Lafiya uwar jiki

Lafiya uwar jiki

Share

WANNAN MANHAJAR NA BUDE SHI DOMIN ILIMANTAR AKAN KULA DA LAFIYAN JIKI DA KUMA ABUBUWAN DA YAKAMATA SU AMFANE MU GAME DA LAFIYAN MU

24/08/2025

Gwajin bakin mahaifa (pap smear) na kare mace daga ciwon daji ta hanyar gano matsala tun kafin ya tsananta.Adaure ayi

Allah ya tsare mana lafiyan muh

23/08/2025

Allah ya tashe mu lafiya

23/08/2025

“Maganar cewa yunwa ce ke kawo ulcer ba daidai ba ce, wannan zancen kasuwa ne kawai. Idan kana da ulcer, yunwa na iya ta’azzara maka ciwon, amma yunwa kaɗai ba ta haddasa ulcer.”

23/08/2025
23/08/2025

Ana garinta a rika sha a madara ko nono karamin cokali.

1. Tana magance matsalar rashin haihuwa ga maza
2. Tana kara karfin mahaifa ga mata
3. Idan ana sha da dare kafin a kwanta bacci a madara ko nono Tana magance rashin bacci.

23/08/2025

TSARABAR KARSHEN MAKO

Wannan Hadin zai saki kiba ya gyara miki NoNo yana Karin Ni'ima uwa uba ya Gyara miki fata, zaisa ko ina naki ya ciko Bulbul abinki, wannan Hadin Anawa Amare shi domin Gyaran jiki.

Waken SUYA
Shinkafa
Alkama
Rogo
Hulba
Sassaken faru
Girfa
Kankarar mata
Citta
Kaninfari
Masoro
Kimba

Ahadesu waje daya ki nikesu Aringa hadawa da madara ana sha cikin sati daya zakiga yadda jikinki zaiyi kyau.

Share

23/08/2025

Amfanin namijin goro, ga lafiyar Dan Adam

Amfanin sa,

Guda goma sha shidda (16)
(1) Namijin goro yana maganin tari idan Aka hada da (Tom Tom) Ana chi.
(2) Namijin Goro yana maganin matsalar ciwon sanyi, idan Aka hada da kanunfari A tasafa Asha Ruwan.

(3) Namijin Goro Yana maganin ulcer idan Ahada dabino Adaka, Asa Zuma A sha cokali biyu.

(4) Namijin Goro Yana maganin matsalar tsutsar ciki idan Aka jajjaga A matse Ruwan A Zuma Asha .

(5) Namijin Goro Yana Qara kuzari da nisan tafiya ga Mai iyali idan Anaci da dabino daya namijin goro A tauna.
A Cinye kullun kaci sau uku.

(6) Namijin Goro Yana gayra maniyyi Idan Aka jajjagashi A samu garin Hulba Tafasa dashi Asaka madaran Ruwa Asha.

(7) Namijin goro Yana kawar da majinar kirji idan kana cin shi.

(8) Namijin Goro yana hana shan Taba idan Aka hada da furan tumfafiya Ayi garin su Asamu Karan sigarin da mutum yake Sha da madaran shanu wanda babu Hadi, Ajika yakwana da safe kafin Aci Komi A ba maishan Taban ya shanye duka zaiyi Amai.

(9) Namijin goro yana maganin hawan jini, Idan Aka hada ganyan cediya A tafasa Asa Zuma Asha.

(10) Namijin Goro Yana maganin ciwon Kai, idan kayi garin shi Ana hayaki Koda mace Mai yawan ciwon Kai tayi.

(11) Namijin goro yana gyara murya idan kahada da danyar citta da Zuma kana dafawa da Lipton kasha kafin kaci Komai.

(12) Namijin Goro Yana maganin kuraje Idan kasamu garin namijin goro ka kwaba da Man zaitun.
Idan Kuma kazuwa ce ko bakon dauro ka kwaba da manja kashafa.

(13) Namijin Goro Yana maganin sanyin Mara idan kahada da kanunfari da lemon tsami da Citta da garin Albabunaj.ka tafasa kasha da Zuma.

(14) Namijin Goro yana maganin wuta- idan kahada da sassaken itacen Qirya kadaka kasa gurin da wuta taci.

(15) Namijin Goro Yana tsayar dajini idan Kika hada da tsamiya ki tafasa Kisha zai tsaya.

