Mumbarin sunna nss

Mumbarin sunna nss

Share

Wa'azantarwa da fadakarwa

14/05/2022

TUNATARWA

*"Wadatar zuci ƊABI'A ce dake da matukar tsada. Idan ka ga musilmi da irin wanan arziki, maza ka kusan ce shi don koyon wanan ƊABI'AR

29/12/2021

Kada Kayi Tsammani Mutuwa Zata Tsallakeka, Saboda Kai Yaro Ne Matashi Kuma Mai-Lafiya.

Kasani Cewa Mutuwa Bata Shamaki Da Qanwanci Na Shekaru, Koh Lafiya, Koh Nagarta. Dan Haka, Ka Zauna Da Shirin Mutuwa Akoda Yaushe.

Lallai Wadanda Suke Bin ALLAH (Ta'ala), Suna Zama Da Shirin Haduwa Dashi. Ta Hanyar Aikin Alkhairi Na Ladah

27/11/2021

Kyawun Diya-Mace, Ba Surar Jikinta Bane, Koh Hasken-Fata, Koh Salon-Magana. Kyawunta Sune; Na Dabi'ah, Imani, Tsoran-ALLAH Da Son Addininta, Ta Hanyar Sanya Tufafi Masu-Kamala, Da Kyawawan Ayyukan Alkhairi.

Amma *KASHHH*! Kadan Ne Daga Cikin Maza Suke Gane Hakan. Kuma Kadan Ne Daga Cikin Mata Sukeyin Haka.

27/11/2021

Ka Zama Mai Rokon ALLAH (Ta'ala), Da Ya Tsarkake Maka Zuciya. Wato Kayi Komai Dominsa, Ba Don Riya Ba.

Ta Yiwu Kana Aikata Alkahiri, Alhali Zuciyarka Babu Tsarki, Sai Duk Abinda Ka Aikata Ya Tafi A Banza. Ba Tare Da Samun Ladah, Koh Amfanuwa Ba. Saboda Haka, Aiki Baya Karbuwa Face Da Niyya Mai-Tsarki.

26/10/2021

SAƁANIN FAHIMTA.
-
"Bazai taɓa yiwuwa ba ace kowa yabi irin ra'ayin ka ko fahimtar da kake da ita, imma ta fuskar rayuwa ko ta fuskar addini, dole akan sami saɓanin fahimta ta ɓangarori ma bam-banta, amma hakan baya zama dalilin cin mutuncin juna ko raina juna"
-
"Samun saɓanin fahimta acikin addinin musulunci ba sabon abu bane a lokacin baya, kuma bazai taɓa zama silar yin gaba da juna ba a yanzu, sahabbai da manyan bayi masu nagarta da s**a biyo bayansu da kyautatawa sun sha samun saɓani game da wasu mas'aloli na addini, amma hakan bai taɓa zama silar rarrabuwar kawunansu ba, amma dukkanin wani wanda ya ƙirƙiro sabon abu a cikin wannan cikakken addinin namu na musulunci, tabbas malaman sunnah sunyi ijma'i wajen mayar masa da abun sa komai kyawun ganin da wasu al'ummar suke yi masa ta fuskar addinin musulunci alhalin kuma musuluncin bai koyar da shi ba"
-
"Lallai kasani! Yau idan wani ya saɓawa fahimtarka yayi abin da kake ganin ba daidai bane, to haƙiƙa tabbas kaima akwai abin da za kayi shima wanda yake yi masa kallon ba daidai bane, amma idan kowa ya tafi a kan fahimtarsa babu cin mutuncin juna, sai kaga an zauna lafiya, kaidai kawai ka guji ƙirƙirar abu acikin addinin musulunci sai ka zauna da Allah lafiya"
-
NAZIFI SALISU

26/10/2021

*YAYA ANNABI ﷺ YAKE YIN ADDUA GA MAMACI BAYAN AN BINNE SA A QABARI???*
Dukkan ibada tana zama daidaine har Allah ya amsa ya bada lada idan ta cika sharadi guda ukku;-
-Anyi ibadar Abisa ilimi kamar yanda Allah da Manzonsa s**ayi umarni.
-Anyi Ibadar da Ikhlasy da niyya kyakkyawa ga Allah shi kadai.
-Kuma anyi irinta Manzon Allah s.a.w
Dukkan wanda ya bautawa Allah babu wadan nan sharudda to ba'a kiran wannan abu da suna ibada ana kiransa ne bidi'a ko Riya ko kuma jahilci.
Daga Usman Bin Affan R.A yana cewa:
*"Manzon Allah s.a.w ya kasance:Idan aka idar da binne mamace yana tsawa awajansa sai yace"*"-
*(Ku nemawa dan uwanku gafara,ku roqa masa tabbatur harshensa akan gaskiya lokacin tambayar Qabari,domin yanzu za'ayi masa tambaya)*
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑـﻮ ﺩﺍﻭﺩ 3221 ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤـﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ .
I
ﺍﻟﺸــﻮﻛﺎﻧﻲ ﺭﺣـﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa:
"Wannan hadisin ya shar'anta mana nemawa wanda aka binne gafara bayan binnesa tare da roqa masa tabbatuwar harshensa akan gaskiya lokacin tambayar qabari".
Domin ana yi masa tambayane alokacin da aka binnesa.
@ ﻧﻴـﻞ ﺍﻷﻭﻃـﺎﺭ 4/11 .
ﺍﻟـﻌــﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﺑـﺎﺯ ﺭﺣـﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa:
"Yin addua ga mamaci bayan binnesa da nema masa gafara da tabbatuwar harshe akan gaskiya lokacin tambayar qabari,yin hakan sunnah ne".
@ ﻣﺠـﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔـﺘﺎﻭﻯ 13/205
ﺍﻟـﻌــﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴـﻤﻴﻦ ﺭﺣـﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa:
"Tsawa a qabarin mamace bayan binnesa kowa yana yi masa addu'a da nema masa gafara,yin haka sunna ne".
"Saboda Manzon Allah s.a.w ya kasance idan an gama binne mamaci yana tsayawa a wajan qabarin sai yace"-
*(Ku nemawa dan uwanku gafara,ku roqa masa tabbatuwar harshe akan gaskiya lokacin tambayar qabari,domin yanzu ana masa tambaya)*
@ ﻟـﻘﺎﺀ ﺍﻟـﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﻔـﺘﻮﺡ ﺭﻗﻢ 118
Daga haka zamu fahimci cewa:
Sunnar Manzon Allah s.a.w ta koyar da mu abubuwa guda ukku bayan an binne mamaci,yin hakan shine sunna,saba masa kuma ya zama bidi'a da son zuciya.
1-Abu na farko
*Tsayawa a tsaye a gindin qabarin,ba zama ake ba,kuma ba tafiya ake ba,kowa zai tsayen gwargwadon alqarka da mamacin".
2-Abu

Photos from Mumbarin sunna nss's post 19/09/2021

Zuwan malam Accra Ghana wa'azi
Dr abdallah usman Umar gadankaya

06/09/2021

Fadakarwa

01/09/2021
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Sumaila
Kano
712102