakanni zai ci gaba da haskawa a zukatan al’ummar mu.
An tattauna kan hanyoyin kare harshe, kiɗa, tufafi, adabin baka, da sauran al’adu, tare da shirin sabunta su ta yadda za su dace da zamani amma ba tare da rasa asalin su ba.
Fadar Gwamnati ta tabbatar da cewa wannan taro ba kawai tunawa da tarihi ba ne, illa ma wani alkawari ne na kare martabar Hausa da Fulani har zuwa ƙarni masu zuwa.
29/07/2025
Wanda ya riƙe Kwankwaso a matsayin jagora ya huta takaici domin Yanzu gaskiya tana bayyana a fili.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya faɗi gaskiya game da yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke nunawa Arewa ɓangaranci a cikin ayyukan raya kasa da gwamnatin sa ke gabatarwa.
Daga cikin manyan hujjoji:
Ginin titin Lagos-Calabar da ya kai ₦15 Triliyan babu wani kaso na Babban Aiki daga Arewacin Najeriya!
Ayyukan gwamnatin tarayya suna zurfafa, a kudu yayin da Arewacin Najeriya ke cigaba da tagayyara!
Bayan wannan magana ta Kwankwaso ta karade kasa, Shugaba Tinubu ya umarci manyan ministoci da jami’an gwamnati su yi gaggawar bayyana a Kaduna domin kare kansu!
Amma idan babu laifi me yasa, ake ta kare kai?
Kwankwaso bayyi wannan magana dan kawo rikici Yana kiran Ayi adalci ne ga kowanne ɓangare.
Wanda ya saurari Kwankwaso da zuciya ɗaya, ya tsira daga ruɗu.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
20/07/2025
Ziyarar Mataimakiyar Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Duniya (UN), Hajiya Amina J. Mohammed, Zuwa Wajen Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Mataimakiyar Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Duniya (UN), Hajiya Amina J. Mohammed, wadda ta kai ziyarar aiki zuwa Kano.
Ziyarar na cikin yunƙurin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Ɗinkin Duniya wajen aiwatar da manyan manufofin cigaban duniya (SDGs), musamman a fannonin ilimi, ƙarfafa matasa da mata, da sauya fasalin muhalli.
Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiya bisa wannan ziyara tare da yabawa irin tallafi da goyon bayan da ƙungiyar ke baiwa jihar Kano. Ya kuma bayyana aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiki tukuru don cimma burin ci gaban al’umma da daidaito.
A nata jawabin, Hajiya Amina J. Mohammed ta bayyana jin daɗinta da kokarin da gwamnatin Kano ke yi wajen inganta rayuwar jama'a, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyi domin kawo ci gaba mai ɗorewa.
Ziyarar ta haɗa da ganawa da manyan jami’an gwamnati, wakilan ƙungiyoyin haɗin gwiwa, da wakilan al’umma, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
17/07/2025
SANARWA GA MANEMA LABARAI
17 Ga Yuli, 2025
Shugaba Tinubu Zai Kawo Ziyarar Jaje Kano Gobe.
Jihar Kano na shirin karɓar Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR a ranar Juma’a, 18 ga Yuli, 2025, domin yin ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da al’ummar jihar, tare da iyalan marigayi dattijo, attajiri kuma mai jinkai, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Alhamis.
Ziyarar na zuwa ne bayan rasuwar mashahurin ɗan kasuwa wanda ya shahara da ayyukan alheri, sadaukarwa da gina ƙasa, lamarin da ya shafi rayuwar dubban ‘yan Najeriya tsawon shekaru da dama.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ziyarar a matsayin alamar haɗin kai na ƙasa da girmamawa ga mutanen Kano da kuma martabar da marigayi Aminu Dantata ya gada a tarihin Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su tarbi Shugaban Ƙasa cikin mutunci, zaman lafiya da halin karamci da jihar Kano ta shahara da shi.
Wannan lokaci ne na yin tunani mai zurfi da kuma girmamawa ga wani babban mutum da ya bayar da gudummawa matuƙa,” in ji Gwamna.
“Ina kira ga daukacin al’ummar Kano da su tarbi Shugaban Ƙasa cikin lumana da kulawa, yayin da yake shiga cikin jimamin da muke ciki.”
An kammala shirye-shiryen tsaro da sauran abubuwan da s**a shafi gudanar da ziyarar cikin nasara da kwarewa.