(16) Yawan cin namijin Goro Yana kawar da wasu cututtukan da suke cikin mutum.

Allah kara mana lafiya da Imani Amin.

23/08/2025

Idan kasan kana/kina amfana da wannan shafin karubuta mana a comment section👇

22/08/2025

Ciwon mara lokacin haila ana kiransa da "Menstrual cramps" ko Dysmenorrhea a turance akwai matan da har Suma sunayi idan ciwon yatashi.

🩸 Abinda ke haddasa wannan ciwon:

1. Hormone mai suna Prostaglandin:

Lokacin haila, jiki na saki prostaglandins – wani sinadari da ke sanya mara ta matse domin zubar da jinin ciki.

Idan wannan sinadarin ya yi yawa, yana haddasa ciwon mara mai tsanani.

2. Yawan murɗewa (Contractions):

Uterus (mahaifa) tana murɗewa sosai domin fitar da jini.

Wannan murɗewar na hana jini isowa da kyau, wanda ke haddasa zafi ko ciwo.

3. Endometriosis:

Wannan ciwo ne da ke faruwa idan wani sashi na mahaifa yana girma a wuri da ba dace ba.

Yana haddasa ciwon haila mai tsanani sosai.

4. Fibroids (Ciwon nama a mahaifa).

Su ne ƙuraje ko nama marasa cutarwa da ke girma a mahaifa Ma'ana Wanda ke fitowa cikin mahaifar.

Zasu iya hana haila fita da kyau, suna jawo ciwo da kumburi.

5. Infection (Ciwon sanyi)

Idan mace tana da infection kamar PID (Pelvic Inflammatory Disease), zai iya kawo ciwon mara yayin haila.

6. Stress da gajiya:

Gajiya ko damuwa na iya ƙara tsananta ciwon haila.

✅ Yadda ake rage ciwon

1. Shan ruwa mai zafi ko soup.

2. Zama ko kwanciya da roba mai dumi a mara.

3. Shan maganin saukar ciwo kamar Paracetamol, Ibuprofen (da izinin likita).

4. Aiki ko motsa jiki (light exercise).

5. Guji shan kayan sanyi ko lemu sosai lokacin haila.

📌 Idan ciwon mara

Ya yi tsanani sosai

Ya wuce kwanaki 3-4

Ko ya hana ki yin aiki ko zuwa makaranta
👉 Sai a ga likita.

✍️ Nanerh Fadimatou Zahrah

22/08/2025

“Alhamdulillah yanzu muna da followers sama da 40,000 a wannan group. Amma idan muka yi posting ba mu cika ganin likes, comments ko shares ba. Mu duka muna so mu san kuna tare da mu, domin hakan ne zai ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen kawo muku abubuwan da kuke so. Ku kasance masu like, comment da share don mu ci gaba tare.”

Lafiya uwar jiki ✍️

22/08/2025

Kowa ya zaɓi irin tafin sawunsa A ko B?

Masu leƙen tafin sawun macen da suke neman aurenta da zimmar gano wane irin tafin sawu take da shi tare da amfani da abin da s**a gani wajen yin fassarori waɗanda ba su da tushe b***e makama, to gaskiya hakan zurfafawa ce da ba a buƙatarta.

To amma kafin ku leƙe tafin sawun budurwa ko saurayi, kowa ya zaɓi irin tafin sawunsa ba tare da ya duba comment section ba😅 Saboda cikon bayanin yana can.😁🤸

© Lafiya Uwar jiki

22/08/2025

ALLAHU AKBAR
Watarana MANZON ALLAH S.A.W. ya gama ibada yana addu'a Yana cewa Allah ka yafema sayyada Aisha R. A. zunubbanta da wanda ta sani da wanda bata saniba Da wanda tayi yanzu da wanda zataiyi nan gaba duk Allah ka yafemata ashe sayyada Aisha tana ji sai taji wani irin dadi sai tace: Ya RASUULULLAHI (S.A.W.) na gode sai Manzon Allah yace wannan addu'ar dana yimaki. Itace nake yiwa AL 'UMMATA A kowace Sallah. Idan kaji dadi turawa wasu suma domin suji dadi!

IDAN KAJI DADI KATURA A GROUP 7 ZUWAGA MASOYA ANNAB ﷺ ALLAH YAKARA MANA SON ANNABI MUHAMMADU ﷺ

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Jiddari Polo
Maiduguri
23401