Sanarwa
Sanusi Bature D-Tofa
Darakta Janar
Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na gidan gwamnatin Kano.
04/07/2025
Jam'iyyar APC Da Gwamnatin Tinubu Suna Cikin Barazanar Faɗuwa Zaɓen 2027.
Inason sabuwar tafiyar ADC ta kayar da gwamnatin Tinubu na jam'iyyar APC domin Ɗorewar mulkin Damukuraɗiyya, a Nigeriya.
Saboda buƙatar tazarcen Tinubu jam'iyyar APC take Amfani da ƙarfin Iko wajen tilastawa ƴan Doka bijirewa Umarnin gwamnonin jam'iyyun adawar Nijeriya.
Ƙasar Nigeriya tana buƙatar sauyin gwamnati musamman a wannan yanayi da rashin tsaro ke ƙara yawa, a faɗin Nigeriya maimakon gwamnatin APC ta tura jami'in tsaro wajen da ƴan ta'adda s**a hana zaman lafiya sun gwammace su tara su wajen da bashi da mahimmanci ga, al-ummar Nigeriya.
Ɓangaren Shari'a ya rasa ƴancin gudanar da, aikin sa cikin Adalci musamman a karkashin jagorancin jam'iyyar APC.
Tsadar rayuwa talauci da rashin Aikin yi yaƙara yawa sakamakon rashin iya gudanar da gwamnati a karkashin jagorancin jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC bata da Manufar kawo sauyi a Nigeriya Shiyasa kullum Darajar kudin ƙasar mu yake cigaba da karyewa, a kasuwar chanjin kuɗin Duniya.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
03/07/2025
Matuƙar Ana, Buƙatar Samar Da Nagartattun Mutane Amatsayin Shuwagabanni Dole ne al-ummar Nigeriya mu kaucewa tsarin siyasar sak.
Babu jam'iyyar da bata da mutanen kirki Acikin ta sannan babu jam'iyyar Da Bata da mutanen banza, Acikin ta,
Kamar yadda Shuwagabanni da wakilai suke manta Banbancin jam'iyyar siyasa idan s**a haɗu muma talakawan Najeriya lokaci yayi da zamu jingine batun jam'iyyar siyasa mu duba chancanta.
Tsarin yadda kiristocin Nigeriya s**a yi wajen zaɓen 2023 matuƙar akabi, irinsa babu Abinda zai hana Nigeriya samun damar zaɓar Shuwagabanni Nagari.
A zaɓen 2023 kiristoci sun tsayar da Peter Obi amatsayin ɗan takara ɗaya tilo na shugaban kasar Nigeriya, a jam'iyyar LP Sannan sun bawa jama'ar su damar kowa ya zaɓi duk ɗan takarar da yake so a sauran Kujerun siyasa, a kowace jam'iyya, a shugaban kasa ne s**a haɗu wajen ra'ayi ɗaya.
Akwai mutanen da guguwar sak tabasu Nasarar samun Shugabanci ko wakilcin Al-ummah Sai gashi Manufar sa ta sauya kan yadda mutane s**a yi tunanin samun Shugabanci nagari daga wajen su.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
30/06/2025
Bance Kwankwaso Bazai Koma Jam'iyyar APC ba, Amma Dai, Ina Ganin Ko Zai Koma Jam'iyyar APC Sai Gab Da Zaɓen 2027.
Duk wanda yasan Kwankwaso yasan duk matsin lamba da zai fuskanta, baya saurin yenke hukuncin ficewa daga jam'iyyar sa sai gab da zaɓe.
A shekarar 2014. Shekara guda Kafin zaɓen 2015. Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.
A shekarar 2018 shekara guda kenan Kafin zaɓen 2019 Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
A shekarar 2022 Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar NNPP shekara guda kenan Kafin zaɓen 2023.
Na tabbata ko ƴanzu Kwankwaso Bazai yenke hukuncin komawa wata jam'iyyar siyasa sai zaɓen ya rage shekara guda wato shekarar 2026.
Duk da haka zamu cigaba da, amfani da wannan gaɓa muna tunzura tunzuraru.😂
Ko ƴanzu mun gamsu Kwankwaso jagoran Siyasar har yanzu bai ce komai ba, Amma shirun sa ya rikata lissafin ƴan tayi Daɗin siyasa.😂😅🤣
© Shehu Saleesu Farawa ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Gwale
Kano
08137209833
